Offline

Mahukuntan Kasar Saudiyya Sunyankemata Shekaru 15, Saboda Goyon Bayan Hizbulla a Twitter.



- Mahadi Tukur Almizan.

Mahukuntan kasar Saudi-Arabia sunyanke ma wata likita 'yar asalin kasar Tunisia mazauniyar Saudiyya hukuncin shekaru 15 agidan yari maisuna Mahdia al-marzouki.

Wannan mata dai laifinta shine ta nuna goyon baya ga kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon awani Posting da'akayi a shafin Twitter.

Tunda farko dai anyankemata hukuncin shekaru biyu da watanni takwas ne kafin daga baya mahukuntan kasar suka daukaka kara Inda aka tsawaita daurin zuwa shekaru 15.

Mahdia dai tanada shekaru 51, kuma tana zaune ne a kasar ta Saudiyya tun shekarar 2008, ankamatane a shekarar 2020.

©Freedom Fighters Ng.

Post a Comment

Previous Post Next Post