Offline

Afganistan: Hare-Haren Bam sunyi Ajalin dalibai 27 a Kabul

Rahotanni daga Afganistan na cewa sama da dalibai 27 ne suka rasa rayukansu sanadin tashin bama bama a wata makaranta dake Kabul.

Lamarin ya faru ne a makarantar yara maza ta Abdul Rahim Shahid, dake unguwar ‘yan shi’a a birnin Kabul, a lokacin da dalibai ke barin harabar makarantar bayan kammala karatun safe.

Bayanai sun ce akalla bama-bamai masu karfi biyu ne suka fashe a makarantar kuma akwai yiwuwar adadin wadanda lamarin ya rusa dasu ya karu.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, sai dai masu sharhi na ganin cewa zai iya zama da hannun kungiyar IS, a ciki wacce ta yunkuro tun bayan da 'yan Taliban suka kwace mulki a kasar a cikin watan Agustan bara.

Da take Allawadai da harin, Iran, ta bakin kakakin ma’ilkatar harkokin wajen kasar ta bukaci hukumomin Afganistan dasu zakulo tare da hukunta wadanda ke da hannu a wannan dayen aiki na ta’addanci.


source: Hausa Tv

Post a Comment

Previous Post Next Post