Offline

Wani Bafalasdine Rabi Arafah mai shekaru 32 ya gamu da munanan raunuka sakamakon harbin da sojojin mamaya na Isra'ila suka yi masa a Qalqilya da ke gabar yammacin kogin Jordan.

 




Wani matashin Bafalasdine ya rasu da yammacin yau a wani asibiti a birnin Qalqilia da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan da aka mamaye, sakamakon raunukan da ya samu a safiyar yau da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka yi a kusa da birnin, A cewar ma'aikatar lafiya.


Maaikatar lafiyar ta ce a takaice dai Rabi Arafah, mai shekaru 32, ya samu munanan raunuka sakamakon harbin da Isra'ila ta masa a kai, kuma an garzaya da shi asibitin Darwish Nazzal na birnin domin duba lafiyarsa, inda ya rasa ransa sakamakon munanan raunukan da ya samu bayan 'yan mintoci kaÉ—an.


Ma'aikatar ta ruwaito shaidun gani da ido na cewa, sojojin mamaya na Isra'ila da ke wani shingen bincike a kusa da birnin sun bude wuta tare da yi masa mummunan rauni a kai.


Source: Wafa

Post a Comment

Previous Post Next Post