To, mu kan ce mun gamu da jarabawowi, na sha wannan maganar. Mun gamu da jarabawowi. Jarabawowi a kan hanya lazim ne, kuma wani abu ne da dama za a sa ran ya zo, har ma in bai zo ba ya kamata mu sakawa kanmu ayar tambayar anya kuwa a tafarkin muke? Tunda yake tafarkin wadanda ake jarabawa ne.
Allah Ta’ala ya jarabta magabata, kuma zai jaraba wadanda suka zo daga baya, wannan lazim ne. Saboda haka jarabawa dama abin da za a sa rai ne. To, amma jarabawowin nan ba za su kara mana komai ba sai ci gaba.
Sai dai kamar yadda mukan ce, mishkilar jarabawa ita ce ba kowa yake ci ba. Abin da muke jin tsoro kenan, kar wata rana a yi babu mu, mu fadi jarabawa. Muna fatan Allah Ta’ala ya sa mu hayyake, kar ya zama a zo a gama maki ace mu ba mu hayyake ba.
Ka ga na jaddada mana, ba ‘majal’ ne na yabo ba, ko na yabon kai ba, ko na cewa wane ne ya yi kaza wane ne ya yi kaza ba. ‘Majal’ ne na godiya ga Allah Ta’ala.
LOKACIN HAIHUWAR IMAM MAHDI (AJ) LOKACI NE NA FATA:
To wannan lokaci, lokacin haihuwar Sahibul Asr Waz Zaman (AS) lokaci ne na fata. Domin ya nuna mu ba muna zaune ne a lokacin da fata yak are ba. Wata magana da na yi ‘yar guntuwar magana, na ga har ‘yan jaridu sun daddauka, da Ingilishi, nace ba muna zaune a ‘Hopeless Time’ bane, ‘there is hope’. Yauwa, ba muna zaune ne a lokacin da babu fata ba.
Akwai wasu da suke cewa an fid da rai. Kun san kimanin shekaru 43 kidayar Shamsiyya, watan Jimadal Akhira, lokacin da muka yi wannan Muzaharar da muka saka mata suna ‘Musulunci Kawai’ a Zariya, April 1980. To mun tsaya akofar Fada, muka dan yi ‘slogans’ da jawabai. To sai bayan da muka tashi sai na ga wani dattijo ashe yana jinmu.
(Cikin mamaki) sai yace oh, to, an yi sake, tuntuni ya kamata a yi wannan abin, amma ba a yi ba, yanzu an yi nisa, wannan abu ba zai yiwu ba. Yace wannan ba zai yiwu ba, an yi sake. Wato yana tunanin cewa shi tun zuwan Bature ba a yi wannan ba, aka kyale Bature ya yi mulkinsa shekara da shekaru, yanzu a zo ace za a yi wannan, yace ba zai yiwu ba. Kamar nace masa dattijo ai zai yiwu. Na ji shi ne yana cewa ai an makara. Wato kamar ya fahimci abin da muke cewa, amma yana ganin an riga an makara.
Kuma a wancan lokacin ne ma, wani Malami yana magana a gidan rediyo, wai ya za a yi Bature ya kafa abu shekara 100 ka zo ka tumbuke rana daya. Nace ah! To wa ya ce masa za mu tumbuke rana daya ne? In zai dauki lokaci ba a gama tumbukewar ba, ba sai a fara ba?
Tun shekarun saba’inoni, ina samun Mujalloli da Hausa daga China, to sai aka sa ya yi wani jawabi wai “Wawan tsoho da ya rusa duwatsu.” Wani tsauni ne a gaban gidansa, sai aka ganshi yana kokarin ya fasa, katon dutse, yana ta dukan dutsen. Aka ce dattijo me kake yi? Yace ina son na kawar da wannan dutsen ne a kwashe shi. Aka ce haba tsoho, yanzu ya za ka yi ka kawar da wannan tsauni haka? Sai yace ni zan yi, nai ta ta yi, nai ta ta yi har zuwa karshen iya abin da nake iyawa, in na mutu sai dana ya cigaba, shima ya yi ta yi, in ya mutu sai jikana ya cigaba, shima in ya mutu sai dansa ya cigaba har sai an kawar.
To, ka san in aka dade ana saran dutse ana kwashewa ai za a dibi wani abu ko? Za a kawar da gwargwado, kila ba gaba daya yake nufi ba, yana son ne ya zama ya dan samu waje, yau da kullum ana yi in aka dade ana yi (sai a samu wajen).
To mu bamu ce rana daya ake sauyi ba. Wa ya ce muku rana daya ake sauyi? Ba rana daya ake sauyi ba. Ko juyin-juya halin Musulunci na Iran ba rana daya aka yi ba. Akwai wani littafi yana nan (na ga akwai shi a ‘net’ ma ko?) “Ten Decades of Ulama Struggle”, shekara 100 cur Malamai na gwagwarmaya kafin ‘revolution’ din Iran ya samu nasara. Lokacin da aka yi nasara shi Imam Khumaini shekararsa kamar 79 ne ko? To kun ga yana nufin kenan tun kafin a haife shi ne aka fara, Malamai suke fafatawa.
