Offline

An Kama Ɗaruruwan Masu Zanga-zangar Adawa Da Zuwan Netanyahu Amurka.

 


Daga - Abdurrahman Bala Idris & Mahadi Tukur Almizan

Ƙungiyar Yahudawada ake kira 'Jewish Voice For Peace Activist' ne suka shirya zanga-zangar.


Masu zanga zangar nuna goyon bayan Palasdinawa 200 ne aka tsare a Capitol Hill a ranar 23 ga watan July, gabanin jawabin da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi wa Majalisar Dokokin Amurka.


An gudanar da zanga-zangar ne a ginin ofishin Canon House.


Masu zanga-zangar, suna sanye da riguna masu ɗauke da rubutun "Ba da sunan mu ba".


A cewar ƴan sanda an gargadi masu zanga-zangar cewa gudanar da zanga-zangar a ginin ofishin Canon ya sabawa doka.


Babban Daraktan ƙungiyar ta Muryar Yahudawa don Zaman Lafiya, Stefanie Fox, ya ce jawabin da firaministan Isra'ila ya yi a Majalisa ranar Laraba shi ne dalilin zanga-zangar.


"Tsawon watanni tara, muna kallo cikin firgici yayin da gwamnatin Isra'ila ke aiwatar da kisan kiyashi, da makamai da kuma tallafin Amurka.


Majalisa da gwamnatin Biden suna da ikon kawo karshen wannan firgici a yau, maimakon haka, shugabanmu yana shirin ganawa da Netanyahu kuma shugabancin majalisar ya karrama shi da gayyatar yin jawabi ga Majalisa,” inji ta.


Wakilin Republican Mike Lawler ya kira zanga-zangar a matsayin "abin kunya" kuma ya zargi masu fafutukar neman zaman lafiya na ƙungiyar ta muryar Yahudawa da kasancewa "masu goyon bayan Hamas." 


Tun a watan Mayu ne kakakin Majalisar Wakilan Amurka Mike Johnson ya sanar da zuwan Netanyahu domin yin jawabi ga Majalisar Amurka.


Kuma a wannan lokacin ne kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta bada sammacin kama Netanyahu da ministan tsaronsa. 


Johnson ya yi barazana a lokacin sanarwar sa a watan Mayu cewa Amurka "ya kamata ta hukunta" kotun ICC saboda hukuncin da ta yanke. 


Firaministan Isra'ila ya isa birnin Washington a ranar Litinin, gabanin jawabin da zai yi a majalisar dokokin kasar a ranar 24 ga watan Mayu da kuma ganawa da shugaban Amurka Joe Biden, wanda aka shirya yi washegari.



Kotun ta ICC ta fada a ranar Talata cewa ta amince da kararraki 64 da ƙasashen duniya da ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi suka shigar na shiga tsakani  da bukatar kama Netanyahu da wasu ciki har da shugabannin Hamas.


Jawabin da firaministan ya yi a Majalisa ya zo ne a rana ta 292 na yakin kisan kare dangi da Isra'ila ke yi a zirin Gaza, wanda ya kashe mutane sama da 39,000 - galibi mata da yara - tare da jikkata sama da mutane 90,000.

Post a Comment

Previous Post Next Post