Offline

TAKAITACCEN TARIHIN IMAM MAHDI(AS); KHALIFAN ANNABI MUHAMMAD(SAW) NA KARSHE; A JERIN KHALIFOFI 12.


IMAM AL-MAHDI(AS); HUJJAR ALLAH, WANDA DUNIYA KE SAURARON BAYYANARSA:



Nasabarsa ta bangaren mahaifinsa: Muhammad Al-Mahdi (as) (Imami na 12), dan Imam Hasan Askari(as) (Imami na 11), d’an Imam Ali Al-Hadi(as) (Imami na 10), d’an Imam Muhammad Al-Jawad(as) (Imami na 9), d’an Imam Ali Ar-Rida(as) (Imami na 8), d’an Imam Musa Al-Kazim(as) (Imami na 7), d’an Imam Jaffar As-Sadiq(as) (Imami na 6), d’an Imam Muhammad Al-Baqar(as) (Imami na 5), d’an Imam Ali Zainul-Abideen(as) (Imami na 4), d’an Imam Husain Sayyidus-Shuhada(as) (Imami na 3); kanin Imam Hasan Al-Mujtaba(as) (Imami na 2); ‘ya’yan Imam Ali bin Abi Talib(as) (Imami na 1) da Sayyida Fatimah Az-Zahra(as) ‘yar Annabi Muhammad(saw).

Nasabarsa ta bangaren mahaifiyarsa: Muhammad Al-Mahdi(as) d’an Narjis Khatoon; nasabarta tana tukewa ne da Sham’un; Wasiyyin Annabi Isah(as). Ko da yake akwai wasu hadisai da su ke nuna sunan mahaifiyar Imam Mahadi(as) shine; Maryam bint Zayd ko Sayqal…

Lakabinsa: Al-Mahdi, Al-Hujja, Al-Qa’im, Bakiyyatullah, Bakiyyatul-Anbiya, Gausul-Fukara, Khatamil-Awsiya, Al-Muntazar, Hujjatullah, Khatamul-A’immah, Khashiful-Gumma, Khalafus-Salih, Khalifatullah, Khalifatur-Rahman, Imamul-Insi-Wal-Jin, Sahibur-Raja’a, Sahibuz-Zaman, Ad-Da’iy, As-sa’a, Sahibud-Dar, Sahibun-Nahiya, Sahibul-Asr, Al-Fakih, Al-Farajul-A’azam, Al-Gayatul-Kuswa, Katilul-Kafara…

Al-Kunyarsa: Abul Kasim.

Ranar Haihuwarsa: Daren Juma’a, 15 ga watan Sha’aban.

Garin da aka haifesa: Samarra (Iraq).

Shekarar haihuwarsa: Shekara ta 255 H. 2 August 869 M.

Farkon Imamancinsa: 8 ga watan Rabi’il-auwal, shekarata 260 H. 5 January 874 M. – har zuwa yanzu.

Shekarunsa biyar ne yayin da mahaifinsa ya bar duniya. Allah ya zabe shi halifa kuma ya sanya shi Imami kamar yadda ya sanya Annabi Yahya(as) da Isa(as) annabawa suna kanana yara.

A halin yanzu yana raye, ana arzuta shi, yana jiran umarnin Allah ne kawai ya bayyana, don ya cika Duniya da adalci da daidaito kamar yadda ta cika da zalunci da rashin daidai.

IDAN MUN YARDA ALLAH(SWT) YANA DA IKO AKAN KOMAI; MENENE ABIN MAMAKI DON YA RAYA IMAM AL-MAHDI(AS) SAMA DA SHEKARU 1184???

ME YA SA AKE CEWA; MAHDI(AS); MAI DOGON ZAMANI (SAHIBUL-ASR WAZ-ZAMAN)???

Shekarun Imam Al-Mahdi(as) yanzu a Duniya 1184. Idan mun lissafo daga haihuwarsa zuwa yanzu, (1439 H – 255 H = 1184).

Zai yiwu mutum ya yi shekaru 1184 a Duniya?

Zai yiwu. Tarihi ya tabbatar mana akwai mutanen Allah(t) ya rayar sama da shekaru dubbai, wasun Annabawa(as) ne, wasu kuma ba Annabawa(as) ba ne. Misali:

1. Annabi Nuhu(as); ya rayu shekaru 2500, ya yi shekaru 850 gabanin aiko masa sako, ya yi shekaru 950 yana da’awa. (Da nasssin Al-Qur’ani). Sannan ya yi shekaru 700 bayan halakar da mutanensa.