Ba mu ce maka rana daya za mu kawar ba. Kun san su makiya suna ganin kamar sha-yanzu-magani-yanzu ne, kowane makiyi sai cikinsa ya duri ruwa, wai yanzu ne za a yi a gama. To, bamu san lokacin da za a yi ba, amma namu mu tsaya mu yi namu aikin, saura na Allah ne.
To amma yadda muke ganin al’amura, na san suma suna lura da al’amuran, suna ganin cewa lallai lokacin da duk aka yi jarabawowin suna kara mana karfi ne. Kuma duk da basu da dadi, amma dai natijoji muke gani nasu. Kara al’amari suke yi ba baya muke ba, karuwa ake yi. Akwai fata kenan.
Har nake cewa, idan kuka lura mutanen nan da sun tabbatar da cewa wannan abin da muke yi ba zai taba yiwuwa ba har abada, da bai kamata su damu da mu ba. Ya kamata ka damu da mutumin da ya zo yace zai kwashe kogin Niger? Ya dauko bokiti yace ba kana kama kifi ne ba, sai na kwashe ruwan. Ya debo bokiti yana kwasa yana watsarwa. Me za ka yi? Yace, sai na kwarfe kogin nan, ka rasa kifin. Sai kace to ba da kokari. Ai bai kamata ka dauko sanda ku shiga fada ba, ballantana ma ka dauko bindiga kace kogin Neja yake so ya kwashe mana, wallahi ba za mu bari ba. Alhali ka san ba zai kwasu ba.
Dalilin da yasa suke fada din nan, ai sun san zai yiwu ne. Da sun san ba zai yiwu ba da sun ce mana mahaukata. Akalla na san su kan ta yin maganganu daban-daban, (kamar cewa) ana bamu kudi ne. Nace dama kun ce mu mahaukata ne da ma ya fi. Ka san kuma mahaukaci bai kamata ka daka ta tasa ba ko? In yana haukatakunsa, in dai ba ya dauko sanda yace zai bigeka bane. In kaga mahaukaci yana daga hannaye, kace wane me za ka yi? Yace zan tashi sama ne. To ya kamata ka damu? Sai kace sai ka dawo.
Muna ‘prison’ din Inugu, ana bamu labari, wani cikin ‘yan ‘prison’ ya dade a ‘prison’ din a tsare, sai ya hau kan rufi wai shi zai tashi sama. Yana ta cewa Haluluya! Haluluya! Sai shi mai tsaron kurkukun yace masa, Oya, yanzu dai kana nan a Kurkuku, in ka tashi zan rubuta rahoto cewa ka tashi sama. (Dariya), sai kuwa ya dinga zama nan, amma da ya gaji sai ya sauko. Yace illa iyaka ni na yi rahoto, nace daya daga ‘yan kurkukun ya tashi sama. To, ya san ba zai tashi ba. Shima da ya gama zamansa a saman rufi, da ya ji yunwa sai ya sauko. To, shikenan, ina nan ‘prison’ din 1983 gwamnan Anambara ya yafe masa.
To, shi wannan ba mahaukaci bane, kawai dai kurkukun ne ya ishe shi, yace kawai tashi sama zai yi, yana ta kiran Haluluya. Shi kuma yace masa in k agama tashinka shikenan. Me zai sa a damu don yace zai tashi sama? Ai bai kamata a damu ba ko? Kamar yadda yace to in ka tashi illa iyaka na ba da rahoton cewa daya daga yan kurkukun da aka ce na tsare ya tashi sama.
To, ya kamata idan abu ba zai yiwu ba sam-sam, to ya kamata su kyale mu ne su ce mu ba da kokari, in sun san ba zai yiwu ba. Amma da yake sun san zai yiwu, shi yasa ka ga duk wannan haukatakun.
To, mu mun san wannan lokaci lokacin Sahibul Asr Waz Zaman (AS) ne, alkawari ne na Allah. Akwai wani da yake tambayar Imam Jafarus Sadik (AS) yace masa, to idan kuma ‘Bada’, (an san akwai ‘Bada’ Allah Ta’ala yana iya canza abu in ya so). To, idan Bada ya auku, aka ce an fasa Imam Mahdi din nan fa? Sai shi Imam (AS) yace masa ai bayyanar Imam Mahdi (AS) alkawari ne, shi kuma Allah baya saba alkawari. Alkawari ya yi, Allah in ya yi alkawari ya kan saba? Alkawari ne na Allah.
Saboda haka mun tabbatar da cewa lallai ilallah wannan zamaninsa ne. Kuma dama Allah ya yi musu alkawarin yawaita bayan karanci, ‘Kasra ba’adal qilla’. Su Iyalan gidan Allah zai yawaita su, sannan magaya bayan gidan suma zai yawaita su. Wannan alkawari ne. Da can su ‘yan kadan ne ana ta tursasa su a bayan kasa, to wata rana Allah zai yawaita su, zai kuma yawaita magoya bayansu. To wannan muna ganin alamar lokaci ne, alamomin da muke gani kenan. Ana dada yawaita ne.
