Offline

Ta’addanci Da Sunan Fulani, Makircin Makiya Ne.

 
Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

Ranar Lahadi, 17 ga Sha’aban, 1443 (20/03/2022) Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya karbi bakuncin wakilai daga kungiyar Fulani ta Harkar Musulunci mai suna “Kautal Ko’e Julbe” a gidansa da ke Abuja.

A cikin jawabinsa ga maziyartan, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi musu bita kan irin ta’addancin da sojojin Nijeriya suka yi a kansa da sauran ‘yan uwa a lokacin waki’ar Zariya ta 2015, inda ya nuna cewa: “Inda makiya suna da tunani wannan abin da suka yi (mana da nufin ganin bayanmu), za su ga cewa sun tambatsa al’amarin ne.” Ya kara da cewa: “Dama mun gargadesu kan cewa mun san kuna da nufin za ku dira mana, amma fa in kuka dira mana za ku tambatsa abin ne.”

Shaikh Zakzaky yace, su suna ganin bindiga zai iya musu komai ne, in har komai bindiga ke iya yi to ta harbe matsalolin da suke fama da ita a gwamnatinsu, ko ta harbe ciwon da ke damun shugaban kasar mana. Yace: “Kisa da rushe rushe ba zai taba kawar da mu ba har abada. Sai dai ma ya kafa mu daram!” Ya kara da cewa: “Da za a tambaye su ace to yanzu kun share wannan abin (Harkar Musulunci) ya sharu? Za su ce Ina!”

Da yake magana dangane da makircin makiya ga wannan kasar, Jagora (H) ya nuna yadda ya dade yake magana dangane da Boko Haram cewa ba wani abu bane illa shiri ne da aka shigo da shi da gangan na samar da wata fitina domin a dibi arziki. Amma sai mutane suka rika shakku har da wasu da ake tare da su.

Yace: “Ya za a yi banda in rainin wayau ace mana akwai wasu mutane wai sunansu Boko Haram, wai suna so su tabbatar da addinin Musulunci ne, wai suna yakar gwamnatin kasar nan ne, amma kullum basu da wajen hare-hare sai kasuwa. Mutane suna cin kasuwa su je su kashe mai saye da mai sayarwa. Sai kuma masallaci ana salla, sai coci, sai tashan mota, sai kuma su je su ta da gari (kauye).

“To don Allah mai fada da hukuma abin da zai yi kenan? Ba sai ya je can fadar gwamnati ya yi fada da su ba? Me ya hada shi da talaka a kasuwa? Amma don izgili ga addinin Musulunci sai aka tsaya tsayin daka aka ce wai wadannan masu kishin addinin Musulunci ne.”

Da yake magana dangane da halin da ake ciki, musamman kana bin da ake kira ‘Bandits’ ko Mahara a yanzu, Shaikh Zakzaky ya bayyana takaicinsa kan yadda ake ta kashe a’umma da sunan Mahara ba tare da wani bayyanannen dalilin akan hare-haren ba.

Yace: “Sai aka ce Mahari hari kawai yake yi, ba wani dalili, sai ya kai hari, kuma baya sata, in ya shiga gari sai ya harbe mutane ya cinnama gidajensu wuta, sai kuma ya kona rumbun abinci, inda suka tara hatsinsu na shekara, ya kokkona, ko kuma ya yamutsa dawa da gero da wake, ya yamutsa ya watsar. Kuma bashi da dalili illa (kawai shi Mahari ne) yana hari ne.”

Shaikh Zakzaky jaddada cewa: “Wannan ma wata manufa ce, akwai wani ‘clip’ da na yi, ya dan yi yawo, nake cewa abin da suke so shine za su share mutanen da ke wannan yanki na Zamfara su yi filayen jiragen sama su dibi zinare. Haka abin da suke yi tsakanin Zariya da Birnin Gwari.”

