Offline

SUN TAIMAKE MU TA WATA HANYA

Bahaushe ya kan ce a kan yi sara da duban bakin gatari, ban san ko su kan duba bakin gatarin ba. Alal misali, muce yanzu su tambayi kansu, wane buri suka cimmawa? Na musu Ingilishi, nace me suka yi ‘achieving’? Idan manufarsu shine kashe mutane su ji dadi, to sun kashe, sun kashe sama da mutum dubu sun bizne su. In dama manufar kenan, to sun yi, sun cimma wannan manufar. 

Amma in manufar ita ce kawar da wani abu da basu so, to mu tambaye su, to kun kawar? Sai suka ga karuwa ya yi. Suka ga sun karfafa shi ne, sun tambatsa shi ne, sun yi mana ayyuka da ko ma mun dauki shekara da shekaru ba za mu iya yi ba. Alal misali, wannan waki’ar ita ta koyar da mutane cewa su wadannan mutane me suke kira gare shi ne? Kuma wadanne irin mutane ne su? 

Akwai wani babban ma’aikaci da yake fada mana cewa, akwai wata Darakta a wajensu, shi lokacin yana mataimakin Darakta, yanzu ya zama Darakta din shima. Yace wata Darakta a ma’aikatansu take ce da shi, inda an ce mata Shi’a (kamar yadda suke cewa Shiites) mutane ne da ba masu ‘violence’ (ta da tarzoma) ne ba, ba za ta yarda ba, amma bayan wannan waki’ar ne ta gane haka.

To har ma wani ina fada masa, sai yake ce min ah, shi ya ji ina wannan maganar, ya dauka shima wata ce wadda ya ji, sun je National Hospital Gwagwalada, don su godewa mutanen Asibitin kan kula da marasa lafiyarmu da suke yi, shima sai yace, sai wata ta fadi haka nan, tace ai ita da za a ce mata Shi’a ba ‘yan tarzoma bane, ba za ta taba yarda ba, sai da ta gani da idanunta.

Sai ya dauka wannan nake magana. Nace a’a, wannan wani ma’aikaci ne a wata ma’aikatar daban yake fada min. Sai yace shi kuma wannan da shi a asibiti wannan matar take fada. Sai ya dauka ma wannan ni nake nufi. Nace a’a ni ban san wannan ba ma. 

Wato kenan (waki’ar) ya canza yadda mutane suke kallonmu, yanzu ne ma mutane suka fahimci wai me ma muke cewa ne ma. An yi shekaru kusan 40 ana magana amma wani bai ji ba. amma yanzu da ya kai gare shi, yace wai me ake cewa ne? Sannan ya fahimta. To ka ga sun taimaka ta wata hanya, sun isar da da’awa.

BABU KOTUN DA TA SAME MU DA LAIFIN DA SUKA ZARGE MU:

Sannan kuma duk yunkurin da suka yi su malkwaya al’amarin su ce atafau mu ne ma muka yi laifi. Wanda na kan ce wannan kekesar zuciya da yawa take, ace tsabar rashin kunya da bushewar ido, wai ku kashe mutane dubu, sannan ku kamo wasu mutane kamar guda 500 kuce wai sun kashe soja guda daya.

Wajen mutum 500 suka kama, ko sun ji kunya ne, da aka je za a shiga da su gidan yari a Kaduna, sun cika wuri aka rasa yadda za a yi, gidan yarin ma ba zai iya daukarsu ba, sai zuwa can suka aiko cewa to duk ma su tafi banda mata, kuma yara ‘yan kanana ma, wanda suma gidan yari basu karbar yara suka ce ba za su karbe su ba, sannan aka dinga ragewa, daga 500 aka dawo da su kamar 300, aka yi ta ragewa aka dawo 200, aka yi ta ragewa, aka dawo 153. 

