Offline

Imam Khamenei ya yafewa fursunonin Iran fiye da 3,300 a bikin zagayowar ranar juyin juya halin Musulunci na Kasar


Jagoran juyin juya halin Musulunci mai girma Imam Sayyed Ali Khamenei ya amince da shawarar yin afuwa ga fursunonin Iran 3,388 a daidai lokacin da ake cika shekaru 43 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci.

A ranar Alhamis ne Imam Khamenei ya amince da yin afuwa ko sassauta hukunce-hukuncen da aka yanke wa wadanda aka yankewa Iraniyawa bisa shawarar babban jami'in shari'a Gholam Hossein Mohseni Ejei wanda ya bukaci shugaban ya yi wa fursunonin.

An yi afuwar ne domin girmama cika shekaru 43 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci wanda ya kifar da daular Pahvali a ranar 11 ga Fabrairun 1979.

Mataki na 110 na Kundin Tsarin Mulki ya baiwa shugaba damar yafewa ko rage hukunce-hukuncen masu laifi bisa shawarar da shugaban sashen shari'a ya bayar.

Post a Comment

Previous Post Next Post