Har ila yau, Jagoran ya ba da labarin irin salon da aka rika bi da matakai daban-daban wajen kulla wannan makircin har aka kawo inda ake yanzu. “Bayan suna hare-hare irin wannan, sai suka bullo da Banga. ‘Yan banga din musamman ya zama sai suka fara farwa Fulani, Fulani suke kaiwa hari musamman.”

Yace: “Sai ya zama lokacin da muke tsare abin ya yi kamari, shekarar da aka tsaremu sai kawai aka tura sojoji zuwa yankin Zamfara, suka je suka dinga harbe Fulani, wai barayin shanu ne, sai ana kada shanun nasu, wai barayin shanu, kuma soja ke yi.” 

Yace: “Shi soja mene ne aikinsa don Allah? Yana harbe barawo ne? Shi soja abin da aka san shi shi yana aikin tsaron kasa ne, aikin tsare doka na dan sanda ne, sai idan dan sanda abin ya fi karfinsu, basu da yan sanda isassu, sai ya gayyaci soja ya zo a matsayin dan sanda ya taimaka masa.” Ya cigaba da cewa: “Amma wannan soja ne suka zo har da jar fata, suka je duk inda aka ga Bafullatani a dambara masa harsashi a kwashe shanunsa. Yana kora shanu a harbe shi, wai ana harbe barayin shanu. Kai da shanunka da ka gada iyaye da kakanni. An ce sun kashe mutum sama da 500 a haka”

Jagora ya kawo labarin zuwan ministan harkokin kasashen waje na Amurka, John Kerry a shekarar 2016, inda ya nemi mahukuntan kasar nan su canza salon yadda suke kulla wannan makircin da suke yi. “Aka sa maganarsa yana cewa wannan karon ya kamata ne mu yi amfani da mutanen gari, ‘community’ ya kira abin, da yake da Ingilishi yake magana, yace wannan zai kiyaye abin da ya kira ‘vulnerability’; Abin da yake nufi wannan zai kiyaye a gano cewa hukuma take yi. To, a lokacin sai aka fito da ‘Bandit’.”

Shaikh Zakzaky ya cigaba da cewa: “Yanzun ba soja bane kuma, soja ne amma mare ‘uniform’, makamai na soja, za ka ga bindigogi irin na soja, harbi irin yadda soja yake yi, amma wanda suke yi wai ba sojoji bane, wai sunansu Mahara. Me yasa suke kai hari? Wai saboda su Mahara ne. Da me suke hari? Da bindigogin Soja. Wa ya basu bindigogin sojan? Ba a sani ba. Kila sun fado daga sama ne, ko sun haka rami ne suka tsinto.”

Yace: “Ka san bindigar soja ba kowa zai iya harbawa ba, sai wanda aka masa ‘training’ (din harbin). To wa ya koya musu irin harbin soja din? (Wai) ba a sani ba. Su sunansu kawai Mahara. Ka san wannan ba zai yiwu ba ko? Wani shiri ne kawai.”

Ya cigaba da cewa: “Yalai kuwa bayan John Kerry ya tafi sai gashi an dena amfani da soja kai tsaye. Zamfara sai aka koma aka ce ‘Bandits’ (Mahara) ne. Muka ce oho! Abin da ya muku ishara din kenan!?”

Yace: “To bayan an ta far wa Fulani, sai kuma aka bullo da wani sabon salo, yanzu su kuma an yi Fulani masu mai da martani. Yanzu akwai masu satan mutane su yi garkuwa da su, suce a kawo miliyoyi. Kuma ba ka ji sun kama Dan Majalisa, ko Gwamna ko Dan Gwamna, ko Minister ko Dan Minister ba, a’a kawai talaka za a dauka a ce ya kawo miliyan. Bai da komai ace in bai kawo ba za a kashe mutum. 

