Rahotanni daga Al Mayadeen sun tabbatar da cewa Isra’ila ta kashe Falasdinawa akalla 64 cikin awanni 24 da suka gabata yayin da hare-haren mamaya ke kara tsananta a Zirin Gaza.
Isra’ila ta kara kaimi a harin bama-bamai da hari ta sama da bindigogi a wasu yankunan Gaza:
A Arewa: An yi ruwan bama-bamai a Beit Lahia, tare da kai hare-haren sama a unguwar al-Tuffah da ke gabashin birnin Gaza da kuma yammacin Al-Karama Towers.
A Tsakiya: An kai hari ta sama a Al-Bassa da ke yammacin Deir al-Balah da Camp 1 da ke al-Nuseirat.
A Kudu:
Jirgin yaki mara matuki na Isra’ila ya hallaka Falasdinawa biyu da ke cikin mota a Rafah.
Tankunan yakin Isra’ila da ‘yan harbi-mai-kwantar da kai sun kai hari a Abasan al-Kabira da ke gabashin Khan Younis.
Isra’ila ta kashe mutane hudu a wani hari kan gida a Beit Lahia.
An kuma kashe wani Falasdine sakamakon harin drone a al-Mawasi, yammacin Khan Younis.
Hare-haren rokoki sun auka kusa da Masallacin al-Hilmi Saqr a Rafah.
Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta sanar da cewa yawan wadanda suka mutu ya kai 50,144, yayin da 113,704 suka jikkata tun farkon yakin a 7 ga Oktoba, 2023.
A cikin kwana guda kacal, an kawo gawarwaki 62 da wadanda suka jikkata 296 zuwa asibitoci. Sai dai ana kyautata zaton cewa adadin gaskiya ya fi haka, saboda mutane da dama suna cikin baraguzan gine-gine da kuma wuraren da ba a iya kai musu agaji saboda ci gaba da hare-haren Isra’ila.
A gefe guda, Isra’ila ta kama ma’aikatan lafiya 15, ciki har da jami’an gaggawa da na kwana-kwana a Rafah a kwana biyu da suka gabata. Gwamnatin Gaza ta yi Allah wadai da wannan a matsayin cin zarafi da take dokokin kasa da kasa.
Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta yi gargadi kan karancin jini a bankunan jini, tare da bayyana cewa akwai bukatar akalla ruwan jini 8,000 a kowane wata domin kula da wadanda suka jikkata da masu cututtukan da suka shafi jini.
Sai dai saboda karancin abinci, ruwa, da magunguna, mutane sun kasa yin gudunmawar jini. A halin yanzu, asibitocin Gaza na aiki cikin yanayi na gaggawa tare da karancin kayan aikin likitanci da magunguna.
Ma’aikatar ta yi kira ga al’umma da su je asibitoci domin yin gudunmawar jini don ceton rayukan wadanda suka jikkata.
Yayin da Isra’ila ke ci gaba da luguden wuta ba tare da alamun dakatawa ba, yanayin jin kai a Gaza na kara tabarbarewa tare da fargabar cewa adadin wadanda za su mutu zai karu idan ba a dauki matakan gaggawa ba.
