Offline

JAWABIN SHAIKH ZAKZAKY (H) YAYIN NISFU SHA’ABAN 1443/2022


A’uzu Billahis Sami’ul Aleem, Minash-shaidanil la’inir rajeem, Bismillahir Rahmanir Raheem. Wa sallallahu Ala Sayyidina wa Nabiyina wa Shafi’i Qulubina Abil Qasim Mustapha Muhammad wa ala alihid Dayyibinad Dahireenal Ma’asumiyn, siyama Baqiyatullahi fil ard Sahibul Asri Waz Zaman Arwahuna lahu fidha. 

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi Ta’ala wa barakatuhu.

To, zan fara da taya mu murna na zagayowar wannan rana mai alfarma; ranar Nisfu Sha’aban, wacce ta dace da ranar haihuwar Sahibul Asr Waz Zaman (AJ). Nisfu Sha’aban dama sanannen lokaci ne tun kafin haihuwar Sahibul Asr Waz Zaman (AJ).

ƘISSAR ASALIN DU’A’U KUMAIL:

A kalaman Amirulmuminin (AS), an tambaye shi dangane da fassarar (fadin Allah Ta’ala): “Inna anzalnahu fi lailatin Mubarakain inna kunna Munzirin - Fiha yufraqu kullu amrin hakeem.” (Dukkhan: 3-4). Sai aka tambaye shi wane dare ne wannan (lailatin Mubaraka din)…, sai yace daren Nisfu Sha’aban ne. Yace kuma duk wanda ya karanta addu’ar Khidir a wannan dare za a kankare masa zunubansa.” 

To daga cikin Sahabbansa akwai Kumail Bin Ziyad (RA), sai ya bi Amirulmuminin (AS) kafin ya shiga gida, sai yace ka ambaci addu’ar Khidir, wace addu’a kenan? Sai Imam (AS) yace, lallai kai sahibtarka da mu ya dade ya Kumail, dauko dauko takarda. Da ya dauko takarda da Alkalami sai Amirulmuminina (AS) ya yi masa shifta (ya biya masa). Wannan addu’a da muke karantawa mai tsawon nan. Ko da yake Amirulmumin (AS) yace addu’ar Khidir ne, amma mu ana saka shi a cikin addu’o’in Amirulmuminin (AS) ne, tunda ta wajensa aka ji. 

Khidir dai suna ne sananne, mutanenmu su kan saka suna. Wani bawan Allah ne da ba a ambaci sunansa a cikin Alkur’ani ba, amma an fadi kissarsa. Shine wanda kissarsa da Annabi Musa, wanda ya zo a Suratul Kahf. Wanda ya hadu da wani bawa cikin bayin Allah, da Allah Ta’ala yake cewa: “Fawajada Abdan min Ibadina, atainahu Rahmatan min indina, wa allamnahu min ladunna ilma.” (Kahfi: 65). 

Inda (Allah) yace, za ka gamu da wani bawa daga cikin bayinmu, wannan bawan mun bashi rahama daga wajenmu, kuma mun sanar da shi ilimi daga wajenmu. To, shine shi kuma Annabi Musa da kwadayin ilimi, ya tashi takanas, ya yi doguwar tafiya har ya hadu da wannan malami.

To, ba kissar zan kawo ba, kissar Khidir sananne ne. Khidir din nan mutane suna cewa shi wani irin mutum ne? Wasu su ce yana jerin Annabawa, wasu su ce wani waliyin Allah ne cikin waliyan Allah, haka nan dai. To, amma wani abu da aka sani, Khidir Allah ya tsawaita ransa. Ba mu san tun yaushe aka haife shi ba, amma kuma ya daden gaske. Ga kissarsa a zamanin Annabi Musa (AS).

Amma akwai lokacin da Amirulmumina ya ga wani yana dawafi, yana addu’ar ‘Subhanallah min almizan…’ Sai Amirulmuminin yace Khidir ne ko? Sai yace eh, shine. Kaga tun wancan lokacin yana nan. tsakanin Manzon Allah (S) da Annabi Musa (AS) kusan shekara dubu biyu da dori, amma kuma shi yana nan da rai. To Khidir har yanzu yana nan? Wasu suna cewa har yanzu yana nan. An sha a awani zamani sai a ce an ga Khidir, a wasu zamuna wasu su kan ce sun ganshi. 

To, addu’arsa ce wannan addu’ar; Da’a’u Kumail, duk da ta shahara da Addu’ar Kumail Bin Ziyad, don ana ce mata Du’a’u Khumail, wacce mu kan yi duk daren Juma’a.

To, da Amirulmuminin (AS) ya ba (Kumail) wannan addu’ar, sai yace ita wannan addu’a ‘mukaffarat’ ce tsakanin karantata da karantata. In ka karantata a Nisfu Sha’aban an yafe duk zunubanka, in wata Nisfu Sha’aban din ta zo ka sake karantata, shima sai a shafe zunuban karshen karanta Du’a’u Kumail din da wannan.

