Offline

DUK MA’ASUMAI SUN YI MAGANA SUNA YARA



Kuma da gani ka san su yadda suke, duk A’imma (AS) gaba dayansu ba wanda bai yi magana yana cikin uwarsa ba, ba kuma wanda bai yi magana yana jariri ba. manta da batun Ama na cewa wai mutum nawa ne suka yi magana suna jariri. Duk Annabawa sun yi magana suna jarirai, ba Annabi Isa ne kawai ya yi magana yana jariri ba. Duk Ma’asumai sun yi magana suna cikin uwarsu. Duk Ma’asumai sun yi magana a ranar da aka haife su.

To, da ganin Imami, ba wani abu ne da zai buyawa mutum ba, har da makiyi, zai gane cewa wannan ba mutum ne ‘adiy’ ba, don zai ga cewa wannan mutum ne yana magana da ilimi, amma yana karamin yaro, wanda a al’adance abin da aka sani sauran mutane a kan haife su ne su yi jarirantaka, a yi musu tarbiya har su fara koyon ‘lugga’ a hankali.

Yaro ya fara cewa Ba, ko Ma, shi yasa ma sai ka ji y ace Ba-Ba, wasu kalmomin yara ke kirkirowa ‘universal’ ne, shi yasa ka ga duk duniya ake cewa uba Baba. Kowane Harshe Baba yake cewa, saboda yara ne da farko sai su ce Ba-Ba, ko Ma-Ma, daga nan za ka ga ko a wane harshe ne in aka ce Mama za ka ga haka nan ne. To a kan fara koyawa yaro luggan da yake a muhallin da yake, ya koya a hankali a hankali, har ana mamaki ya fara cewa kaza, ya fara cewa kaza.

To, su kuwa (Ma’asumai) ranar da aka haife su suke yin magana tangaran, ‘bi lisanin Arabiyyin fasih’, tangaran, mutum ya yi magana fes. Kuma da ganin yarintarsu kai ka san ba yaro ne ‘adiy’ (gama-gari) ba. Duk kuma haka suke, tun daga na farkonsu ba wanda ya yi kama da yaro ‘adiy’.

Saboda haka ko Ma’amun da yake gwadawa, lokacin Imam Jawad yana yaro ai ya gwada sai ya gane cewa wannan shine Imam din, ko da gani. Saboda ya fahimci gashi yaro karami gashi (mai ilimi). Kun san labarin yadda suka yi da Yahya Bin Askam ko? Da Ma’amon ya tara Malamai kan a yi ‘yar qure, sai shi Yahya Bin Askam ya tambayi Imam me za ka ce kan wanda ya yi farauta yana Ihrami da Hajji? Kun san wannan Kissar ba sai na kawo muku ba ko? 

Sai da Imam ya jaddada masa mas’ala kusan 50; yace to shi farautan da ya yi da daddare ne ko da rana? A waje kaza ya yi ko a kaza? Abin da ya farauto din tsuntsu ne ko dabba? Ya dinga karanto masa. Sai kawai Alkalin Alkalai ya wage baki (yana mamakin) wannan wane irin ilimi ne? Kuma gashi yaro. Sannan sai Imam (AS) ya warware masa kowanne, in kaza ne hukuncinsa kaza ne, in kaza ne hukuncinsa kaza ne, har hukunci kusan 50 daban-daban.

Kowa sai ya wage baki yana cewa wannan abin mamaki, ina wannan yaron ya yi karatu? Sai shi Ma’amon yace ai na fada muku, wannan shine limamin zamanin nan, wannan magajin babansa ne. Na gwada muku ne. Shi yasa ma lokacin da Ma’amon yana son ya aurarwa da (Imam Jawad) da ‘yarsa, sai su Banul Abbas suka ki yarda, sai ya yi wannan gwajin, sai suka ce kai kai kai, wannan wane irin ilimi ne haka, matashi da wannan ilimin.

