Kadan Daga Cikin Ladan Azumi a Wannan Wata.
Shaikh Al-Sadooq (r.a) daga isnadinsa ya ruwaito Abu-Sa'eed Al-Khudri (r.a) yana cewa Manzon Allah (s.a.w.a) cewa:
Duk wanda ya azumci rana guda na rajab, ya rufe wa kansa kofa guda ta wuta.
Duk wanda ya yi azumi na kwana uku cikin rajab, Allah Zai halicci wani shamaki tsakaninsa da wutan Jahannama, wanda fadinsa ya kai (tafiyar) shekaru saba'in.
Duk wanda ya yi azumi na kwanaki bakwai cikin Watan Rajab-Allah zai rufe kofa guda daga cikin kofofi bakwai na wutan Jahanna na kowace ranar azumin. Duk wanda kuma ya azumci kwanaki takwas na rajab, Allah zai bude kofa guda cikin kofofi takwas na Aljanna da kowace rana guda na azumin
Duk wanda ya yi azumi na kwanaki 14 cikinrajab, Allah Zai ba shi ladan, a fadojin da aka yi su da lu'u-lu'u da abubuwan kyalkyali, da idanuwa ba su taba gani ba, kuma kunnuwa ba su taba ji ba haka nan kuma zukata ba su taba tunaninsu ba.
Duk wanda ya yi azumin kwanaki 16 cikin rajab zai kasance daga cikin na farko da za su hau wata dabba ta aljanna mai haske da zata zagaya daga Aljanna zuwa ga Gidan Rahama
Duk wanda ya yi azumin kwanaki 18 cikin rajab, zai kasance tare da Annabi Ibrahim (a.s) a fadarsa; fadar da aka yi ta da abubuwan kyalkyali.
Duk wanda ya yi azumi na kwanaki 19 cikin rajab, Allah Zai gina masa gida (fada) da aka yi shi da abubuwan kyalkyali yana duban fadar Annabi Adamu da Annabi Ibrahim (a.s)a Aljanna. Daga nan zai gaisar da wadannan Annabawa kana su kuma su mayar masa da gaisuwar suna masu jaddada cancantansa.
Duk wanda ya yi azumin kwanaki 30 cikin rajab, Wani mai kira a Aljanna zai yi kira ya ce: 'Ya kai bawan Allah! an gafarta maka abubuwan da ka aikata, don haka ka fara aiki don makomarka'. Sai aka tambayi Manzon Allah (s): 'To idan kuma mutum bai samu daman yin azumin ba saboda rashin lafiya, tsufa ko kuma jinin haila?'
Sai Manzon Allah (s) ya amsa da cewa: 'To sai ya/ta ba da sadaka ko da kuwa na guntun biredi ne a kowace rana. Na rantse da Wanda raina ke hannunSa idan har suka bayar da wannan (sadaka) to ladarsu za ta kasance daidai.' Sai wani mutum ya sake tambaya: 'To idan mutum kuma ba zai iya ba da wannan sadaka ba fa? Sai Manzo (s) ya ce masa: 'To sai ya karanta wannan tasbihin sau 100 kowace rana: Subhanal Elahil Jalil, Subhana Man Layanbaghil Tasbeeh Ella Lah, Sobhanal A'azil Akram, Subhana Man Labesal Izza Wa Huwa Lahu Ahl.
Biharul-Anwaar; Juzu'i na8, Shafi na 170.
Rubutawa; Muhammad Auwal Bauchi.
Tags
A'amal