Yanzu muna ce mata Du’a’u Kumail, saboda shi Kumail din ne ya karba wajen Amirulmuminin (AS), amma ba addu’ar Kumail din ne ba. Amma har ila yau muna ce mata addu’ar Amirulmuminin (AS). In ka duba Sahifa Alawiyya za ka ganta a ciki, tunda wajensa shi kuma kawai aka ji. To yace addu’ar Khidir ne.

Har ila yau Amirulmuminina (AS) yace ita kuma ‘mukaffara’ ce tsakanin karantata da karantata. Saboda haka in kana iyawa ba kawai so daya a shekara ba, in kana iyawa ka karantata duk wata, in kana iyawa ka karanta duk mako; duk daren Juma’a. Shi yasa ya zama mana zaunannen abu mu kan karanta Du’a’u Kumail Bin Ziyad a duk daren Juma’a. To, amma musamman daren Nisfu Sha’aban, tunda a kan wannan aka ruwaito ta. 

MUHIMMANCIN DAREN NISFU SHA’ABAN:

Dalilin da ya sa na kawo wannan ya nuna cewa Nisfu Sha’aban sanannen abu ne dama. Kamar yadda ruwayoyi daban-daban suka zo kuma aka ce a wannan dare ne, kamar yadda aka ce “Fiha yufraqu kullu amrin hakeem.” Rannan ne ake rarraba komai na umurnin Allah; abubuwan da za su faru a shekara duk sai a rarrabe su.

 To, kuma za ka ga irin wannan ruwayar dangane da Lailatul Kadr. “Inna anzalnahu fi lailatil Kadr” da kuma “Inna anzalnahu fi lailatin Mubaraka.” Wanne ne ba wanne ne ba? Sai aka ce ai muna cewa Layalul Kadr. Layalul Kadr a wajenmu suna da yawa, Lailatu Nisfu Shaaban yana cikin Layalul Kadr. 

Duk abin da zai faru a shekara duk rannan za a tattara a rubuta a ajiye. Ka ga in ba a shigar a rannan ba, to ba batun a zartar. Tunda kamar ‘file’ ne aka kai, ana jira a sa hannu. To in akwai ranar sa hannun, duk aka kai aka saka a ka fito da su, to ‘File’ din da ba a kai ba za a sa hannun? Yauwa. Tunda daren Nisfu Sha’aban ake rubuta komai da komai, amma ba rannan ake zartarwa ba.

Sannan sai Layalul Kadr din nan guda uku na cikin Ramadan, to daya sai a zo a tantance a ga wanne ya kamata a zartar wanne za a wurgar? Sai a ciccire wasu, sai a ce to wannan. Sai a sake kwakkwafawa. Don Layalul Kadr din na Ramadan guda uku ne, to sai a sake kwakkwafawa a dare na gaba, a sake tantancewa. To, karshe daren Lailatul Kadr sai a saka hannu, an zartar. To rannan duk abin da aka zartar ya riga zartu, duk abin da zai faru a shekara an riga an fada. 

To, tun daren Nisfu Sha’aban sai ka roki komai da komai da kake fatan a yi maka a shekara. Wato kenan in kana so a shigar da wani abu naka, to tun a daren Nisfu Sha’aban za ka nema. In ka nema aka samu aka shigar, to za ka yi fatan a zartar maka a daren Lailatul Kadr. Amma in baka samu ya shiga ba, to ba ma za a tantance shi ba ballantana ma a zartar, ace ya zama ‘jazaman’ wannan. 

To ‘wufudul hajj’ duk rannan ake yi. A ce to wadannan duk an rubuta musu za su je Hajji. To zuwa Hajji kamar yadda muka sani wani zaunannen abu ne. Hanzu an hana zuwa Hajji. Bara ba abin da ba a yi ba a Duniya. An yi kwallo, an yi dambe, an yi rawa, an yi kade-kade, an yi haduwar ‘yan kida, duk an yi, amma banda Hajji. Saboda Coronta ta hana Hajji. Amma wasan kwallo, ba Corona a wajen wasan kwallo, har a Saudi Arabia an kira gangamin ‘yan rawa na duniya sun wataya, ba a rufe hanci ba, har da maza da mata sun yi rawa, an halatta musu wannan karon. Ba Corona a gidan rawa. Amma an hana Hajji. Ka san me yasa aka hana Hajji? Corona. Wai ana gudun kar Corona ta zo ta kama Mahajjata, to an hana su.