In mutum ya duba sai ya ce to wai yanzu, “Awalam yarau anna na’atiyl arda nanqusuha min adraafiha…” (Raad: 41). Ka san wasu suna cewa ana tsuke kasa ne. A’a, ana cira ne a hankali a hankali, yau da kullum ana karuwa, ka ga wa ke galaba kenan? Mai yawaita ko mai karanta? To, ka ga kana fada da abu amma yana dada karfi. Kana dada fada da shi yana dada karfi, kana dada fada da shi yana dada karfi, to ka ga me yake nufi kenan? Zai fi karfinka kenan.
MASU FADA DA ALLAH SUNA GANIN JAZA’I:
Ballantana kuma yadda Allah ke nuna mana, ka ga mutum ya fara adawa din, jaza’I ya fada masa. Ka gan shi yana fama, rayuwar bata yi masa dadi ba, gashi mayen tuwo, yana son ya ci, likita yace yanzu wannan abin za ka rika sha. Yace ai da daci, yace dole ka sha shi. Dole kuma ya sha mai dacin. Ace juya nan, a zurmuka masa allura. Yace da zafi. Ace ai haka allurar take.
Yana ta fama, duk ka gan shi kwalmadadde, a yi ta ‘penel beating’, in an gama a yi masa ‘stickchess’, a kwaba kuluma (ko forte), kalan launin jikin mutum a mammanna a gyara. Nan wuyar kullum sai an saka rigar sanyi ko ba a sanyi, ana rufe komodon makogoro babu kyan gani. Nan kuma (fuska) a ciccike a yi face-face, ka ga mutum ya fito duk da haka nan mummuna, ba ko kyan gani, idanu wasu iri, zuciyar babu rahama, shi bai ji dadin rayuwar ba, mafi yawan lokaci ma bai san ma inda yake ba. To wannan wane irin rayuwa ce?
Ka ga fada da Allah ba karamin aiki bane. ka yi kuma a banza. Ba wanda ya taba fada da Allah ya yi nasara. Ko Abu Jahal ya dauka shi ba yana fada da Allah bane, lokacin da yake fada da Annabi (S). Lokacin da za shi yakin Badar, wasu kabila suka aika masa da taimakon mayaka. Sai yace in dai mutane za mu yaka, bamu bukatar karin mutane don muna da yawa. Amma in Allah za mu yaka kamar yadda Muhammadu yake cewa, to ba wanda zai yaki Allah ya yi nasara.
Kun ga shi a wajensa yana yakar wani mutum ne da ya kira shi Muhammadu. To, amma Allah yake yaka. Ta hanyar da kake yakar Allah shine kana fada ne da masu kira izuwa ga hanyar Allah. Ai ana fada da bayin Allah ne. Ko da Allah Ta’ala yake cewa: “Fakad azantuhu bil harbi” din nan, ai ba wai Allah ne za ka ganshi da Mala’ikunsa a wannan bangaren, ga wannan kuma a nan bangaren ba. Ka san su haka suke tsammani, don haka su kan ce ma to ina Allah din yake?
Ka san sun yi mana izgili lokacin waki’ar nan, har wasu suna cewa to wai Allah din ya sauko ya kwace ku mana. Sun yi izgili iri-iri, suna harbin ‘yan uwa. ‘Yan uwa suna Allahu Akbar, su kuma suna dariya, suna cewa to ya sauko daga sama ya kwace ku mana. Da yake su a tunaninsu Allah din mutum ne, sai ma ya sakko. Kuma su kan ce to ina rundunarsa? Ina barikin sojan rundunar Allah din, ina sojojin nasa? Su basu gani ba. Su kan ce, to mu gamu da bindigogi, gamu da bataliyoyi, ga Janarorinmu da sauransu, za ku ce ku sai Allah, to ina yake?
To, amma kaga ai sun kara sun gani ko? Yauwa. Sun kara sun gani. Ta yiwu tarihi ya sajjala. To tarihi kamar yadda yake sajjala mana wanda suka yi na baya, suka tafi yanzu muna iya gani, haka ma mu nan nan gaba za a karanta tarihi a ga yadda ta kaya.
To, kar na tsawaita muku magana, za mu sha ruwa. Muna cewa, muna zamanin fata ne, kuma tabbas alamomin da muke gani, tana nuna al’amari na cigaba ne, kuma yana nufin kyakkyawan fata. Muna fatan Allah Ta’ala ya tabbatar da zukata da duga-duginmu, Ya kuma saka mu cikin ajin wadanda zai yi amfani da su wajen taimakawa Sahibul Asr Waz Zaman a Gaibarsa da kuma in ya bayyana, Insha Allahul Azeem.
Wasallallahu ala Muhammadin wa Alihid Dahireen.
JAWABIN SHAIKH ZAKZAKY (H) YAYIN NISFU SHA’ABAN 1443/2022 (7-Karshe)
MUN KAMMALA
— Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H)
Www.cibiyarwallafa.org
Tags
Jawaban Jagora