Offline

Sansanonin Amurka Da Ke Kasashen Yankin Gulf

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

Amurka na da aƙalla dakaru dubu arba'in (40,000) a gabas ta tsakiya, mafi yawan su suna a ƙasashe masu arzikin man fetur a yankin Gulf.


A ƙasar Saudiyya suna da dakaru a sansanin sojin sama mai suna Prince Sultan Airbase, a wannan sansanin akwai dakarun 378th Sir Expeditionary dake sarrafa jiragen yaƙi na F-16 da F-35.



A Dubai kuwa  Amurka tana da dakarun dake jirage marasa matuÆ™i (Drones) sarrafa MQ-9 Reaper da wasu jiragen yaÆ™i a sansanin  sojin sama na Al-Dhafra.



A ƙasar Kuwait kuwa nan ne gidan dakarun Amurka na 386th Air Expeditionary a sansanin Ali al-Salem Air Base.



A Qatar kuwa nan ne kamar Headquarter umarni ta dakarun Amurka dake gabas ta tsakiya wato US Central Command, suna a sansanin Al Udeid Air Base, akwai labarin dake cewa ma akwai dakarun sojin Isra'ila a wannan sansanin sai dai babu tabbacin ko haryanzu suna cigaba da zama a sansanin.



Ƙasar Bahrain kuwa ta zama gida ga dakarun Amurka aƙalla dubu tara (9,000) wadannan su wani bangare ne na dakarun Headquarter sojin ruwa na Amurka.

©️ Freedom Fighters Ng

Post a Comment

Previous Post Next Post