Offline

GUGUWAR AL-AQSA:KAFA HAMAS, BITAR JIGA-JIGAN HAMAS DA ISRA'ILA TA KASHE TUN FARKON KAFA TA, SU WANENE MANYAN KWAMANDOJIN HAMAS DA SUKA JAGORANCI HARIN 7 OKTOBA GA ISRA'ILA

 



Daga - Yusuf Kabir.

A ranar 14 ga watan Kanunul-ula a shekarar 1987 bisa jagorancin Shaikh Ahmad Yaseen aka assasa motsin Hamas.Wannan kuma ya faru ne a sad da aka yi gwagwarmayar kariyar kai ta duwatsu a ranar 9/12/1987.


Motsin Hamas ya sami karbuwa a tsakanin Palasdinawa da ma'abuta gwagwarmaya da kwatar 'yanci a duniya.Hamas a shekarar 1987 suka dauki makami bayan sun assasa rundunar Mujahidai da suka kira ''Mujahidunal-Falasdiniyyun''


Wasu bayanai da Hamas suka bayyana bayan kafa su.



1.Sun bayyana cewa:su wani bangare ne na alkawarin da aka samar a shekarar 1988 sannan suna karkashin fahimtar Ikhwanil-Mislimin ne da ke da reshe a kasar Palasdinu.



2.Samar da bangaren Soji:Hamas sun bayyana cewa sun samar da bangaren ayyukan Soji da suka ambata da ''Kata'ibu Izziddeen Kassam'' (Bataliyoyin Izzudeen Kassam) a ranar 1 ga watan Janairu 1992.



3.Ayyukan siyasa:A shekarar 2006 Hamas suka ga amfanin aiwatar da motsin siyasa a kasar Palasdinu;hakan ya sa suka shiga zabe kuma suka samu 'yan majalissu masu tarin yawa a kasar.


4.A watan Mayu na shekarar 2017 Hamas sun aiwatar da wasu gyare-gyare dangane da yadda suke gudanar da siyasarsu domin samun nasara.Wannan matakin kuma ya samar musu da nasarori masu yawan gaske.






BITAR JIGA-JIGAN HAMAS DA ISRA'ILA TA KASHE TUN FARKON KAFA TA


Haramtacciyar kasar Isra'ila ta rika bin kusoshin rundunar Hamas tana kashewa ga bitar wasu daga cikin su:-


1.Shaikh Ahmad Yaseen:Shi ne wanda ya assasa motsin.Wanene Shaikh Shaheed Ahmad Yaseen wanda ya kafa Hamas?


Sunansa Ahmad Isma'il Yaseen,an haife shi a garin Jauzatil-Asqalani da ke lardin Gazza cikin kasar Palasdin.


Shaikh Ahmad Yaseen ya ta so cikin jarabawar rasuwar Mahaifinsa tun yana dan shekara 3 a duniya.Ya ta so ne yana maraya a sakamakon rasuwar Mahaifinsa a yayin da Mahaifiyarsa ce ya ci gaba da kula sa rayuwarsa.


Gwagwarmayarsa da karatunsa!



Shaikh Ahmad Yaseen ya yi karatu a Gazza daga bisani ya ci gaba da karatunsa a jami'ar Azhar da kasar Masar.A yayin da yake karatu a Masar kuma,ya tasirantu da fikirorin 'yan uwa Musulmi da ke Misra wanda Shaikh Hasanil Banna ya kafa da musu tarbiyya.


Yadda Isra'ila ta tsare a kurkuku.


Haramtacciyar Qasar Isra'ila ta kama Shaikh Ahmad Yaseen tare da tuhumarsa da ayyukan nuna kin jinin Yahudawa da kyamata su a cikin al'umma.Da wannan dalilin ne ta kama shi a shekarar 1983 ta tuhumar fafutikar kawar da Yahudawa a yankin,a shekarar 1985 kuma suka sake shi a yayin musayar Fursunoni da aka  aiwatar tsakanin 'Yan Hamas da Yahudawan Isra'ila.


A shekarar 1991 aka sake kama shi,a yayin da wata kotu a Isra'ila ta yanke masa hukuncin rai-da-rai,daga bisani dai Allah ya kubutar da shi daga hannunsu.


Shaikh Shaheed Ahmad Yaseen,Dr.Shaheed Abdulazeez Rantisi su  ne dai suka  kafa kungiyar Hamas da suke bayar da kariya ga kasar Palasdinu daga kisan kare dangin da Yahudawa suke yi a zirin Gazza.


Shahadarsa!


Yahudawa 'yan share-guri-zauna ne dai suka shahadantar da Ahmad Yaseen ta hanyar ruwan Bama-bamai a kan sa da 'yan rakiyarsa a sad da ya dawo daga masallaci bayan kare sallar Asubahi.



