Offline

Rasha A Shirye Take Ta Baiwa Duk Masu Adawa Da Amurka Makamai - Cewar Dmitry Medvedev Na Rasha


Daga - Mahadi Tukur Almizan

A ranar Alhamis shugaban Rasha Dmitry Medvedev ya sanar cewa Moscow ta shirya tsaf domin ta baiwa maƙiyan Amurka makamai a matsayin martani bisa aika ma Ukraine makamai da Amurka da ƙawayenta suke.

Shugaba Putin ne ya bayyana wannan matsayar a zaman da yayi da kafafen yaÉ—a labarai na kasashen waje.

Dmitry ya bayyana cewa basu shirya Foreign Policy É—in kasar ba sai yanzu da Amurka da Æ´an koren su suka É—aura aniyar aiko da kowane irin makami zuwa Ukraine domin rusa kasar Rasha ta kowace hanya, a gefe guda kuma suna yi ma duk wani mai tunanin taimakawa Rasha wajen tsaron kasar ta barazana.

"Yanzu Amurka da ƙawayenta su shirya ganin makaman Rasha a hannun wasu mutane ko ƙasashe" cewar Dmitry, ya kara da cewa " Ba zamu bayyana waɗannan mutanen ko kasashen da zamu baiwa makamai ba a halin yanzu, amma a sani cewa zasu iya kasancewa duk masu ganin Amurka da ƙawayen ta a matsayin maƙiya, ba ruwan mu da yadda duniya ke kallon su".


Amurka da ƙawayenta sun kara kaimi wajen aika makamai zuwa Ukraine ko a cikin makon nan France ta bayyana zata aika da jirgin yaƙi ƙirar "Mirage-2000" zuwa Ukraine.

Dmitry ya rufe maganar shi da cewa "Duk Wani Maƙiyin Amurka Abokin Mu Ne"



Post a Comment

Previous Post Next Post