Offline

KISSAR SHAIKH ISA ARRUMANIY DA SAHIBUL ASR (AS)

Ka san akwai wasu kissoshi da na bayar a baya a rana mai kamar yau. Kila za ku tuna na tab aba da labarin Shaikh Isa Arrumana na Bahrain. Wasu za su tuna na tab aba da labarin a wata rana mai kamar ta yau. Ina iya maimaita muku kissar a gurguje.

Wani mutum ne ya zo fadar sarkin Bahrain da Ruman, a ciki akwai rubutu a jikin Ruman din, an rubuta Muhammadur Rasulullah, sai aka ce Wane Khalifatu Rasulallah, Wane Kaza, Wane Abdullah, aka rubuta sunayen halifofinsu Rashiduna guda hudu a jikin Ruman din. Sai gashi ya zo da shi fada. (Kun san shi Ruman bayansa yana da karfi, sai ka bara sai ka samu ‘ya’ya a ciki, yana da bawo mai karfin gaske (ba kamar Tufah ba da ake gatsawa a ci), shi a kan bare ne a ci ‘ya’yan). 

Ruman ya zo da fada da wannan rubutun, sai yace to gashi. Ina Shi’a masu cewa daga Annabi sai Ali, to ga gaskiya ta bayyana. Ga Kulafa’ur Rashiduna guda hudu a jikin Ruman. Ka ga wannan rubutu ne ‘dabi’iy’ gashi Ruman ya rubuta, a jikin Ruman an ga rubutu, ya ka gani Malam, ba kaga an kama dahir ba? (Dariya). 

To shikenan sai aka kira su Shi’a wanda yake ba suna da yawa bane a Bahrain a wancan lokacin. Sai aka ce to me za ku ce dangane da wannan? Ga gaskiya ta bayyana, Allah ya fito da sunayen wadannan mutane a jikin Ruman, alhali ku kuna cewa daga Annabi sai Ali, sai Hasan sai Husaini, sai ‘ya’yan Husaini su tara. To gashi sunan Halifofi ya bayyana. Me za ku ce?

Su Shi’a suka yi shiruu, sai suka ce to a bamu kwana uku mu san amsar da za mu bada. Aka ce to kuna da wannan. Su ka je suka hadu, suka ce tofa, wannan wata musiba ce ta kunno kai, kuma dai ba wanda zai magance mana wannan sai Sahibul Asr Waz Zaman (AS). Saboda suna da yakini akwai Sahibul Asr din.

To yanzu suna tunanin wane ne zai je ya nemi ganin Sahibul Asr Waz Zaman (AS) don warwarwar wannan al’amuran. Sai suka ce dole ne mu fidda daya daga cikinmu. Akwai wani hukunci da Imam Jafarus Sadik (AS) ya bayar (ba hukuncin zan kawo ba, don maganar zan kawo), tsakanin dabbo bi ne, in ana so a fitar da wata, sai a raba garken biyu sai zabi daya, sai a kara raba biyu a zabi daya, har sai ya koma biyu sannan sai a dauki daya. To ina tsammanin irin wannan suka yi. 

Suka ce to yadda za a yi mu dare biyu nan, aka ce to yanzu a fid da wannan rabin. Cikin wannan rabin kuma ku dare, kowanne ana addu’ar Allah ka fidda mana wanda ya kamata. Kuma wadannan ku sake darewa, har abin ya fada kan na karshe mutum daya, shine wannan mai suna Shaikh Isa. Suka ce to Shaikh Isa sai ka je ka yi tawassuli, ko ma samu amsa.

To shine sai ya tafi Hamada yana ta addu’o’I da salloli da kira’a da sauransu, dare na daya bai ga komai ba, na biyu bai ga komai ba, na uku ana gobe wa’adi zai cika kenan, sai ya ji murya amma bai ga mai magana ba. Yana cewa ya Isa, me yasa kuka zabi har kwana uku? Me yasa rannan baku ce rannan a baku lokaci ku zo ku kawo ba? Sai yace to ai mun rasa yadda za mu yi ne, muka ziyarceka.

