Wani sabon rahoto ya bayyana cewa an kashe 'yan jarida da ma'aikatan kafafen yada labarai fiye da kowane lokaci a yankin Gaza tun daga watan Oktoba na shekarar 2023, lokacin da "Isra'ila" ta fara farmakin ta na kashe-kashe a yankin. Adadin ya zarce yawan 'yan jarida da aka kashe a Yakin Duniya na Farko da na Biyu, da sauran manyan rikice-rikice a tarihin duniya.
A cikin cikakken bincikensa mai taken News Graveyards: How Dangers to War Reporters Endanger the World, wanda aka wallafa a ranar Talata ta hannun cibiyar Watson Institute for International and Public Affairs ta Jami’ar Brown, dan jaridar bincike na Amurka, Nick Turse, ya bayyana cewa an kashe 'yan jarida 232 a Gaza har zuwa ranar 26 ga Maris.
Wannan adadi mai ban mamaki, wanda ke nufin kusan mutum 13 a kowane wata, ya zarce jimillar 'yan jarida da aka kashe a Yakin Basasar Amurka, Yakin Duniya na Farko da na Biyu, Yaƙin Koriya, Yaƙin Vietnam (da rikice-rikicen da suka shafi Kambodiya da Laos), Yaƙin Yugoslavia na shekarun 1990 da 2000, da kuma Yaƙin Afghanistan, a cewar rahoton.
Rahoton ya jaddada cewa 'yan jarida na cikin gida ne suka fi shan wahala, domin raguwar 'yan jarida 'yan kasashen yamma ya sa kafafen yada labarai na duniya sun fi dogaro da 'yan jarida na gida, wadanda galibi ba su da wadatattun kayan aiki ko kariya.
A cewar binciken: "Yawancin 'yan jarida da ake cutarwa ko kashewa, kamar yadda ke faruwa a Gaza, 'yan jarida na gida ne. Duniya na kara dogaro da wadannan 'yan jarida da ba su da wadatattun albashi ko kayan aiki, domin yin aiki a wuraren da ke da hadari yayin da yawan 'yan jarida 'yan kasashen yamma ke raguwa."
Turse ya bayyana a cikin rahoton cewa hana 'yan jarida na kasashen waje shiga Gaza da kuma kashe 'yan jarida Falasdinawa yana hana duniya samun sahihan labarai daga yankin.
Ya kara da cewa hakan yana da matukar hadari, musamman ganin cewa Amurka ta amince da bayar da tallafin kudi na kusan dala biliyan 18 ga Isra’ila domin ci gaba da kai hare-haren ta a Gaza da sauran wurare tun bayan watan Oktoba 2023.
A cikin watan farko na yakin Gaza a shekarar 2023, an kashe 'yan jarida 37, wanda hakan ya sanya shi mafi muni a tarihin kungiyar Committee to Protect Journalists (CPJ) tun bayan fara tattara bayanai a 1992.
A cewar Palestinian Journalists Syndicate, an jikkata kusan 'yan jarida 380 a Gaza daga watan Janairu na wannan shekarar.
Turse ya bayyana cewa ba a san adadin 'yan jarida da aka kashe da gangan ba, da kuma wadanda suka mutu a matsayin fararen hula ba, sakamakon ruwan bama-bamai da Isra'ila ke yi a wannan yanki mai fadin mil 140 kacal.
Rahoton ya kara da cewa a kalla sau 35 tun daga Oktoba 2023, akwai hujjojin da ke nuna cewa Isra’ila ta kashe 'yan jarida kai tsaye saboda aikinsu, a cewar kungiyar Reporters Without Borders (RSF).
A jiya ne gidan rediyon Al-Aqsa ya bayyana cewa an kashe dan jarida Mohammed al-Bardaweel tare da iyalansa sakamakon harin da Isra'ila ta kai a gidansu da ke Khan Younis.
A cikin wata sanarwa, gidan rediyon ya ce: "Sojojin mamaya na Isra’ila suna kokarin murkushe muryar Falasdinawa da boye gaskiya ta hanyar kai hare-hare kan 'yan jarida."
Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya yi tir da kisan al-Bardaweel da iyalansa, inda suka bukaci kungiyoyin yada labarai na duniya da su yi tir da wannan zalunci kuma su dauki matakin shari’a a gaban kotunan kasa da kasa.
Kashe al-Bardaweel ya kara yawan 'yan jarida Falasdinawa da aka kashe a yakin Gaza tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023 zuwa mutum 209, a cewar ofishin yada labarai na Gaza.
Ana ci gaba da yin kira ga kasashen duniya da kungiyoyin yada labarai na kasa da kasa da su dauki mataki don kare 'yan jarida a Gaza, da tabbatar da cewa ana watsa labaran da suka dace ba tare da tauye gaskiya ba. Wannan rikici yana ci gaba da haddasa hasarar rayuka da lalata kafafen yada labarai, wanda ke hana duniya samun sahihan bayanai daga yankin.