Qur’ani ya tabbatar mana Annabi Nuh(as) yayi shekaru 950 yana da’awa:

ﻭَﻟَﻘَﺪْ ﺃَﺭْﺳَﻠْﻨَﺎ ﻧُﻮﺣًﺎ ﺇِﻟَﻰ ﻗَﻮْﻣِﻪِ ﻓَﻠَﺒِﺚَ ﻓِﻴﻬِﻢْ ﺃَﻟْﻒَ ﺳَﻨَﺔٍ ﺇِﻟَّﺎ ﺧَﻤْﺴِﻴﻦَ ﻋَﺎﻣًﺎ ﻓَﺄَﺧَﺬَﻫُﻢُ ﺍﻟﻄُّﻮﻓَﺎﻥُ ﻭَﻫُﻢْ ﻇَﺎﻟِﻤُﻮﻥَ (ﺍﻟﻌﻨﻜﺒﻮﺕ : 29‏).

Malamai sun yi sabani akan shekaru nawa Annabi Nuh(as) ya yi kacokaf a Duniya; malaman Ahlus-Sunnah sun kawo ra’ayoyin Sahabbai, Tabi’ai… mabambanta akan hakan, mafi rinjayen zantukan suna tabbatar Annabi Nuh(as) yayi shekaru sama da 1000 a Duniya. Mai bukatar karin bayani zai iya duba:

– ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ﺍﻟﻌﻈﻴﻢ : ﻻﺑﻦ ﻛﺜﻴﺮ : 6 / 268.

– ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺍﻟﻘﺮﻃﺒﻲ : 13 / 332.

– ﺍﻟﻄﺒﺮﻱ : ﺟﺎﻣﻊ ﺍﻟﺒﻴﺎﻥ : 20 / 17.

– ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺣﺎﺗﻢ : ﺍﻟﺘﻔﺴﻴﺮ : 1804، 18043.

– ﺍﻟﺴﻴﻮﻃﻲ : ﺍﻟﺪﺭ ﺍﻟﻤﻨﺜﻮﺭ : 6 / 455. 6 / 456

– ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺷﻴﺒﺔ : 7 / 18.

– ﺍﻟﺤﺎﻛﻢ ‏: 9 / 251، ﻭﺻﺤﺤﻪ ﻭﺍﺑﻦ ﻣﺮﺩﻭﻳﻪ.

Ruwayoyi daga Ahlul-bayt(as) suna tabbatar da cewa; Annabi Nuh(as) ya rayu shekaru 2500 a Duniya:

ﺣﺪﺛﻨﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ ﺍﻟﺤﺴﻦ ﺑﻦ ﺃﺣﻤﺪ ﺑﻦ ﺍﻟﻮﻟﻴﺪ(ﺭ) ﻗﺎﻝ: ﺣﺪﺛﻨﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﺍﺑﻦ ﺍﻟﺤﺴﻦ ﺍﻟﺼﻔﺎﺭ، ﻋﻦ ﺃﺣﻤﺪ ﺑﻦ ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ ﻋﻴﺴﻰ، ﻋﻦ ﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﺍﻟﺤﻜﻢ، ﻋﻦ ﻫﺸﺎﻡ ﺑﻦ – ﺳﺎﻟﻢ، ﻋﻦ ﺍﻟﺼﺎﺩﻕ ﺟﻌﻔﺮ ﺑﻦ ﻣﺤﻤﺪ(ع) ﻗﺎﻝ: ﻋﺎﺵ ﻧﻮﺡ(ع) ﺃﻟﻔﻲ ﺳﻨﺔ ﻭﺧﻤﺴﻤﺎﺋﺔ ﺳﻨﺔ. ﻣﻨﻬﺎ ﺛﻤﺎﻧﻤﺎﺋﺔ ﻭﺧﻤﺴﻮﻥ ﺳﻨﺔ ﻗﺒﻞ ﺃﻥ ﻳﺒﻌﺚ، ﻭﺃﻟﻒ ﺳﻨﺔ ﺇﻻ ﺧﻤﺴﻴﻦ ﻋﺎﻣﺎ ﻭﻫﻮ ﻓﻲ ﻗﻮﻣﻪ ﻳﺪﻋﻮﻫﻢ، ﻭﺳﺒﻌﻤﺎﺋﺔ ﻋﺎﻡ ﺑﻌﺪ ﻣﺎ ﻧﺰﻝ ﻣﻦ ﺍﻟﺴﻔﻴﻨﺔ.

