Dag, Bilal Nasir Umar Sakkwato.
A cigaba da bukukuwan Maulidin Annabin rahama (s.a.w.w) ƴan uwa mata Harisawa a Sakkwato, sun kai ziyara a babbar Asibitin ƙasa ta masu fama da matsalar ƙwakwalwa (Federal Neuropsychiatric) dake cikin ƙaramar hukumar Kware ta Jahar Sakkwato.
Ziyarar wacce suka kai a jiya Assabar 12 ga watan Rabi'ul Auwal shekara ta 1444 daidai da 8/10/22022.
Ziyarar kuma wacce ta gudana a ƙarƙashin jagorancin Malama Zara Aliyu Eco.
Yayin wannan ziyarar ƴan'uwan sun gana da ma'aikatun da ke kula da majinyatan tare da gaya musu cewa, “su ƴan'uwa ne Almajiran Sheikh Ibrahim Yaqoub Alzakzaky, kuma sun zo ziyara ne ga marasa lafiya alfarmar wannan wata na Rabi'u Awwal watan da aka haifi fiyayyen halittu Annabi Sallallahu alaihi Wasallam.
Ƴan'uwa matan masu ziyarar sun rarrabawa majinyatan sabulun wanka da na wanki, rawan sha dss.
Haka kuma anyi addu'o'i na musamman ga majinyatan tare da fatar Allah ya basu lafiya.





