Offline

WANNAN YANAYIN DA AKE CIKI SHIRI NE DAGA WAJE

Abin da nake cewa, gaskiyar magana wannan al’amari ne da gaskiya fa ya fi karfinmu, wani shiri ne gagarumi da aka yi mana daga waje, ba mu ne ke da shirin ba, ba a nan kasar aka yi shirin ba, a waje aka yo shi aka zo aka shigar.

Tun lokacin wani shugaban Amurka da aka taba yi mai suna Eisenhower, ina jin an yi shi a shekarun 1953-1961 ne, to ya san an yi masa nazari a kan al’amarin mutanen Arewacin Nijeriya, sai aka ce an lura cewa su mutanen Arewacin Nijeriya su sun dogara da kansu ne, mutanen birane suna yin kasuwanci da sana’o’i, su kuma mutanen kauyuka suna yin noma da kiwo, amma ana musaya. 

Su na gari suna kasuwanci da sana’a kamar su saka da kira da sassaka da gini da ire-iren wadannan, su kuma mutanen daji suna noma suna kiwo. To kowanne ya dogara da kowanne. Su wadannan su suke kawo abinci, wadannan kuma duk abin da ake bukata na yau da kullum.

To sai aka yi tunanin yadda za a yi, a san yadda za a yi a raba na dajin da wannan noma da kiwo din, a zo a kashe kuma masana’antun gari, don ta haka nan ne kawai za a turo musu kayan waje su saya. Don da can ainihin hatta irin rigunan nan ba na waje muke saya ba a nan ake sakawa, duk komai mu muke yi ma kanmu a da.

Sai suka yi nazari, aka zo aka fara tunanin yadda mata ke nadi, da yadda ake saka, duk aka lura, aka zo da na waje, kadi ya mutu, saka ya mutu, kira ma ya mutu, komai yanzu sai a kawo na waje, haka nan kuma duk sauran sana’o’i suka fara macewa. To yanzu abin da ya rage shine noma da kiwo. To in ka lura yanzu noma da kiwon ne aka farwa.

Yanzu mutum ya yi nomansa da kakan nan, ya riga ya tattara komai, hatsin da zai ci kenan ya (kafin) ya yi noma shekara mai zuwa. To an je garin an yamutsa rumbun, an kona wannan noman da ya yi na shekara wanda shi zai ci ya zauna a wajen. To sai me ya rage, zai zauna a wajen? Ai bai ga ta zama ba.

Ko kuma makiyayi, shima an kwace shanun, har ma an firgita shi, ba kawai kwacewa ba. Da ma kwacewa ne kawai aka barsa da ransu, amma kila an kashe ‘ya’yansa ko iyayensa, an sa shi a cikin wani irin hali na damuwa, yanzu a tsorace yake a firgice yake ba dukiya ga kuma tsoro, bashi cikin aminci dole, dole a bar kauyuka da dazuzzuka a shigo birane. To kuma in aka zo birane aka zauna, matsalolin Birane za su bijiro sai kuma a bar birnin.

To wannan shiri ne lallai aka yi mana, kuma za ka ga kamar yadda nake cewa, ba wanda za ka yi ma magana ka ga ya damu, duk wanda yake cikin Hukuma in ka yi masa magana sai dai ya yi maka garau kawai, shi abin da ya dame shi shine abin da shi yake samu yanzu a rayuwarsa, tunda shi yana samun nashi shikenan in ya so kowa ma ya halaka bai dame shi ba. Za ka ga ba abin da ya dame su, basu damu da halin da al’ummar ke ciki ba sam, kowanne ta kansa kawai yake yi in kai masa magana.

MU KOMA GA ALLAH DA ADDU’O’I:

Saboda haka yanzu wannan halin da muka shiga ina mafita garemu? Illa kamar yadda muka sani lallai Allah ba azzalumin kowa bane, kamar yadda wannan yake cewa an fara irin wannan taron addu’a din nan, Allah Ta’ala maji rokon bayi ne. tunda in ya zama baka da wani makami sai Shi, Shine Madogaran wanda bashi da madogara, Shine Gatan wanda bashi da gata, Allah ba azzalumin kowa bane, ba za a yi wannan zaluncin a wuce da shi ba.