To sannan 153 ne aka kai su kotu, aka raba su kotuna biyu, wannan 77 wannan 76, duk ana chajinsu. Inda Allah ya tozarta su, suka rasa mene ne laifin da aka yi? Wai an tsare hanya. Har Madugunsu yace wai shi in shi ne ma aka masa abin da aka yi, abin da zai yi zai wuce haka nan. 

To in wani Kwamandan Soja ya zo an tsare masa hanya ya kashe mutum dubu, to shi mai gidansa yace in shine ma aka tsare masa abin da zai yi zai wuce haka nan. Ka ga shi zai ta da garin ne gaba daya. In shine zai ma share garin ne gaba daya. Wai an tsare musu hanya.

To kuma wai duk wadannan (da aka kama din) su kuma sun kashe soja kwara daya. Sai muma daga karshe ni da Malama ma aka sake kai mu duk aka mana wannan chajin, amma mu namu ba an ce mun kashe soja bane, wai mu muka ingiza aka kashe. To duk dai kotunan da suka kai sai basu ga laifinmu ba.

BA SU DA JARUMTAR BUGUN KIRJI KAN BARNAR DA SUKE YI:

Amma duk da haka, har yanzu duk lokacin da suka yi barna, wadanda suka wa barnar ne suka yi laifi. To, na ga kamar Fir’auna ma ya fi su ma gaskiya, don shi Fir’auna baro-baro ya fada, yace za mu cigaba da kashe ‘ya’yayensu maza, mu kyale ‘ya’yansu mata, ai mun fi karfinsu. 

Saboda haka, ya kamata shima Fir’aunan wannan zamanin shima ya yi karfin hali irin na kakansa. Yace an kashe din! Meye ne cewa an tsare maka hanya ne? Kace an kashe din sai me? Haka shi Fir’auna yace, za mu cigaba da kashe su ne, ai mun fi karfinsu. Ya kuma ce, ku kyale ni na kashe Musa, ya kira Ubangijin nasa, ni fa ina jin tsoron kar ya canza muku addini, ko kuma ya kawo barna a kasa. A wata kira’a ya kuma bayyana fasadi a kasa.

Wato a nan Fir’auna ya zama shine mai addini sahihi, addinin gaskiya, yana jin tsoron kar a canza masa addinin mutane a kawo musu wani addini daban. Da suna addinin bautan Fir’auna da gumakansa, yanzu su koma addinin bautan Allah shi kadai. To shi Fir’auna baya son haka. Kuma yana jin tsoron kar Musa ya bata kasa. Ya bata kasa yake? Da can ana addinin da aka gada iyaye da kakanni, yanzu a koma a bi addinin Musa, wanda ake bautan Allah Ubangijin da ya halicci sama da kasa. 

To ka ga ba Fir’auna ya fito da abinsa a sarari ba? Ya fito da aniyarsa a sarari cewa ga abin da baya so, ga abin da yake so, saboda haka a kyale shi. To wannan kuwa su basu da wannan karfin halin na yin irin na Fir’auna, su ce sun yi din, kuma su ce ga dalilin da ya sa suka yi din.

MUNA TAMBAYARSU KAN BAYANIN YARIMA BIN SALMAN:

To amma da Allah ya kama su, sai ga Dan Sarkin Saudi Arabiyya yace sun murkushe wata Harka irin ta Hizbullah a Nijeriya. Sun hana Jagoranta Zakzaky kafa gwamnati ta Musulunci irin ta Iran.

Har yanzu muna binsu bashin amsa, muna tambayarsu wai wannan maganar da ya yi da gaske ne ko ba da gaske ne ba? Ka san suna da Ministan watsa labaru sunansa Lai, har yanzu Lai ya yi shiru, ya yi likimo. To, Lai, ko kuma mai gidanka, wannan maganar da gaske ne ko ba da gaske bane? Shiru.

JAWABIN SHAIKH ZAKZAKY (H) GA IYALAN SHAHIDAI RUKUNI NA BIYU A RANAR 5/12/2021 (2)

Za mu cigaba.
— Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H)
www.cibiyarwallafa.org

Post a Comment

Previous Post Next Post