A irin wannan lokaci da ake ciki na hauhawar zazzabi cizon sauran (malaria) wanda ya addabi al'umma musamman marasa karfi a ya yankunan masu yawa a Nigeria, wanda ya hada harda Jahar Zamfara.
Yan'uwa matasa a almajiran Sayyid Zakzaky (H) sun gudanar da feshin maganin saura a Unguwar Dallatu dake cikin garin Gusau babban birnin Jahar Zamfara, domin saukaka yaduwar cutar cizon sauro.
Da yawan mutanen da akayi aikin a wuraren su, sunyi maraba da aikin da Kuma nuna farin cikin su sosai, tare da yin kalamai masu dadi ga Harka Islamiyya da Jagora (H) ta dalilin wannan aikin.
Wannan aikin anyi shi ne saboda kara nuna farin cikin da zagayowar watan wiladar Manzon Allah (S) da kuma farantawa masoya Manzon Allah da iyalan sa (A.S).
Dandalin matasa Gusau:
09/10/2022






