Wasu majiyoyi sun tabbatar wa al-Ahed News cewa mahukuntan Saudiyya na neman tabbatar da zarge-zargen rashin adalci kan wasu matasa 11 daga garin Umm al-Hamam da ke lardin Qatif na Gabashin kamar mai mabiya mazhabar Shi'a.
A cewar majiyar, babban mai gabatar da kara na neman a yankewa Ali al-Alawi hukuncin kisa, tare da daure wasu wadanda aka bayyana kamar haka.
Faisal al-Kuaibi
Ahmed al-Kuaibi
-Ali al-Kuaibi
-Mohammed al-Kuwai
-Ali al-Awami
-Mohammed al-Shebib
-Jaafar al-Marhoun
-Mortadha al-Marhoun
-Mujtaba al-Marhoun
-Ali al-Marhoun
Tun bayan da Mohammed bin Salman ya zama shugaban Saudiyya na a shekarar 2017, masarautar ta kara daukar matakan kame masu fafutuka, masu rubuta ra’ayinsu a yanar gizo, masana, da sauran wadanda ake kyautata zaton ‘yan adawa ne na siyasa.
An kashe malaman musulmi, an saka masu fafutukar kare hakkin mata a gidan kurkuku da azabtar da su, kuma ana ci gaba da hana 'yancin fadin albarkacin baki, da kuma Hana mutane bayyana akidojinsu dasukayi imani dasu.
Source; Al'ahed News English
Tags
News