Offline

JAWABIN SHAIKH ZAKZAKY (H) YAYIN NISFU SHA’ABAN 1443/2022 (2)


HAIHUWAR SAHIBUL ASR WAZ ZAMAN (AS) YA KARAWA DAREN DARAJA:

To, sai kuma a shekara ta 255 bayan hijirar Manzon Allah (S) Allah ya kaddara a safiyar wannan dare mai albarka, a safiyarsa, gab da alfijir kenan, aka haifi Sahibul Asr Waz Zaman (AS). To, sai ya karawa wannan dare da wannan rana babban daraja. Dama yana da matsayi, an san shi a matsayin daren da ake rubuta abubuwan da za su faru a shekara ne, sai kuma ya dace da ranar haihuwar Sahibul Asr Waz Zaman (AS).

To, haihuwar Sahibul Asr Waz Zaman albishir ne ga wannan al’umma cewa shugaban wannan zamani, kuma madogaran wannan al’umma, wanda kuma Allah ya kaddara masa zama cikin mabiyansa duk tsawon zamani, a wannan lokacin aka haife shi. Tun kafin haihuwarsa Manzon Allah (S) ya ba da labarin limaman nan 12, limami bayan limami da sunan kowanne, kuma ya ambata cewa shi wannan Imami zai yi gaiba har biyu; akwai gajeruwa akwai kuma doguwa. 

MAKIYA BASU JAHILCI AL’AMARIN IMAMAI 12 BA:

To, wannan batun haihuwarsa ya kai haddin ‘tawatur’, duk masoya da makiya duk sun sani, sarakunan Banu Umayya sun sani, sarakunan Banul Abbas sun sani sarai. Duk sun san A’imma din nan, duk sun sani sarai. Kuma ba abin da ba su yi ba, don su hana wannan al’amari gudana.

Alal misali, akwai wani sarkin Musulmi da aka yi mai suna Ma’amon (Ba’abbase) da ya gano cewa Imam Jawad (AS) shine limamin zamanin, to sai ya bashi auren diyarsa. Aka yi gagarumin biki, har Banul Abbas, wadanda sune jinin sarauta suka ji haushin don me zai hada jininsa da Ba’alawiye, Ba Husainiyye?

To, shi fatan da yake yi shine tunda wannan shine Imam, to shima zai zama dansa Imam ne. Tunda shine Imam na tara, dansa zai zama Imam na goma kenan, jikansa ya zama Imam na 11, jikan jikansa ya zama Imam na 12, to in aka yi sa’a ita wannan ‘yar tasa zai zama ita ta haifi Imam mai zuwa, to kaga shima ya dan samu (zai zama Imam din yana da jininsa). Kaga wato ma’ana sun sani kenan.  

To, ita matar bata so auren ba, amma sai ya fada mata sirrin abun, har ta yarda. Sai ta ga shirur-shiru ita bata haihu ba, shiru-shiru bata haihu ba, sai ta gano ashe dama yana da mata kafin ya aureta ita bata sani ba, kuma ta haifi da namiji. To shine tace shikenan ka mutu ka gama. Ita ta yi sanadiyyar kashe shi, ta yi asarar duniya da Lahira. (Sai ya zama) ‘plan’ din Ma’amon bai yi ba.

MA’AMON NE YA KIRKIRI HADISIN DA KE CEWA SUNAN BABAN MAHDI IRIN NA ANNABI (S) NE:

To, har wala yau Ma’amon ya yi wani mafarki na daban, baya ga wannan na gaskiyar, ya kuma so ya fito da Mahdin karya. Lokacin yana da Fadawa masu yi masa Hadisi. Kun san akwai wasu mutane an ace musu ‘wadda’un’; masu kirkirar Hadisi. Sarkin Musulmi ne kawai zai nishadantu yace wai ba Hadisi ne da Annabi yace ana iya yin kaza? Sai su ce ranka ya dade za a duba. 

Sai a bata hankalin dare a yi ‘isnadi’, shine yanzu ake ta fama da mutane, a littafansu sahihai su ce atafau wannan hadisi ne, nan kuwa a fadan sarki aka kirkiro. Wanda zai kirkiro karya zai ce maka shine ya kirkiro? Zai jinginawa wasu ne wadanda ake ganin darajarsu ai. An wane, an wane, an wane, wadanda za a gasgata su. Shi yasa sai ka ga ‘isnadi’ mai kyau a nazarin mutane, saboda zai lura da wadanda mutanen suke girmamawa ne sai yace ai wajensu ne ma aka ruwaito. In yace shine ya yi mafarkin wannan hadisin wa zai kula da shi? Sai ya saka sunan mutanen da za a aminta da su. Abin da ke faruwa kenan.