To, idan aka rubuta za ka je Hajji, to ko na ki ko an so za ka je. In an rubutaka a cikin wadanda za su je Hajji, to Hajji ya zartu, za ka je Hajji ko ba a so. To, ba lalai ka je Hajjin da gangar jikinka ba, tana iya yiwuwa baka je da gangan jikinka ba amma za a rubuta maka (ladan) Hajjin.

Akwai (kissar) Imam Jafarus Sadik (AS) wata shekara ana Arfa, mutane sun cika makil a Hajji. Sai wani yace ma Imam (AS), “Ma aksaral Hajij!”, wato kai, mahajjata sun yawaita. Shi kuwa sai Imam (As) yace masa: “Ma aksaral lajij!”, wato Me ya yawaita masu hayaniya? Wadannan ‘Lajij’ ne, masu iface-iface, ba ‘Hajij’ bane ‘Lajij’ ne. Wato yace masu hayaniya dai sun yi yawa, ai mutum biyu ne kawai suka yi Hajji, da ni da wane (ya fadi sunan wani mutum).

Sai Imam yace wa wannan mutumin zo ka duba, sai ya sa yatsunsa masu albarka tsakanin ‘sababa’ da ‘wusda’ (in na gwada muku ba yana nufin yatsuna bane, don akwai wasu misalai da na kan qi na nuna tunda yatsuna ba suna da kyau bane, kawai na je ina gwada yatsun bayin Allah). Sai yace masa zo ka leka tsakanin ysatun ‘sababa’ da ‘wusda’. Sai ya buda masa tazara. Sai ya leka, sai ya ga daga kura, sai kare, sai dila, sai kerkeji, gasu nan dai, sai ya ga duk namun daji ne kawai. Yace to kaga wadanda suke wajen a ainihin hakikaninsu. To shi Imam yana ganinsu a ainihin hakikaninsu ne. ‘Lajij’ ne kawai suka hadu. Sai yace da ni da wane ne kawai muka yi Hajji. 

To, sai ya tabbata wannan da Imam ya ambata bai je Hajjin ba. Aka ce ya tara guzurinsa na halas. Don ka san mutane da yawa sun dauka ka je ka zazzagaya ka yi wannan shine kawai Hajji. Ina! Da wane guzuri ka je? Guzuri muhimmi ne. Yauwa. Da guzurin halas ka tafi? Halas kake ci? Suturarka na halas ne? In aka samu wani ba haka bane, sai a ce wannan ka zo ihu ne, ka gama iface-ifacenka ka koma gida.

To, sai ya zama shi wannan ya yi tanadin guzurinsa za shi Hajji, har zai tafi sai wani makwafcinsa lalura ta same shi na rashin lafiya, aka rasa kuma yadda za a a masa magani, sai yace to ga kudin ai masa. To, sai aka rubuta shi a cikin Mahajjata. Ka gani. Wato abin da ya sa nake muku dogon bayanin nan, a gane tana iya yiwuwa mutum ya je Hajji amma bai je ba (ba a karba ba).

Har ila yau, akwai wasu ayyuka za ka gansu a Ma’asurai, ace in mutum ya yi wannan aikin, Allah Ta’ala zai halicci Mala’ika da siffarsa, irinsu daya, in ka ga wannan Mala’ikan za ka ce wane ne. Kamar yadda in da an rubuta Sayyid Khidir, zai shiga Aljanna, in ka ganshi kace Sayyid Khidir, sai ka ji ya maka shiru, ashe ba shi bane, shi wannan Mala’ika ne, amma da siffarsa tsaf. Sai ya yi Hajji, ya yi dawafi da komai da komai, sai a rubuta ma wannan ladan. 

Ka ga in an rubuta maka Hajji, tana iya yiwuwa ma ba kai ne za ka je ba, ta yiwa wani Mala’iki ne zai je maka, ka ga hajjinka tsaf, ladanka tsaf. Nan an hana ka an ce akwai Corona, amma kuma ka je Hajji din ko ba a so. Tana iya yiwuwa kuma in Allah Ta’ala ya so ka je ma da jikinka ka tafi din kai da kanka, ko ba a so.

To, wannan ba Mahajjata kawai ake rubutawa ba, duk abubuwan da za su faru a shekara na alkairi da kuma masa’ib. To, komai alkairi ne (ga Muminai), kamar yadda ya zo a Hadisi duk abin da ya samu mumini alkairi ne. Idan ni’ima ta same shi ya gode sai ya zama masa alkairi. In kuma musiba ta same shi ya daure sai ya zama masa alkairi. To, sai mu ce da ni’imomin da za a bayar da musibobin da za a sa, duk a wannan daren ake rubutawa, za a gama rubuta duk.

Saboda haka ne ma a wannan daren sai ka nemi tsari daga dukkan musibobin wannan shekara, ka kuma roki Allah duk alkairan wannan shekara.

Za mu cigaba.
— Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H).
www.cibiyarwallafa.org

Post a Comment

Previous Post Next Post