Sa'id Haruna
13-02-2022
Jahar Katsina hare haren ƴan bindiga na gab da share ƙauyukan Dutsin-ma da Safana dake jahar Katsina suna fara kai hare harenne a kullum tundaga safe har zuwa yamma suna kashe mutane suna ƙona ƙauyuka bawani Soja ko dan sanda da yake takamasu burki wallahi kauyukan da suka share babu kowa acikin su Allah ne kadai yasan iyakarsu.
Mutanen ƙauyukan sunata kwararowa garuruwan Dutsin-ma da Safana dan kama gidan haya sabida babu wani san,sanin gudun hijira da Gwamnati ta yi dan tai makonsu da yawa basu da kudin kama haya sai dai suyita bara a gari suna kwana a waje duk da matsanan cin sanyin da akeyi.
Yanzu hakadai mutanen Unguwar wake sun fashe sau ra yan kaɗan da bayadda zasuyi mutanen Jantsauni sun fashe mutanen zabuwa sun fashe mutanen tashar Wada sun fashe mutanen Kunkunna sun fashe mutanen Unguwar Aisha sauran kaɗan mutanen Salihawa sauran kaɗan mutanen Karfa sun fashe mutanen mai Jaura sun fashe mutanen Nassarawa sun fashe mutanen mai Kada Sunfashe.
Da sauran ƙauyukan da lokaci bazai bari in lissafasuba duk garuruwa da kukaji na lissafa a baya in kaga mutum a zaune to ba yadda yaiyane bashi da halin komawa gari amman mafi yawan ƙauyukan ba kowa a cikinsu sun zama kango.
Yaa Allah ka tarwatsa wannan Azzalimar Gwamnatin ta Criminal Buhari databari anata kashe Al'ummar Arewa bayan tagama Kisan Al-majiran Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) sama da 1000 a Zariya.
Tags
News