“Ai ta fantsam-fantsam, wani lokaci a kai, kuma suna zaune lafiya lau a dazuzzuka. Kuma suna da bindigogi suma irin na sojoji, da an yi wannan sai a ce Fulani ne. Har ma yanzu wai sai ka ji an ce Fulani ‘Kidnappers’, wai ‘Kidnapping’ din Fulani ke yi. Har ma masu wasan kwaikwayo sai su yi ta yi wai Fulani ke ‘Kidnapping’. A kama mutum ai garkuwa da shi a ce ya kawo kudi, wai sana’ar Fulani ne.

“To, wannan dasisa ce, gaskiya shiri ne na mugunta aka yi mana. Lokacin da ake yanka Fulani da sunan ‘Yan Banga su ba a ce komai ba, amma yanzu ana ta iface-iface a ko ina wai Bafullatani ne matsala. To, kuma suma ‘yan kudu in ka ga irin maganganun da suke yi suma, ana nuna musu cewa Bafullatani shine babban hadari.” Inji Shaikh Zakzaky.

Ya kara da cewa: “Suna da shirin in sun kammala rigimar da ya kau da Bafullatani, za su koma kan wanda ba Bafullatanin ba, don kowa da kowa ne (suke hankoro). Yanzu kauyukan da manoma ke zaune, suma ana zuwa a kai musu hari ace Mahara ne, su ba a ce musu Fulani bane, an ce wannan Mahara ne. Su je su kona gidajensu da rumbunansu, babu noma kenan. Sannan a bi makiyaya suma a harbe su a kwashe dabbobin ba noma kenan ba kiwo.

“To, in ya zama ba noma ba kiwo, to su wadanda suka dogara da noma da kiwo me za su yi? Dole za su watse daga kauyuka su shiga gari, in sun shiga gari me za su yi? Ai sai bara. Saboda an kona maka gidanka da komai naka, baka da komai, kuma dama abin da ka sani kai manomi ne ko ka iya kiwo ne, kai ba ka iya kira ko wani abu bane, ko wani aiki aka baka za ka sha wahala ne kawai, don baka iya ba. In an ce ka yi gini baka iya gini ba. Ana neman a yamutsa rayuwar mutane ne. Kuma abin da ke faruwa kenan.”

Ya jaddada bayanin da ya yi a lokacin ziyarar Cibiyar Wallafa da Mawaka, kan yadda a kafafen sadarwa ya ga ana kokarin a haddasa rikicin fadan Fulani da Hausawa ta hanyar zage-zage da soke-soke. Yace: “Kun ga yanzu ana so a haddasa wani fadan, mai yiwuwa a samar da wasu ‘yan ta’adda da sunan Hausawa ne, ko kuma a fito da wasu ‘yan ta’adda da sunan su Fulani ne, sai a yi ta gwabzawa da sunan kashe-kashen juna.”

Yace: “Mun shiga jidali ba kadan ba, saboda makiyanmu sun yi nazari sun yi shiri mummuna a kanmu kuma suna aiwatarwa. Kuma akwai wawaye wadanda su kuma a shirye suke su yi musu aiki in dai za a basu wani abu. Shine matsalar da muke fuskanta.

“Shi yasa in muka ce wannan shiri ne na makiya daga kasar waje, sai su ce to wane ne yake yi? Kai ka ga Bature ne da idanunka ya zo yake yi? (Su kan ce) kashe-kashen nan duk ku iku kuke kashe-kashenku. Wannan ya kashe wannan wannan ya kashe wannan, amma da hannun Bature a ciki.” Ya tambaya cewa: “Wa ya taba tambayar daga ina bindigogin nan suke fitowa? Wa ya taba tambayar wane ne ya basu tirenin? Ka san shirin wasu ne. Kowa ya san cewa wannan shiri ne da aka mana.” Inji Jagoran.

A karshe, Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa: “Yanzu bamu da wani mafita illa mu koma ga Allah, mu yi ta addu’a, Allah Ta’ala ne kawai zai kwace mu."

@SZakzakyOffice
21/03/2022

Post a Comment

Previous Post Next Post