Daga - Abdurrahman Bala Idris
Ma'aikatar watsa labarai ta Gaza ta sanar da cewa akalla yara 16,000 Isra'ila ta kashe a wuraren da ta mamaye tana kai hare hare tun daga watan Oktoba zuwa yanzu.
A wata sanarwa da Ofishin ya fitar ya nuna adadin mutane 39,000 sukayi shahada tun farkon yakin na Gaza.
Ofishin ya kara da cewa akalla ansamu masu raunuka kimanin 90,000 tun farkon yakin wanda mafi yawanci mata ne da kananan yara haka kuma akalla mutane 10,000 sun bata.
Yara 34 sukayi shahada saboda rashin abinci yayin da akalla yara 17,000 suka zama marayu.
Sabuwar ƙididdigar da akayi ta nuna cewa ansamu karuwar mutuwar Falasɗinawa akalla 186,000 ko fiyeda haka duba da ƙiyasin kashi 7.9 na adadin jama'ar Gaza.
A wani rahoton da aka fitar a farkon wannan watan, kafar "The Lancet" ta bayyana cewa adadin wadanda suka mutu a yakin ya hada da wandanda gine gine suka danne.

