Offline

IDAN BINDIGA NA MAGANIN MATSALA SU HARBE MATSALOLIN DA KE DAMUNSU!

Dama mun gargade su kan cewa kuna da nufin za ku (dira mana), amma in kuka yi fa za ku tambatsa abin ne. Su suna ganin kawai su bindiga za su ta iya musu komai ne. To ai kaga yanzu gashi kusan suna fama da matsaloli. 

Sun yi amfani a kanmu da bindiga da buldoza. Yanzu gashi suna ta fama da matsaloli, Madugunsu yana fama da ciwo. To tunda bindiga tana magani, to a harbe ciwo mana a huta, tunda yana da bindiga ko? Wadannan matsalolin kawai a saka bindiga fafafa a harbe, sai a ce an harbe cututtukan da suke damun shugaban kasa. Kuma na ji an ce har kunnensa na ciwo. Kawai ya kira Buratai yace harbi nan mana. Kawai sai ya harbe masa ciwon duk sai a huta. Ba sai kawai ya warke ba? 

Shi kuma wancan mai rushe-rushen gine-ginen nan (mai rusau), tunda shima yana fama da matsaloli, to a saka buldoza mana, a rushe matsalolin duk a huta, tunda Buldoza take aiki! 

Kisa da rushe rushe ba zai taba kawar da mu ba har abada. Sai dai ma ya kafa mu daram! Shi Mutum shine ‘Ahamm’, tunda akwai mutanen kuma ba su isa su ce za su kawar da mu ba. Mutane halittar Allah ne, baka da iko da su baka da iko da zukatansu, illa iyaka ka yin aka abin da za ka yi ka wuce. 

*DARASI DAGA KISSAR MUSA (AS) DA FIR’AUNA:*

Kamar yadda kakanninsu suka yi. Fir’auna mene ne bai yi ba? Ya zo ya wuce ya zama tarihi. Yanzu sai dai kawai a yi ta la’antar Fir’auna, kuma ba wani wanda zai karanta tarihin Fir’auna ya dauke shi a matsayin gwarzo. Yanzu da za a ce wani mutum ma jikan Fir’auna ne zai ce shi bai yard aba. Yanzu da ake yayin DNA, da za a yi DNA ace ah, kai jikan Fir’auna ne. Zai ce amma kuwa bai ji dadi ba. Da so samu ne ya zama dai shi ba jikan Fir’aunan bane. Zai nisanta kansa da Fir’auna.

Kamar yadda Allah Ta’ala a Alkur’ani a wurare daban-daban ya ba da misalin Annabi Musa, akwai abubuwa da dama a kissar Annabi Musa (AS) tsakaninsu da Fir’auna. Ta kowane babi za ka kawo, akwai babin dauriya, za ka ga an kawo su. Akwai babin halakar azzalumai, azzalumai ba su taba kyakkawar karshe ba, kullum karshensu mummuna ne. Akwai batun cewa in Allah ya yi alkawarin tabbatar addini daram sai ya tabbata. Gasu nan dai darussa ne daban-daban. Kullum sai ka ga ana ta kawo wannan kissa din na Musa da Fir’auna, saboda akwai darussa masu yawa a ciki.

To, duk wadannan misalsalai ne wanda yake in mutum yana da hankali zai iya ganewa. Amma ala ayyi halin, ina fada muku, su dai wadannan sun yi mafarkinsu, kuma dai har yanzu na san ba dai sun dena mafarkin bane, sai dais u canza wani sabon salo, tunda yake bindiga bata yi ba.

*SUN CANZA SALON KASHE-KASHE:*

Ai ma muna tsare ma sun yi dan yi wadansu shirye-shirye daban-daban. Sun yi abin da suka ce, tunda sun yi kisan kowa da kowa bai yi ba, to yanzu su yi kisan zabe, ‘targeted killing’ suke cewa. A zabi a kashe wane ne, a kashe wane da wane, maimakon a je a kashe kowa. Don wancan sun kashe maza da mata da jarirai, da mata masu ciki, har wata ma an harbe ta da bindiga ta haihu nan take, aka nike ta da jaririn da ta haifa. Duk an yi wadannan abubuwan. 

To, yanzu sun yi kisan jamma’i sun ga bukata bata biya ba, to yanzu a kashe wane da wane da wane, ta haka ne aka kashe Malam Kasimu. To shima kun ga jana’izarsa sai gashi an zo har daga Camaru da Chadi, da Niger, wanda ya ba da sallar ma daga Niger ya zo, sannan kuma wasu har daga Mali suka zo. Har ma mutanen garin suka rika cewa kai-kai, a garin nan ba a taba yin jana’iza mai yawan mutane irin wannan ba. 

Bayan sun yi wannan sai suka ga to sai me ya canza? Tambaya, sai me ya canza a garin Sokoto, misali? Sai aka fasa abin da ake yi? Abin ma ya tambatsa ne, ya cigaba. Kuma sun mai da shi Malam Qasimu babban gwarzo. To haka nan al’amarin yake Sai su ga wanda suka kashe daga cikinmu, sai su maishe da shi Gwarzo. A cikinsu kuma wanda ya mutu sai ka zama shikenan. 

Kamar shi wanda ya zama Kwamanda a nan Zaria a lokacin, shine ya wuce a mota aka yi Drama, suka ce wai Buratai ya zo ya wuce an tare masa hanya, drama suka yi, shi Buratan bai zo ba. Wani an ace masa Janaral Yusha’u shine ‘Director of operation Army Headquater, Abuja’, shine wato Daraktan duk hare-hare da ake kaiwa da sauransu, shi ke tsattsarawa. To shine ya yi wannan duk barnar da aka yi a Zariya, shi ya ‘commanding’, maigidansa kuma yana bashi umurni. Shi wannan Zanqalelen Qanjamammen yana bashi umurni daga can.

