Offline

​Iran Ta Yi Allah-Wadai Da Harin Da Isra'ila Ta Kai A Masallacin Al-Aqsa


​Iran Ta Yi Allah-Wadai Da Harin Da Isra'ila Ta Kai A Masallacin Al-Aqsa

Ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir-Abdollahian ya yi Allah wadai da hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke kai wa Falasdinawa masu ibada a harabar masallacin al-Aqsa.

Ya ce; “Abin takaici, mun shaida zaluncin yahudawan sahyoniya a masallacin al-Aqsa a cikin watan azumi mai alfarma,” kamar yadda ya shaida wa takwaransa na Mauritaniya Mohamed Salem Ould Merzoug a wata zantawa ta wayar tarho.

Babban jami'in diflomasiyyar na Iran ya kara da cewa "Muna fatan al'ummar Palastinu za su sami damar samun 'yancinsu na tarihi tare da goyon bayan kasashen musulmi da al'ummominsu."

Sama da Falasdinawa masu ibada 150 ne suka jikkata a lokacin da sojojin Isra'ila suka kutsa kai cikin harabar masallacin Aqsa a ranar Asabar.

Dakarun dai sun ci gaba da keta alfarmar wannan masallaci da suke yi baya ga murkushe masu zanga-zangar nuna goyon baya ga al’ummar birnin na Quds da ake yi dukkanin yankunan yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye.

Amir-Abdollahian ya kuma godewa Mauritaniya bisa matsayinta na goyon bayan da take bayarwa dangane da lamarin al'ummar Palastinu da ake zalunta.

Da ya koma kan batun Yemen, ministan na Iran ya ce Tehran ta yi maraba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar Yemen, tare da fatan ganin an kawo karshen yakin gaba daya, da warware matsalolinta ta hanyar tattaunawa tsakanin ‘yan kasar ta Yemen.

A halin da ake ciki kuma, ya yi maraba da ci gaban dangantakar da ke tsakanin kasarsa da kasar Mauritaniya, yana mai jaddada cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta ci gaba da kara inganta huldar dake tsakaninta da kasashen Afirka.

A nasa bangaren ministan harkokin wajen na Mauritania ya jaddada matsayin kasarsa na jin kai game da batun Palastinu.

Ya bayyana alakar kasarsa da Tehran a matsayin mai karfi, yana mai cewa Nouakchott ta maraba da ci gaba da bunkasa alaka da hadin gwiwa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran wajen raya ababen more rayuwa na kasar Mauritaniya.

Post a Comment

Previous Post Next Post