– ﺍﻟﻜﺎﻓﻲ : 8 / 284 ، ﻟﻠﺸﻴﺦ ﺍﻟﻜُﻠﻴﻨﻲ، ﺍﻟﻤُﻠَﻘَّﺐ ﺑﺜﻘﺔ ﺍﻹﺳﻼﻡ، ﺍﻟﻤﺘﻮﻓﻰ ﺳﻨﺔ : 329 ﻫﺠﺮﻳﺔ، ﻃﺒﻌﺔ ﺩﺍﺭ ﺍﻟﻜﺘﺐ ﺍﻹﺳﻼﻣﻴﺔ، ﺳﻨﺔ : 1365 ﻫﺠﺮﻳﺔ / ﺷﻤﺴﻴﺔ ، ﻃﻬﺮﺍﻥ / ﺇﻳﺮﺍﻥ.

– ﻛﻤﺎﻝ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻭﺗﻤﺎﻡ ﺍﻟﻨﻌﻤﺔ ‏: 46 : ﺑﺎﺏ ‏ﻣﺎ ﺟﺎﺀ ﻓﻲ ﺍﻟﺘﻌﻤﻴﺮ.

2. Annabi Adam(as); ya rayu shekaru 1000 a Duniya:

3519 حَدَّثَنَا رَوْحٌ، حَدَّثَنَا حَمَّادٌ، عَنْ عَلِيِّ بْنِ زَيْدٍ، عَنْ يُوسُفَ بْنِ مِهْرَانَ، عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ، قَالَ: لَمَّا نَزَلَتْ آيَةُ الدَّيْنِ، قَالَ : قَالَ رَسُولُ اللَّهِ(صَ): “…فَكَانَ عُمْرُ آدَمَ أَلْفَ عَامٍ…”

– مسند أحمد : مسند بني هاشم | مسند عبد الله بن العباس : 2270, 2713.

– سنن الترمذي : أبواب تفسير القرآن عن رسول الله(ص) | باب : ومن سورة الأعراف : 3078, 3368.

– ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺣﻤﺪ ﻭﺍﻟﻠﻔﻆ ﻟﻪ ﻋﻦ ﺍﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ ﻭﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ، ﻭﺻﺤﺤﻪ ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ. ﻭﺭﻭﺍﻩ ﺍﺑﻦ ﺧﺰﻳﻤﺔ ﻭﺍﺑﻦ ﺣﺒﺎﻥ ﻭﺍﻟﺤﺎﻛﻢ، ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﺤﺎﻛﻢ: ﺻﺤﻴﺢ ﻋﻠﻰ ﺷﺮﻁ ﻣﺴﻠﻢ. ﻭﻭﺍﻓﻘﻪ ﺍﻟﺬﻫﺒﻲ.

3. Annabi Idris(as) ya rayu shekaru 965, kuma har yanzu yana raye, yayi gaiba ne ta hanyar dauka shi zuwaga bagire madaukaki:

ﻭَﺍﺫْﻛُﺮْ ﻓِﻲ ﺍﻟْﻜِﺘَﺎﺏِ ﺇِﺩْﺭِﻳﺲَ ﺇِﻧَّﻪُ ﻛَﺎﻥَ ﺻِﺪِّﻳﻘًﺎ ﻧَﺒِﻴًّﺎ ﻭَﺭَﻓَﻌْﻨَﺎﻩُ ﻣَﻜَﺎﻧًﺎ ﻋَﻠِﻴًّﺎ. (ﻣﺮﻳﻢ : 56 ـ 57).

ﻭﻗﺪ ﻛﺎﻧﺖ ﻣﺪﺓ ﺇﻗﺎﻣﺔ ﺇﺩﺭﻳﺲ ﻓﻲ ﺍﻷﺭﺽ ﻣﺎﻳﻘﺎﺭﺏ ﺍﻝ 800 ﺳﻨﺔ ﺛﻢ ﺭﻓﻌﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﺇﻟﻴﻪ ﻛﻤﺎ ﺫﻛﺮ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ.

ﻭﻗﻮﻝ ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﻧﺠﻴﺢ ﻋﻦ ﻣﺠﺎﻫﺪ ﻓﻲ ﻗﻮﻟﻪ: ﻭَﺭَﻓَﻌْﻨَﺎﻩُ ﻣَﻜَﺎﻧًﺎ ﻋَﻠِﻴًّﺎ ﻗﺎﻝ: ﺇﺩﺭﻳﺲ ﺭﻓﻊ ﻭﻟﻢ ﻳﻤﺖ ﻛﻤﺎ ﺭﻓﻊ ﻋﻴﺴﻰ. ﺇﻥ ﺃﺭﺍﺩ ﺃﻧﻪ ﻟﻢ ﻳﻤﺖ ﺇﻟﻰ ﺍﻵﻥ.