To, su kan bambanta (da sauran mutane) duk cikansu gaba dayansu, don iliminsu ba irin namu ne da mukan je makaranta a rike ko a manta ba. Ballantana wani lokaci a manta, kuma ma in mutum ya tsufa ya manta. To su nasu in ma Allah ya kaddarawa dayansu tsufa to baya manta komai.

ALLAH YA BOYE IMAM (AJ) DAGA GANIN WADANDA BASU BIYAYYA GARE SHI:

To, shikenan, ina dai fada muku, Sahibul Asr Waz Zaman girmansa sun riga sun san shi ne. Kuma sun yi kokarin su kawar da shit un yana karamin yaro, sun yi abubuwa daban-daban, amma dai Allah bai yarda ba, har sai da ta kai ma lokacin da suka lura da cewa su mabiya iyalan gidan Annabi (S) basu cikin kunci dangane da al’amarin ko suna da shugaba bayan Imam Hasan Al-Askari (AS). Aka rasa kuma inda shugaban nan yake. Suka yi ta fafutukan su ganshi. Amma yana nan tare da mutane, sai dai ‘qalilan’ ne suka san inda yake. 

Amma su a lokacin maqiya suna nemanshi ne wai su kashe, sai ya zama sun hana abin da Allah ya yi alkawari kenan. Ka dan ba a hana abin da Allah ya riga ya shirya zai yi ko? Ba zai yiwu ba, amma dai su makiya dai suna da nufin za su yi wannan. To, amma dai Allah bai basu ikon ma su san ina yake ba, har ya girma. 

Amma suna ganin su mabiyansa basu da wata matsala. Duk wani abu in ya taso, za su ce ai mai zamanin yace mana kaza. Su kan ce a’a! to a ina kuke ganinsa ne? To, Allah Ta’ala ya boye shi daga ganin wadanda basu biyayya gare shi, sai mabiya ke ganinshi. Su mabiya suna da yakini, sauran mutane kuma wadanda suka san akwai shi suna kokarin su hana amma basu san inda yake ba.

To har izuwa lokacin da ya shiga karamar Gaiba, yana amfani da ‘yan sakonsa, yana magana da su ‘yan sakon su kuma suna isarwa. Ya yi ‘yan sako har guda hudu, sannan daga dan sako na hudu, yace daga kai ba wani dan sakon da za a yi, yanzu kuma za a shiga Gaiba doguwa. Ita wannan muke a ciki.

SAHIBUL ASR (AS) KE TAFIYAR DA ABUBUWA YANZU HAKA:

To, amma har yanzu Sahibul Asr Waz Zaman (AS) ke tafiyar da abubuwa. Na sha fadin wannan cewa, su fa Shi’a ba suna jiran Mahdi ya zo ne su bi shi ba, su shi suke bi yanzu din nan ma. Ka san akwai masu tunanin Mahdi zai bayyana, in ya bayyana za a bi shi. To mu shi muke bi yanzu. Kuma yana nan tare da mu. Shi ke kwakkwafa al’amura.

A cikin Malamanmu akwai Shaikhul Mufid, babban Faqihi, wanda aka ce ya tab aba da fatawa, sai ya zama ya gano ya yi kuskure. Fatawar dangane da mace in ta rasu alhali tana da tsohon ciki, ana iya yankawa a fitar da dan? (Ya kan yiwu haka nan, amma sai an yi da gaggawa, in aka dan jima kadan shima dan da ke cikin zai rasu). To, sai (Shaikh Mufid) yace eh ana iya yi, amma a yanka ta waje kaza. to, sai daga baya ya ga ashe ta inda yace a yanka din ba nan ne ya kamata ba. Sai abin ya dame shi, sai ya dade bai fito ya ba da karatu ba. Shiri-shiru-shiru, yana cewa yanzu yadda na yi kuskuren nan da ace an je an aikata wannan, ai an yi kuskure. Abin ya dame shi, don haka sai baya fitowa makaranta.

