Da safiyar yau Talata, daruruwan yahudawan sahayoniya, tare da sojojin da suke yi musu rakiya, sun kutsa cikin masallacin kudus.
Gabanin kutsen ‘yan sahayoniyar cikin masallacin kudus din a yau, sojoji sun hana duk wani Bapalasdine mai kasa shekaru 40, shiga cikin masallacin saboda tsoron yin taho mu gama.
Sai dai duk da hakan, Palasdinawan da suke cikin masallacin na kudus sun yi kokarin hana yahudawan sahayoniya shiga cikin masallacin, lamarin da ya sa aka harba musu hayaki mai sa hawaye, da kuma na barkono.
A jiya Litinin da shekara jiya Lahadi ‘yan sahayoniyar sun kutsa cikin masallacin na kudus, inda jami’an tsaronsu su ka yi amfani da karfi akan Palasdinawan da suke ciki da kuma harba hayaki mai sa hawaye akansu.
A can birnin Khalil kuwa ‘yan sahayoniyar ne su ka kutsa cikin masallacin Annabi Ibrahim, ( a.s) inda su ka gudanar da ibardar su a ciki.
Tuni dai gwamnatin rikon kwarya-kwaryar Palasdinawa ta yi tir da abinda yake faruwa, tare da yin kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su hana faruwar abinda ta kira; Yakin Addini a cikin wannan yankin.
source: IRIB HAUSA
Tags
News