Sai aka ce masa yanzu ku je gidan wannan mutumin da ya zo da Ruman din nan, a duba daki kaza, a duba akwai akwati kaza mai kama kaza, akwai asirin wannan abin a ciki, kuma hujja na cewa wannan abu ba gaskiya bane, shine idan an bare Ruman din hayaki zai fito. Ka san in ka bare Ruman za ka ga ‘ya’yan Ruman ne, sai aka ce in aka bare za a ga hayaki ne ya fito. To shikenan, yace hujjar cewa wannan karya ne, in an bare Ruman din za a ga hayaki ne ya fito. 

To, sai shi Shaikh Isa ya dawo wajen mutanensu. Suka ce mene ne? Yace duk ku biyo ni, sai suka bi shi duuu, sai fadar sarki, to mun zo. Wa’adin kwanaki uku ya cika gashi sun zo. Sai Shaikh Isa yace ina son a hada ni da wasu, mu je gidan wannan mutumin, akwai abin da za mu dauko. Sai mutumin yace shi bai yarda a je gidansa ba, sai sarki yace ah, ya za ka ce ba za a je ba, ba mun ce musu su kawo mana mafita ba? Sai ya hada shi da dogarai yace su je gidansa.

Aka je, Shaikh Isa yace a bude wannan dakin (don an yi masa misalin dakin), yace a bude wannan akwatin, aka bude sai aka ga wani kwasfa na karfe, a ciki ya zana wannan a birkice, ya rufe Ruman din tun yana karami ya girma a jiki, sai rubutun ya fito. Sai aka dauko wannan kusfan karfen aka zo da shi fada. 

Kasan in za ka yi rubutu, kasan Arabiyya daga dama zuwa hagu ne ko? In ka rubuta daga hagu zuwa dam aka manna, zai fito ta dama zuwa hagu ne. to shikenan ya kankara ya kankara, ya rufe Ruman din da wannan karfen, Ruman din ya girma a jikin karfen, sai rubutun ya yi bambaro a jiki. In ya yi mai guru ne ya fito sai ya shiga cikin Ruman din, in kuma rami ya yi sais hi Ruman din ya kutsa ciki.

To shikenan, sai aka zo da wannan kwasfan karfe da aka yi zanen, ga Ruman ga kuma inda ya girma. To, yace kuma hujja na cewa wannan abu karya ne, in an bude shi za a ga hayaki. Sai sarki yace a bare Ruman. Ana barewa fuw, sai hayaki ya fita. Sarki ya sha mamaki (shi Ahlus sunnah wal jama’a ne), yace daga yau na zama Shi’a. Kuma duk wanda yake son gaskiya, to yau ya zama Shi’a. Sai aka zama Shi’a da yawa. Asalin Bahrain su zama Shi’a kenan. 

Sai da British suka je suka canza, wannan gidan sarautan ai ba na asalin bane, Turawa sun je sun dauko ne daga Saudi Arabiyya suka zo suka dankara musu. Wannan Ali Khalifa din da yake barna din nan. Amma mafi yawan mutanen Bahrain Shi’a ne, asali kenan.

To, kaga wannan hujja ce ta cewa akwai ma’abocin zamani. Wannan na kawo muku misali ne, akwai misalsalai da yawan gaske. Wanda yake bani wannan labarin, yace ya ma je Bahrain din, ya je har kabarin Shaikh Isa Arrumaniy din. Ana ce masa Shaikh Isa Arrumani, saboda kissar wannan Ruman din. To, ya je kabarin Shaikh Isa Arrumaniy.

To, misalsalai irin wannan suna nuna mana batun Sahibul Asr Waz Zaman (AS) yana nan tare da mu, kuma yana ‘supervising’ abubuwa, yana kwakkwafawa, yana daidaitawa, wannan haka ne.
JAWABIN SHAIKH ZAKZAKY (H) YAYIN NISFU SHA’ABAN 1443/2022 (4)
Za mu cigaba.
— Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H).
www.cibiyarwallafa.org

Post a Comment

Previous Post Next Post