Offline

SALLAR DA AKEYI AKOWACE JUMA'A TA WATAN RAJAB.


Acikin littafin Ikbalul-a'amal ankawo wannan sallar daga manzon rahama (s) yace " wanda yayi sallah aranar juma'a atsakanin azahar da la'asar Raka'a 4, anakaranta fatiha 1, ayatul-kusiyyu 7, kulhuwallahu 5, sannan kace ASTAGFIRULLAHALLAZI LA'ILAHA ILLA HUWA, WA'AS ALUHUTTAUBA.,

FALALARTA.

Allah zai rubuta mashi kyawawa dubu akowace juma'a har yamutu, kowace aya daya karanta za'agina mashi birni a aljanna na jan yakutu, Allah zai aura mashi hurul-in, Allah zai yarda dashi, Allah zai cika mashi da sa'ada da gafara, kowace raka'a dayayi za'ayi mashi salati dubu, kuma zai zauna a aljanna tareda siddikai, kuma bazai bar duniya ba, har sai yaga mazauninshi a aljanna.

 [ Diya'ussalihin ].

*Daga Zauren: F-Fighters A'amal*

*Freedom Fighters Ng.*

www.freedomfightersng.com

Post a Comment

Previous Post Next Post