2.Ahmad Abu Shanbi:Daya ne daga cikin manyan Kwamandojin Hamas da Isra'ila ta kashe a ranar 21/8 2003.


3.Kwamanda Abdul'azeez Rantisi:Daya ne daga wadanda suka yi musharaka wajen assasa motsin Hamas.Ya yi shahada a ranar 14/4/2004.


4.Ahmad Jubarayi:Daya ne daga kwamandojin Katibar Izzudeen Kassam.An kashe shi a ranar 14/6/2012.


Wadannan tsakure ne daga jiga-jigan Hamas da haramtacciyar kasar Isra'ila ta kashe a lokuta mabambanta.



SU WANENE MANYAN KWAMANDOJIN HAMAS DA SUKA JAGORANCI HARIN 7 OKTOBA GA ISRA'ILA


Tun ranar Asabat 7 ga Oktobar wannan watan,rundunar gwagwarmaya ta Hamas da ke Palasdinu suka yi martanin kashe wasu Palasdinawa da aka yi ta hanyar kai hari a kan bangarorin tsaro na kasar mamaya wato Isra'ila.

Tun sad da labaran wannan mayar da martani da Palasdinawa suka yi ya fara yaduwa;masanan yaqi da tsaro na kasashe suka fara nazartar yadda Hamas suka kaddamar da harin nan wanda ba a taba yiwa Isra'ila mummunar marna shekaru 70 baya ba kamar shi.Masanan sun ci gaba da nazartar yadda Isra'ila din ta kasance kasa wacce ta ke da tsaro da kuma samun goyon bayan duniya.Amma a gefe guda kuma,an rika tambayar shin wadanne Kwamandoji ne Hamas ta samu da ke jagorantar rundunar zuwa ga wadannan nasarorin,abunda ke tafe bayani ne a kan wadansu Kwamandoji guda 6 da rawar da suka taka wajen kai harin,a sha karatu lafiya.

1.Muhammad Daifi:Sunansa Muhammad Dayyaf Almisriy an haife shi a shekara ta 1965 a birnin Gazza.Lakabinsa shi ne ''Daifi'' Alkunyarsa ''Abu-Khalid'' Kasar mamaya ta Isra'ila na masa lakabi da ''Mutum daya mai tai 6'' ko ''Aljani wanda ba san fuskarsa ba sai dai ayyukansa'' Ya yi degree dinsa na farko a Jami'ar Musulunci ta Gazza a kan ''Biology'' sannan yana da basirar wasan kwaikwayo da shirya abubuwan da suka shafi ayyukan basira da hazaka.

Sad da aka bayyana Samar da rundubar Hamas a Gazza,ba tare da taradudi da tsoro ba ya tsunduma ciki a shekara ta 1989,sannan Isra'ila ta taba kama shi ta tsare shi na watanni 16 ba tare da an kai shi kotu ba.A sad da yana tsare sun tattauna da Zakariya Shurubarji da da Salah Shahha a kan assasa runduna karkashin Hamas mai suna ''Kassam'' wacce aikinta shirya hare-hare domin kame sojojin mamaya.

 A sad aka kama shi an tuhume shi da laifuka daban-daban mafi girma a cikin shi ne shirya harin da ya kai ga mutuwar Yahudawa 50 da raunata da dama a shekarar 1996.Bugu da kari an sake kama shi a shekarar 2000 wanda ya kubuta daga gidan yari bayan wani sulhu da aka yi tsakanin Isra'ila da Palasdinawa.

Yunkurin halaka shi

Tun sad da aka sake shi a shekarar 2000,bayaninsa,ya buya ga Isra'ila sai dai sun yi yunkurin halaka shi a lokuta mabambanta,amma yana tsallakewa.A shekarar 2002 an kai masa mummunan hari,in da ya kubuta duk da an karya kafarsa da hannunsa kamar yadda Hukumar Isra'ila suka bayyana.Bugu da kari yana fuskantar wahalar magana saboda hare-haren da ya fuskanta a lokuta mabambanta.

A shekarar 2014 Isra'ila ta kaiwa Muhammad Daifi hari sad da ta yi kwanaki 50 tana kaddamar da hare-hare a kan Gazza;sai dai ya tsallake duk da hakan sun kashe matarsa da 'ya'yansa biyu.

A na masa lakabi da ''Daifi'' (ma'ana bako) ne  saboda bai da takamaiman wajen rayuwa,bai da takamaiman kayan sawa,rahotanni na bayyana cewa,kusan kullum sai ya canza muhallin da zai kwana saboda batar da sawun MOSSAD yadda take bibiyarsa. Duk hakan har zuwa yanzu Isra'ila ba ta takamaiman hotonsa.