*WANNAN ZANKALELEN QANJAMAMMEN BA BAFULATANI BANE:*

Wannan ya tunatar da ni, kun san wannan Zanqalelen Qanjamammen suna cewa wai Bafullatani ne? Ba fa Bafullatani bane, Ba’are ne. Da yawa sun ace mashi Bafullatani, karya ne, ba Bafullatani bane. Shi Fulatanci duk da yake ban iya Fulatanci ba, amma na san iyayena da kakannina Fulani ne, saboda a jini ne. Shi kuwa ya fada mana waye ubansa, waye uban ubansa? Ba’are ne.

Kun san Arawa? A kan gansu sai a dauka su Fulani ne. In dai kana son Fulani kana iya cewa kana son Fulani, amma ba sai ka ce kai ma ka zama Bafullatani ba. Amma (shi) ba Bafullatani bane, Ba’are ne daga Nijer. Kun san Arawan nan duk daga Nijer suke, to daga can ya fito, shikenan sai yana ta makawa kansa Bafullatani. 

Muna magana da wani a waya ma yake cewa wai shi har kunyar a ce shi Bafullatani ne. Nace Subhanallahi. Wai saboda abin da wannan mutumin ya yi. Nace ai ko da dagaske ne Bafullatani ne, ai idan wani Bafulatani ya yi abin tsiya ba Fulani ne duk suka yi abin tsiyan ba. To, ballantana shi ma ba Bafulatanin bane.

*WASU DAGA WADANDA SUKA KASHE MU SUN GA JAZA’I:*

Ina maganar Yusha’u ne, Janar Yusha’u, shi Janar Yusha’u nace shi ya yi ‘commanding’ a Zariya, shi kuma babban ‘commandar’ dinsu daga ‘remote’ yana 1 Div, a Kaduna. Shi ke fada masa akwai maza da mata da yara, yana ce masa duk a kashe su ne. Yana fada masa suna dada karuwa. Yace duk a kashe su ne nace. To, sai da aka ce masa an kona gidan kurmus, Zakzaky da matarsa da yayansa duk an kona su kurmus. Sannan ya numfasa ya koma Abuja. 

To, sai gashi shi wannan Janar Yusha’u din bayan waki’ar ba a fi wata uku ba, shi kuma sai aka ce shima ya kone kurmus. Sai suka ce hadarin mota ne. To shikenan, amma dai hadarin da walakin, inji Bahaushe ya kan ce wai ko goro a miya ne?

To, hadari ne aka yi, motar ta kone da shi Janaral a ciki, amma Driver lafiyarsa lau, dan rakiya ma lafiyarsa lau, akwai ‘convoy’ da ke tafe tare da shi gaba da baya, motoci uku a gaba, motoci uku a baya, da sojoji, ba abin da ya samu kowa. Shi kadai, direba lafiya lau, dan rakiyarsa lafiya lau, kowa lafiya lau, amma shi kadai ya kone kurmus. 

Koma mene ne dai, sun ce hadari ne, amma labari ya nuna cewa ba hadari bane, sojoji ne suka kona shi, yana da ransa kuma, bayan da suka cinnama motar wuta yak one kurmus.

Da damansu in sun mutu sai ka ji shiru. Haka ma wanda ya rika bugo waya yana cewa wai Kanal Yusuf, aka ce an neme shi an rasa, kwana uku an tsinci gawarsa shima. Duk ba a fi wata uku ba duk.

Haka ma wanda ya fito yana cewa na kashe Zakzaky, na kashe Zakzaky, har shi Janar din ya kode shi da mari, don shi Janar din yana da bindigarsa a gefe yana jiran ya ga Zakzaky ya harbe, sai ga wani ko igiya bashi da shi, ya zo yana cewa na kashe Zakzaky. Sai ya ji haushi ya kode shi da mari. 

Shima bai yi wata uku (a raye ba) ba, shi mai cewa na kashe Zakzaky din. Shi ya dauko tsanin karfe ya dora a kanmu yana ta tsalle yana dira. To, shima sai aka ce ciwo ya kama shi aka kawo shi National Hospital Abuja, ya yi jniya yam utu.

To gasu nan gasu nan dai, kuma in suka mutun ma sai ka ji tsit. Wane ya mutu ka ji ana wani zumudin tunawa da shi? Haka nan suke macewa a banza da hofi. Ka gani? Amma mu namu ka kashe ya zama gwarzo. Ko mutuwa ya yin a Allah da Annabi zai zama gwarzon, baka is aka hana shi gwarzontakarsa ba, saboda matsayi ne da Allah ya bayar, kai kuma baka so.

Matsayi ne Allah ya bayar kai kuma baka so haka ba, ka ga da wa kake yi kenan? Wanda Allah Ta’ala ya daukaka, sai wani yace bai kamata Allah ya daukakan ya kai haka ba, da wa yake yi? Da Allah. Kamar cewa yake Allah bai san inda ya kamata ya saka daukaka ba. Kamar abin da yake cewa kenan, ba da harshensa ba, da aikinsa. ‘Lisanil hal’, wato bai kamata ace haka ba. To shi kuma zai kawar. Sai ya yi duk abin da zai yi sai dai ya kambama abin. Shi kuma sai dai ya yi asara.

To, wannan sai ya zamana mun dai ga yadda al’amura suke gudana yanzu, yadda abubuwa suka kotse musu, ya zama yanzu da za a tambaye su ace to yanzu kun share wannan abin ya sharu? Za su ce eh? Ina!
JAWABIN SHAIKH ZAKZAKY (H) YAYIN ZIYARAR FULANI (2)
Za mu cigaba.
— Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H).
Www.cibiyarwallafa.org

Post a Comment

Previous Post Next Post