A koma gare shi da magiya, kamar addu’o’in nan da kuka shirya na Minna din nan, yana da kyau ya zama kamar duk lokaci a sauke Alkur’ani da wasu addu’o’i. Yanzu muna da addu’o’in da kila sai an koyawa mutane, ko in basu iya ba ma za su iya jin ana yi, irin su addu’o’inmu Ma’athurai; muna da addu’o’in da muke yi dama duk daren Juma’a; Du’a’u Kumail, na neman gafara; Muna kuma da Addu’ar Tawassul da mu kan yi duk daren Laraba, muna kuma da wadansu addu’o’I da mu kan yi daga lokaci zuwa lokaci, ko wajen Jana’iza ne kuma har ila yau mu kan sauke Jaushan a wajen Jana’izozinmu. To irin wadannan addu’o’in Allah Ta’ala maji rokon bawa ne.

Kuma kamar yadda dazu nake cewa, in an yi maka tarko kar ka fada, in zai yiwu ka kauce, kamar yadda shi Ardo ke bayanin cewa shima an duba masa wani waje a Kamaru, duk warin da ya fi zama lafiya sai mutum ya je can. Gashi yanzu an ce in mutum ya bar dajin ya zo gari an biyo shi garin? Yanzu ana ragoton da an ga bako Fatullatani ya zo sai a fara tunanin yaya? Ballantana ace har ya sayi gida. Sai a fara zargin ashe ‘Kidnapper’ ne, sai kuma ‘yan banga da ‘yan sanda su zo su tafi da shi, a je a yanka shi.

Yanzu in mutum ya san inda zai je ya samu ya tsira, to daidai gwargwado sai ya tafi. Ance Kamarun ma ba wai komai lafiya lau bane, amma tuntuni Fulaninmu sun rika tsiyayewa suna komawa Kamaru, da yawansu, saboda tun ma kafin a shigo da wannan musibar, lokacin tsananta musu da ake yi da batun haraji da sauransu, ya sa wasu suna tsiyayewa suna komawa can.

To kuma na san wannan abin an kakkai sauran wurare, amma bai yi tsanani ba. wadanda suke zaune kamar a Mali, Mali an kai musu rigingimu suma can, amma bai kai tsananin na nan ba. Su an kai musu na rigimar tsakanin Dawarik da sauran mutanen wajen, amma bai kai tsananin na nan ba. Haka kuma su Guinee da su Burkina Faso, da Senagal. To ta yiwu duk da sauki can.

Tunda wannan kamar muna wani marhala ne da muke fatan ya zo ya wuce, don insha Allah ba zai dauwama ba, muna fatan ya zo ya wuce. In mutum ya ga zai kaucewa tarkon daidai gwargwado ya samu inda zai samu zaunawa cikin kwanciyar hankali, to sai ya yi wannan, har zuwa lokacin da abubuwa suka natsa, sai a dawo a cigaba da harkoki.

Amma dai babban makaminmu shine a cigaba da addu’a din nan, mu koma ga addini ne kawai. Allah zai ya taimake mu kuma. Gaskiya da ban takaici, da ban-takaici wallahi, Allah Ya tausaya mana. Muna rokon Allah Ya tausaya mana. Labarin babu dadi wallahi. Na kan rika bibiyan labarin a inda ake badawa, ba dadi labarin, kullum aikin kenan.

JAWABIN SHAIKH ZAKZAKY (H) YAYIN ZIYARAR FULANI (7)
Za mu cigaba.
— Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H).
Www.cibiyarwallafa.org

2 Comments

  1. Allah Taala ya tausaya mana yakawo karshen wannan musifu yakara masu malam lafiya Bihakki Muhammad saww.

    ReplyDelete
Previous Post Next Post