2.Marwan Isa:Shi ne na hannun daman Muhammad Daifi, sannan mataimaki a gare shi kuma abokin gudanar da ayyuka.Isra'ila na masa lakabi da ''sawun Keke'' ba a gane gabanka'' ko kuma ''hawainiya mai caccanzawa''

Isra'ila ta taba kama shi ta tsare har na tsawon shekaru 5 saboda ayyukansa a kungiyar Hamas.

Kungiyar leken asirin Isra'ila ta bayyana shi a matsayin mai juya akalar Hamas,sannan daya daga cikin Jagororinta.Ta bayyana cewa,matukar yana a raye,to tabbas ba za ta yi galaba a kan Hamas ba.

Isra'ila ta yi yunkurin halaka shi a lokuta mabambanta manya a cikinsu su ne a shekarar ''2006,2011,2014,2021''Duk yana tsallakewa sai dai samun raunuka a jikinsa.

3.Yahaya Sinwar:A watan Yulin 2015 majalissar dinkin duniya ta sanya shi cikin List na 'yan ta'addar kasa-da-kasa.

An haife shi a shekarar 1962 a birnin Gaza.Shi ne yake Jagorantar rundunar ''Majad'' runduna ce ta sirri domin bibiyar motsin MOSSAD da kuma Jagororin Hukumar Isra'ila.

   An kama Sinwar sau uku,su ne a  shekarar 1988,1982,2011 in da daga lokacin ba a sake kama shi ba.

4.Abdullahi  Bargusi:Shi kwararre ne wajen hada Bama-bamai da Nakiyoyi manya da kanana.An haife shi a kasar Kuwaitia shekarar 1972,bayan nan ya sami shaidar zama san kasar Palasdinu.

Bargusi ya zamanto kwararre wajen hada Bama-bamai,shi ne harhada ababen fashewar da suka kai ga mutuwar Isra'ilawa 66,da raunata sama da 500.

An kama shi tattare da kai shi Kotun Isra'ila in da aka yanke masa hukuncin shekaru 65,da Karin shekaru 5200 a tsare.

Bargusi ya yi yajin kin cin abinci da ya kai ga sakinsa bayan wani yunkuri daga rundunar Hamas.A sad da yana tsare ya wallafa littafi mai suna ''AMIRIL-ZIL'' (Ma'ana shugaban inuwa) in da a ciki ya bayyana rayuwarsa da yadda ake hada Bama-bamai da abubuwa masu fashewa.

5 Isma'il Haniyye:Shi ne shugaban sashen siyasa na rundunar Hamas.Ya kasance na hannun daman Shaheed Shaikh Ahmad Yassin da Dr. shaheed Abdul'azeez Rantisiy.

A shekarar 1989 Isra'ila ta tsare shi na shekaru 3,sannan aka kora su iyakar Labnan tare da wasu 'yan Hamas.

6.Kalid Mish'il:Ya kasance cikin wadanda ke kula da sashen siyasa na Hamas.Mutum ne mai basira da hazaka.

Banjamen Natanyahu ya bayar da umarnin bin shi kasar Urdun domin kashe shi ta hanyar amfani da Mambobin MOSSAD;amma ya kubuta bayan Hukumar kasar Urdun sun gano shirin da Isra'ila ke aiwatarwa.

A watan Disambar 2012 ya ziyarci birnin Gazza bayan ya bar kasar tun yana dan shekara 11 da haihuwa.

7.Mahmuod Zahhar:An haifi Zahhar a birnin Gazza a shekarar 1945.Mahaifinsa Dan Palasidinu,Mahaifiyarsa kuma 'yar Misira CE.Ya yi digirinsa na farko a kan harkar lafiya a Jami'ar 

''AINISH-SHAMSI'' a kasar Misira a shekarar 1971.

Zahhar dai ya kasance wanda Isra'ila ke kaiwa hare-hare domin kashe shi a lokuta mabambanta amma yana tsira da raunuka.A shekarar 2006 Isra'ila ta wurga Bom a gidansa da niyyar kashe shi wanda nauyinsa zai iya kashe gomomin mutane,amma ya fita da raunuka.

Isra'ila ta kashe babban dansa Khalid a cikin hare-haren da take kaiwa Palasdinawa a Gazza.

Zahhar ya kasance marubuci,manazarci ya rubuta Littafai daban-daban ciki har da wanda ya yiwa Natanyahu raddi.

Wadannan dai sune mutum 7 jiga-jigan kungiyar Hamas da Isra'ila ke nema ta kashe ruwa a jallo.

Yusuf Kabir - 09063281016.

kabiruyusud533@gmail.com



Post a Comment

Previous Post Next Post