Offline

Isra'ila Ta Jefa Bom A Filin Ƙwallon Palasɗinawa Mutum 29 Sun Rasa Rayukan Su.

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

A ranar Talata sojin Isra'ila suka jefa Bom a filin ƙwallon Makarantar Auda da Palasɗinawa ke gudun hijira a Abassan dake gabashin Khan Younis.


Shaidar gani da ido ya tabbatar wa manema labarai cewa akwai taron mutane a filin ƙwallon dake kallon Match ɗin da ake bugawa a filin ciki harda Mata da ƙananan Yara da masu tallar biscuits da sauran wasu abubuwa, duk suna daga cikin mutanen da suka rasa rayukan su aƙalla mutum 29.


Shaidar gani da idon a garin na Abassan mai suna Ghazzal Nasser ta bayyana ma kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa " Sun taru suna kallon wasan ƙwallon da ake bugawa kwatsam sai Bom ya tarwatsa wajen, naga masu raunuka da Shahidai kwance bayan faruwar lamarin, jikkunan mutane sun yi kaca kaca sassan jikin mutane daban daban cikin jini".

Kafar yaɗa labarai ta Aljazeera ta fitar da bidiyon yadda ake buga wasan ƙwallon a filin makarantar har zuwa lokacin saukar Bom ɗin da bayan fashewar Bom ɗin zaku iya kallo a kasa down 👇


"Komai na tafiya daidai, masu wasa na buga wasa, ƴan kallo na kallo, masu siyar da abubuwa na yin ciniki, kuma babu ƙarar jirgi kwata kwata".


Rundunar sojin Isra'ila tace tana kan bincikar rahoton cewa an kashe fararen hula a harin, saboda su sun jefa ma wani ɗan Hamas bom ne saboda yana daga cikin waɗanda suka kai ma Isra'ila harin 07 October wanda ya yi sanadiyyar ɓarkewar yaƙin Gaza.


Wai sojin na Isra'ila basu samu sakon cewa fararen hula suna buga wasan ƙwallon ƙafa ba a wajen lokacin da aka basu umarnin jefa Bom ɗin.


Anyi jana'izar Shahidan a kusa da asibitin Nasser Hospital inda mutane suka taru domin yin bankwana da Shahidan kafin a binne su.


Daya daga cikin ƴan uwan waɗanda suka rasu a harin mai suna Asmaa Qudeih ta bayyana ma manema labarai cewa "Makarantar a cike take da mutane har titi ma ya cika, kwatsam sai missile ya sauka ya tarwatsa wajen baki ɗaya".


"Jikkunan mutane sun tarwatse, bangarorin jikin mutane sun fita daban daban" a cewar Asmaa 



Haka dai sojin Isra'ila ke cigaba da ta'addancin su kan al'ummar Palestinu a kowace rana, ko a ranar Laraba ma sun riƙa shiga gidajen mutane suna bincike a arewa da kuma tsakiyar Gaza.

Post a Comment

Previous Post Next Post