To, lokacin shi Ma’amoon sai ya so ya fito da Mahdin karya. Shine ya kirkiro Hadisin da yake cewa sunan Mahdi zai zama irin sunan Manzon Allah, wannan haka ne. Sannan yace sunan babansa kuma Abdullahi, sunan mahaifiyarsa kuma Amina, kamar na Manzon Allah. Shi yasa aka yi masa wannan Hadisin. Yana nan a littafan ‘Ama’.

Saboda mene? Shi Ma’amon sunansa na asali Abdullah, don in sun yi sarauta ne suke kirkirowa kansu suna, nan za ka ji an ce Mu’utasim, Mutawakkil da sauransu, in sun yi sarauta ne suke saka suna, amma kafin su yi sarauta suna da wani suna daban, in mutum ya zama sarki sai ya sa suna. To, Ma’amon din sunansa na sarauta ne. Babansa kuma Harun, wanda shi kuma ake ce masa wai Rashid. 

To, yana da mata Amina, sai ta haifi da, sai ya saka masa suna Mahdi. To, shine sai yace sunan mahaifin Mahdi zai zama Abdullah, mahaifiyarsa Amina, daidai da irin na Manzon Allah (S). Shi kuma sai ya haifi da ya sanya masa Mahdi, yana son nan gaba ace oh, ai ga ma Mahdi din. 

In mun ce ‘Hujjatu Binil Hasan’, sai su ce Ah! Ba an ce Abdullahi bane? In kace sunan Mahaifiyarsa kuma Narjees, sai su ce ai ance sunanta ya dace da irin sunan mahaifiyar Manzon Allah (S). To, a kirkirarren hadisi ne. Shi Sarkin Musulmi Ma’amon ne ya kirkiro wannan. 

To, kun san a cikin ‘ya’yansa akwai Mahdi ko? Ya yi barna kuwa Mahdi din nan, Mahdin Ma’amon kenan ba, ya yi sarauta, ya yi barna sosai, ya yi wa iyalan gidan Annabi barna, amma ya rika amsa sunan AlMahdi. To, yanzu ya tabbata ba shi ne Mahdi din ba.

SUN YI YUNKURIN HANA HAIHUWAR IMAM MAHDI (AS):

To, Mahdin sosan sun san cewa zai zama Hujjatu Binil Hasan, ranar haihuwarsa sai da suka yi duk abin da za su yi don su hana. Shi Sarkin Musulmin wannan lokacin ya yi shiru, daren nan bai yi bacci ba. Tun ma kafin rannan, yadda Fir’auna ya sa ‘muraqaba’ a gidajen Banu Isra’ila don kar a haifo Musa (AS) haka wannan sarkin Musulmin wannan lokacin shima ya saka ‘muraqaba’ a gidan Imam Hasan Al-Askari (AS).

Ya saka ‘yan rahoto, ‘yan SSS mata da SSS maza (ina misali da SSS ne don haka ake kiran jami’an tsaron farin kayan Nijeriya), wato ya saka jami’an tsaro na ciki boyayyu suka saje, wasu suna cikin gidan, mata, wasu kuma suna aiki a gidan, maza, ana kai masa rahoto. Yak an tambaya akwai wata mace mai ciki a gidan? Suce babu. Ko kuyanga? Su ce lallai babu Kuyanga mai ciki. Sai yace da an ji labari ko an ga alamar ciki a sanar da mu.

To, ana nan ana ‘muraqaba’ ba wanda ya ga alamar ciki. Yace shi bai yard aba, dole akwai mai ciki, don Annabi baya karya, suma A’imma basu karya, sun kuma ce shi Hasan din nan shine Limami na 11, kuma lallai dansa ne zai zama na 12, kuma an haifi ranar da za a haide shi. Duk an fada ai, har daren Nisfu Sha’aban din. Yace wannan daren ne. Yace, an riga an fada mana wannan daren ne daren haihuwarsa. Ba fa kowane Nisfu Sha’aban ba, wannan ‘kususan’ na ranar da aka haife shi din ne, saboda haka zaunannen abu ne, sun sani sarai.