4. Annabi Hudu(as) ya rayu shekaru 962 (ko yake akwai sabanin masana akai).

5. Annabi Isa(as) yana raye har yanzu; shekarunsa a yanzu sama da 2018. Allah ya tabbatar mana bai mutu ba, yayi gaiba ne ta hanyar daukaka shi zuwaga (al’amarin) Allah:

ﻭَﻗَﻮْﻟِﻬِﻢْ ﺇِﻧَّﺎ ﻗَﺘَﻠْﻨَﺎ ﺍﻟْﻤَﺴِﻴﺢَ ﻋِﻴﺴَﻰ ﺍﺑْﻦَ ﻣَﺮْﻳَﻢَ ﺭَﺳُﻮﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻭَﻣَﺎ ﻗَﺘَﻠُﻮﻩُ ﻭَﻣَﺎ ﺻَﻠَﺒُﻮﻩُ ﻭَﻟَﻜِﻦْ ﺷُﺒِّﻪَ ﻟَﻬُﻢْ ﻭَﺇِﻥَّ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺍﺧْﺘَﻠَﻔُﻮﺍ ﻓِﻴﻪِ ﻟَﻔِﻲ ﺷَﻚٍّ ﻣِﻨْﻪُ ﻣَﺎ ﻟَﻬُﻢْ ﺑِﻪِ ﻣِﻦْ ﻋِﻠْﻢٍ ﺇِﻟَّﺎ ﺍﺗِّﺒَﺎﻉَ ﺍﻟﻈَّﻦِّ ﻭَﻣَﺎ ﻗَﺘَﻠُﻮﻩُ ﻳَﻘِﻴﻨًﺎ ‏(157) ﺑَﻞْ ﺭَﻓَﻌَﻪُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺇِﻟَﻴْﻪِ ﻭَﻛَﺎﻥَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﺰِﻳﺰًﺍ ﺣَﻜِﻴﻤًﺎ ‏(158)(ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ : 158-157).

6. Khidir(as); Malaman mafi yawansu, sun tabbatar da yana raye, kuma tun zamanin Annabi Musa(as) ya ke raye; sama da shekaru 3000. Shine malamin Annabi Musa(as) da nassin Qur’ani:

وَإِذۡ قَالَ مُوسَىٰ لِفَتَىٰهُ لَآ أَبۡرَحُ حَتَّىٰٓ أَبۡلُغَ مَجۡمَعَ ٱلۡبَحۡرَيۡنِ أَوۡ أَمۡضِيَ حُقُبٗا… فَوَجَدَا عَبۡدٗا مِّنۡ عِبَادِنَآ ءَاتَيۡنَٰهُ رَحۡمَةٗ مِّنۡ عِندِنَا وَعَلَّمۡنَٰهُ مِن لَّدُنَّا عِلۡمٗا

(Al-Kahf : 65).

7. As-habul-Kahfi; wanda suka yi gaiba cikin kogo sama da shekaru 309, sannan daga baya suka bayyana:

أَمۡ حَسِبۡتَ أَنَّ أَصۡحَٰبَ ٱلۡكَهۡفِ وَٱلرَّقِيمِ كَانُواْ مِنۡ ءَايَٰتِنَا عَجَبًا… وَلَبِثُواْ فِي كَهۡفِهِمۡ ثَلَٰثَ مِاْئَةٖ سِنِينَ وَٱزۡدَادُواْ تِسۡعٗا.

A takaice dai, tsawon rai na Imam Al-Mahdi(as) ba wani bakon abu ba ne a tarihin dan adam. Kuma ko dama ba hujjar wasu da suka yi tsawon rayuwa kamar tasa, wato a ce gabaninsa ba a samu wani dan adam da ya yi tsawon rai haka ba, to hujjar cewa Allah(t) mai iko ne a kan komai ya wadatar. Ko Allah bai da karfin raya Imam Al-Mahdi(as) shekaru masu yawan gaske?

ALLAH(T) YA GAUGAUTA BAYYANARSA! YA SA MUNA CIKIN MABIYANSA!! YA BIYA MANA BUKATUNMU; AL-BARKACINSA(AS)!!!

➖➖➖➖➖➖➖➖

Abdulrahman Murtala – abdulrahmanyj@gmail.com

🌹🌈🌹🌈🌹🌈🌹🌈

Post a Comment

Previous Post Next Post