Offline

An Tsinci Gawarwakin Palasɗinawa Uku, Isra'ila Ta Kashe Su Bayan Ta Sake Su Daga Prison.

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan


An tsinci gawarwakin ne a kusa da bodar Gaza da Isra'ila, hannayen su a ɗaure da ankwa tsirara babu kaya a jikin su.


A jiya Litinin 8 ga watan July kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana cewa sojin Isra'ila sun kashe Palasɗinawan guda uku jim kaɗan bayan sakin su daga tsarewar da Isra'ilar tayi masu.


A ranar Lahadi ne aka tsinci gawarwakin hannayen su a ɗaure kuma babu kaya a jikin su a kusa da iyakar Karem Shalom dake tsakanin Gaza da Isra'ila.


Kawun ɗaya daga ciki matattun mai suna Abdel Hadi Ghabayen ya bayyana ma Reuters cewa ya fita neman dan nashi Kamel Ghabayen da safiyar ranar Lahadi bayan sojin Isra'ila sun kamashi a ranar Asabar.


"Na iske gawar shi kwance a kasa tare da gawar wasu shahidai biyu ko kaya babu a jikin su, hannayen su kuma an ɗaure su da roba (Had plastic cuffs), abinda sojin Isra'ila suka aikata kan su kenan" inji Ghabayen.


Ghabayen ya bayyana cewa sojin Isra'ila ne suka hari ɗan nashi da sauran Shahidan biyu bayan sun sake su, "Ɗaya daga cikin su ma an cire mashi ƙafa anyi kaca-kaca da gawarshi" cewar Ghabayen


Yayin da Ghabayen ya fara neman ƙafar wanda aka cire ma kafar a wajen sai sojin Isra'ila suka buɗe mashi wuta shima


Daga baya ne ya samu ya dauko gawarwakin a motar shi zuwa "Nasser Hospital" dake Khan Yunis.


Sauran Shahidan biyu sune Mohammad Awad Ramadan Abu Hejazi da kuma Ramadan Awad Ramadan Abu Hejazi.


Wani bafalasɗine Mahmoud Abu Taha da aka saki ya bayyana cewa suma haka sojin na Isra'ila suka buɗe masu wuta bayan sakin su.


"Mun isa titin Karkar a cikin Gaza munyi kamar mintuna 10 anan sai muka ga anjefo mana bom Allah yasa ina gaba, haka bom ɗin ya kashe mutum bakwai daga cikin mu, na gode ma Allah da ya raya ni" cewar Abu Taha


Tun daga fara wannan yaƙi Isra'ila ta dauke dubunnan Palasɗinawa tana rike dasu tana yi masu azaba mai tsanani.



A ranar 6 ga watan June da ya gabata kafar yaɗa labarai ta New York Times ta wallafa wani rahoto na shaidun yadda Isra'ila ke azabtar da Palasɗinawa a wurin da suke tsare mutane mai suna 'Sde Teiman Camp' rahoton ya bayyana cewa sojin Isra'ila na yi ma Palasɗinawa azaba da kujerar lantarki, hakanan suna tursasa su zama akan zazzafan rodi mai ɗauke da lantarki.


Ana tsare da Palasɗinawa 36 ƴan Gaza suka mutu a wannan wurin azaba na 'Sde Teiman Camp'

Post a Comment

Previous Post Next Post