Sai ya sa aka baza masu gadi ko ta ko ina, su ‘yan rahoto suka ce lallai ba mace mai ciki a gidan. Ita Sayyida Narjees tana da ciki, amma ba wani alamar mai ciki a tare da ita, ba yadda za a yi mutum ya ganta yace tana da ciki.

To, sannan da dare ya yi Imam Askari (AS) ya aika a kira ‘yar uwarsa Hakeema ta zo don ita za ta yi unguwar zoma. Ya aika ta zo. A kan hanya duk akwai masu gadi a cikin daren nan, in sun wuce sai su ga dogari, in sun karkata can sai su ga dogari, in sun bi ta wannan lungun sai su ga dogari, karshe dai inda suke tsammanin za su bi babu dogarin, suna fitowa sai gasu ga dogarin, ba batun inda za su kauce su labe, kawai sai ga dogari dam a gabansu. Sun ji tsoron zai gansu; wanda ya je kiran Sayyida Hakeema da ita Hakeemah din. 

Sai suka kawai dogarin ya yi wani garau, sau suka wuce ta gabansa bai gansu ba. Suka wuce suka ganshi yana ta leke yana jiran ya ga ko zai ga wasu. Tunda sun san dama an ce ita Hakeem ace unguwar zoma, don haka zai ga ta inda za ta bi. To kuwa sai ta wuce ta gabansa.

Ta je gidan, tace meke faruwa ne? Imam Hasan Al-Askari yace haihuwa za a yi. Wa za ta haihu? Yace Sayyida Narjees ce. Tace ni ban ga alamar ciki tare da it aba. Tace lallai ita za ta haihu, yau kuma za ta haihu.

Ya zauna a daki yana ‘controlling’, kamar ‘remote control’ yana karatun Inna anzalnahu Fi lailatil Qadr, nan kuma a dakin ana jiran lokaci. Zuwa can kuwa lokaci sai ga alamar naquda. Aka haifi wannan Haske wanda Allah Ya yarda shine (Limamin karshe). 

To, abin da mutum bai isa ya hana ba kenan. Duk da cewa akwai jami’an tsaro na boye a gidan amma ba wanda ya san an yi haihuwar. Amma shi Sarkin Musulmi ya san rannan za a haihu. Yace musu lallai an yi haihuwa. Suka ce ba a haifi kowa ba. yace lallai an yi, lallai an yi haihuwa. Suka shafa su basu ga komai ba.

Da yake Sahibul Asr Waz Zaman (AS) sai ya yi girman wata daya a kwana daya, bayan kwana bakwai sai aka ga wani kamar yaro yana kaiwa da komowa a gida ya dan yi girma haka. To ya za a yi ace an haifi yaro dan wata kamar bakwai, kaga ba za a ce an haife shi jiya ba kenan ko? Ana nan sai aka gay a fara tafiya ma, nan da nan ya girma.

To, labarin kissar haihuwar Sahibul Asr Waz Zaman in ana fadawa mutumin da ba ma’abocin yaqini ta hanyar Ahlulbait (AS) ba, sai dai ya yi garau yace ana sharara karya. Kuma ba zai taba ganewa ba, shi yasa wadansu abubuwan mun barwa kanmu, wanda ya sani ya sani, wanda bai sani ba kuma shikenan. In muka ce maka an dauke shi an yi saman bakwai da shi, ka ga wani zai wage baki haaa! Saman bakwai!? Muce Mala’iku suka dauke shi suka yi sama da shi. Haaaa! Kaji su Shi’an nan kenan. To, In baka da rabo ba yadda za ka gane. 

Amirulmuminin (AS) yana cewa al’amarinsu mawuyacin al’amari ne, sai zuciyar da Allah ya tatsi imani daga ciki, ba kowanne ke gane al’amarinsu ba. Yauwa. Amma su wadannan (masu mulkin) sun san al’amarin, don haka sai suka fara jin labarin akwai yaro. Sai aka ce ai gashi ashe ta haihu, ba wanda ya sani har gashi yaro yana kaiwa da komowa.

Za mu cigaba.
— Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H).
www.cibiyarwallafa.org

Post a Comment

Previous Post Next Post