Daga - Mahadi Tukur Almizan
A cigaba da zaman ɗarɗar da ake a gabas ta tsakiya, ƙasashen yankin Gulf sun Gargaɗi Amurka kan lallai kar tayi amfani da sansanonin sojin ta dake ƙasashen su wajen kaima jamhuriyar Musulunci ta Iran hari kamar yadda kafar yaɗa labarai ta Middle East Eye ta labarto.
Ƙasashen ta yankin Gulf dai nata kokarin kawar da duk wani abu da zai jefa su cikin rigimar dake tsakanin Tehran da Washington saboda tsoron kar Iran ko ƙungiyoyin ƴan gwagwarmaya masu alaƙa da ita su kawo masu hari.
Ƙasashen sun haɗa da Oman,Dubai (UAE), Kuwait da Saudi Arabia, daga cikin matakan da suke ɗauka harda hana jiragen yaƙi na Amurka shawagi a sararin samaniyar su.
Ko a daren jiya da ƙasar Iran ta fara kai hare haren mayarda martani ƙasashen dake maƙotaka da Isra'ila sun rufe sararin samaniyar su irin su Jordan, Lebanon,Iraqi,Egypt harma Jordan tayi iƙirarin kakkaɓo duk abinda ya ratsa ta sararin samaniyar su.
Saidai Iran ta gargadi waɗannan ƙasashe cewa duk wata ƙasa da ta sake ta baiwa Isra'ila ko Amurka damar amfani da ita wajen kaima Iran hari to itama zata fuskanci hari daga Iran.
Amurka da ta daɗe tana kashe kuɗaɗe tsawon zamani wajen damar da sansanoni da gudanar da su a yankin na Gulf, kuma ta waɗannan sansanoni ne Amurka zata iya kaima Iran hari Kasancewar su a kusa da Iran ɗin kamar yadda wani tsoho jami'in Amurka ya bayyana ma kafar yaɗa labarai ta Middle East Eye.
©️ Freedom Fighters Ng

