Offline

Isra'ila Ta Hana A Shigar Da Riga-kafin Polio Sama Da Miliyan 1 Gaza.



 Daga - Mahadi Tukur Almizan 

Kwanan nan sojin Isra'ila suka riƙa shelar yi ma sojojin su Riga-kafin Polio a lokaci guda kuma sun bar Palasɗinawa su kamu da cutar.


A ranar 7 ga watan August ma'aikatar lafiya ta Palasɗinawa 'Palestinian Health Ministry' ta tuhumi Isra'ila da hana  riga kafin Polio sama da miliyan ɗaya da ake tsananin buƙata shiga zirin Gaza.


"Zirin Gaza na bukatar na bukatar riga kafin Polio miliyan ɗaya da ɗigo uku (1.3 million), amma haryanzu Isra'ila ta hana a shiga da riga kafin zirin na Gaza" cewar Daraktan sashin 'Health Care' na ma'aikatar lafiyan ta Palasɗinawa Musa Abed.


"Barazanar yaɗuwar cutar ta Polio a zirin Gaza za ta cigaba da ƙaruwa samakon cigaban ta'addancin Isra'ila da kuma karancin kayan aikin lafiya, duk wani tsaikon da aka samu ma shigowar riga kafin zai kara ta'azzara lamarin da ake fama dashi yanzu haka na rashin lafiya musamman ga ƙananan Yara da masu shekaru da kuma marasa lafiya" cewar Musa Abed


Cututtukan Infection na cigaba da yaɗuwa a zirin na Gaza cikin sauri sakamakon ta'addancin Isra'ila da ya raba kusan Palasɗinawa miliyan 2 da muhallan su.



"Akwai babbar musibar yaɗuwar cututtuka a zirin Gaza, a halin yanzu akwai adadi mai yawa na  wadanda suka kamu da cututtukan da ake kira "Waterborne or Respiratory disease", a yanzu haka akwai sama da mutum dubu ɗari dake fama da 'Epidemic hepatitis' wanda a shekara ɗaya kafin Isra'ila ta fara kai hare haren ta'addancin akwai mutum 85 ne kawai dake fama da wannan cuta a faɗin zirin Gaza gaba ɗaya"  Cewar ministan ma'aikatar lafiya ta Palasɗinawa Majed Abu Ramadan a ranar 4 ga watan nan da muke ciki na August.


Ya kara da cewa babbar musibar da suke fargaba yanzu ita ce yaɗuwar cutar Polio a faɗin zirin Gaza.


Wannan gargaɗi da ministan ya yi a ranar 4 ga watan ya biyo bayan maganar da hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya (WHO) ta yi cewa za ta turo riga-kafin Polio guda miliyan 1 zuwa zirin na Gaza.

Post a Comment

Previous Post Next Post