To, wata rana sai ya ji an kwankwasa masa kofa, aka ce fito ka koyar da mutane fiqihu suna da bukatarka. Naka kai ka koyar, mu ne masu gyarawa. To, kaga tabbatan wane ne ya gyara masa kuskuren tun asali? Da ya ba da fatawar ai ba a kai ga aikatawa ba aka gyara masa, ashes hi Sahibul Asr din ne ya gyara masa. Yace naka koyarwa, namu gyara. Ka je ka koyar mutane suna bukatarka.

Idan aka kuskure sai ya kwakkwafa. Lokacinsa ne, yana ‘supervising’ duk abin da muke yi, yana ‘muraqaba’ yana bi daki-daki.

WASU KISSOSHIN GANIN SAHIBUL ASR WAZ ZAMAN (AS):

To kuma kissoshi na ganin Sahibul Asr Waz Zaman (AS) za ka ji shi daban-daban a wannan zamani namu. A zamanin da za ka ga magabata sun yi rubuce-rubuce daban-daban sun rubuta cewa sun ga Sahibul Asr (AS). 

Kamar ina jin ko a Muqaddiman littafin Sawabul A’amal wa Iqabul A’amal ne, Shaikh Saduq ya rubuta cewa yana Dawafi sai ya ga Sahibul Asr Waz Zaman (AS), sai yace ya rubuta littafi. Sai yace ai na rubuta, sai yace banda wannan ka rubuta wani. Sannan sai ya zo ya rubuta wannan littafin, a cikin muqaddiman littafin yace shi ya gani, yace masa ya rubuta.

Sannan kuma dai Malamanmu in ka lura da su za ka ga suna ce rana kaza muhimmiyar rana ce a wajensu. Kamar Sayyid Ibn Dawus, akwai randa yace shi wannan rana muhimmiyar rana ce a gare shi da jikokinsa, su yi godiya ga Allah, don rannan ne ya kasance a gaban Suldanil Asr (AS).

WASU NA IZGILI KAN IMAM MAHDI (AS):

Za ka ga da yawan mutane suna ba da labari, na magabata da ma wannan lokacin. Sai ka sha mamaki kan ganin Sahibul Asr waz Zaman (AS). Don wasu suna yi mana izgili, masu izgilin ba za su taba gane komai ba, ba kuma za su ganen ba. Suna cewa kullum baku da wata magana, sai cewa akwai wani shugaban da ba a ganinsa. To a ina yake? Kullum ku kuna da shugaba amma ba a ganinsa?

To, ko kana da shugaba, wanda kai kake gani, dole ne ka yi ta ganinsa? Yanzu wannan zanqalelen kanjamammen, mutum nawa suke ganinsa a cikin mabiyansa? Wasu shine waliyinsu amma ba ganinsa suke ba, illa iyaka su ce zankalele yace kaza, kanjamamme ya fita neman magani. Illa iyaka, amma ba ganinsa suke ba. amma ka ga shine waliyinsu, shine shugabansu. To, kaga su ma kenan. Ballantana wanda yake Hujjar Allah a doron kasa, shine kake bukatar lallai-lallai sai kowa ya ganshi? Ba lallai ne ya zama kowa ya ganshi ba, amma yana nan.

To, suna izgili har ma su kan ce wai shugaban naku ina lambar wayarsa ne mu buga masa? GSM dinsa, Mobile, sai mu buga masa waya. Wato Izgili suke da wannan. Suna ta izgili. (Sai mu ce) ku ba da kokari, ku ne za ku yi asara insha Allah. Mu muna da yaqini ne, ba muna hasashe bane.

JAWABIN SHAIKH ZAKZAKY (H) YAYIN NISFU SHA’ABAN 1443/2022 (3)

Za mu cigaba.
— Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H).
www.cibiyarwallafa.org

Post a Comment

Previous Post Next Post