Daga - Mahadi Tukur Almizan
Jirgin yaƙin Isra'ila ya jefa Bomb a wata makaranta a sansanin gudun hijira na Nuseirat dake Gaza a safiyar yau Alhamis 6 ga watan June kamar yadda kafar yaɗa labarai ta WAFA News Agency ta labarto.
Masu bada agaji sun bayyana cewa sun yi nasarar ƙwaƙulo gawar mutum 32 daga baraguzan ginin kuma ana tsammanin adadin zai ƙaru.
Dubunnan PalasÉ—inawa ne suke zaune a makarantar tun bayan da hare haren Isra'ila suka raba su da gidajen su ta ta'addancin da Isra'ilae take yi tsawon watanni bakwai.
Mai magana da yawun ofishin sashen yaÉ—a labarai na gwamnatin Gaza Isma'il al-Thawabta ya bayyana cewa an cigaba da kawo adadi mai yawa na masu raunuka a asibitin Al-Aqsa dake tsakiyar Gaza.
Ya kuma bayyana ma manema labarai cewa wannan mummunan harin da Isra'ila ta aikata ya isa ya zama shaidar cewa Isra'ila tana aikata kisan kiyashi kan mata da yara a zirin Gaza.
Ya kara da cewa a halin yanzu dai asibitin da Al-Aqsa ta cika da masu raunuka mutanen dake ciki sun ruɓanya adadin da asibitin zata ita dauke sau uku.
Isra'ila kuma a gefe guda tayi iƙirarin kai harin ne da sunan wai dakarun Hamas sun ɓoye a sansanin.
BREAKING| The death toll of the Israeli targeting of an UNRWA school in Al Nuseirat refugee camp, sheltering thousands of displaced citizens, has risen to 30.
— Quds News Network (@QudsNen) June 6, 2024
The head of the Government Media Office stated that the number is expected to rise as dozens of casualties continue to… pic.twitter.com/RwXD1LYrjp
Mai É—aukar hoto na kamfanin dillancin labarai na AFP ya dauko hotunan yadda mutane ke kwance a wurin kafin harin da kuma yadda ake dauke katifu sharkaf da jini bayan harin.

