Offline

Isra'ila Ta Saci Gawarwakin Palasɗinawa Sama Da 2000 Daga Kaburburan Su - Cewar hukumar lafiya ta Palasɗinawa

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan 

Dakarun Isra'ila sun kwashe gawarwaki sama da 2000 daga kaburburan su da suka tone a makabartu mabanbanta a faɗin zirin Gaza, rahoton ofishin watsa labarai na hukumar Gaza ya bayyana cewa sojin na Isra'ila sun dawo da wasu gawarwakin bayan sun keta alfarmar su.


A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya fitar da bayanan yadda Isra'ila ta sace gawarwakin sama da Palasɗinawa 2000 tun daga fara wannan kisan bayan 07 October, Kuma sun dawo da wasu cikin mummunan yanayi.


" A cikin kwanaki 304 na kisan kiyashin kan Palasɗinawa, sojin Isra'ila sun yi garkuwa da gawarwakin Palasɗinawa sama da 2000 daga gomomin maƙabartu a faɗin zirin Gaza, inda suka riƙa haƙa ƙaburburan da motar rusau da ake kira 'Bulldozzer' da wasu motocin soji, wannan kuma cin zarafin ɗan Adam ne" wani bangare na bayanan da Ofishin suka fitar.


Bayanan sun kara da cewa "Sojin na Isra'ila sun keta alfarmar gawarwakin shahidai 89, sun mayar dasu ƙwarangwal (Skeleton).


Daraktan hukumar bada agaji ta 'Palestinian Civil Emergency Service ' a Khan Yunis dake kudancin Gaza Yamen Abu Sulaiman ya bayyana cewa a ranar Litinin ɗin da ta gabata sun karbi gawarwaki 80 a cikin jakun kuna 15, hakan na nufin akwai shahidai sama da 4 a cikin kowace jaka, an naɗe su a wuri ɗaya.


Abu Sulaiman ya kara da cewa Sojin na Isra'ila ba su kawo wani bayani ba akan gawarwakin, ba bu sunayen su ko inda suka samo su ko suka ciro su, ya bayyana hakan a matsayin laifin yaƙi da keta alfarmar ɗan Adam.


"Bamu sani ba ko Shahidai ne ko kuma tsararru da Isra'ila ke kashewa a tsare ta hanyar azabtar wa a gidajen yari" ya bayyana cewa za a yi bincike kan gawarwakin domin a tatance ko za a iya gane ko su waye da kuma yadda aka shahadantar da su.


Ƙungiyar gwagwarmaya ta Palasɗinawa 'Hamas' ta bayyana cewa kawo gawarwakin shahidai 89 da Isra'ila ta yi, ya nuna gayar ta'addancin da Isra'ila ka aikatawa kan al'ummar Palasɗinu.

Post a Comment

Previous Post Next Post