A yakin nan na guguwar Al'aqsa masanan yaqi,manazarta,masanan Tarihi,fitattun 'yan Jarida sun rika bayyana ra'ayoyinsu a kan yakin nan.Wasu sashen na nuna barnar da Isra'ila ke wa Gazza,tabbas haka ne a zahiri,amma kuma a badini Hamas ce ta yi nasara a kan su,kamar dai yadda ya faru tsakanin Hizbullahi da Isra'ila a 2006.Ga jerin nasarorin da da Hamas ta yi a kan Isra'ila:-
1.Samun tausayawar al'ummomin duniya:wannan kuma a zahiri ma haka ne,domin an sami al'ummomi daga nahiyoyi daban-daban na tausayawa Palasdinawa.Hakan kuma yana nuna da a ce mutane da ke Muzaharori za su sami samar shiga Gazza;tabbas da sai sun kare Palasdinawa da rayukansu.
2.Yakin kwakwalwa:Duk da kasancewar mafiya yawan kafofin sadarwa Jaridu,mujallu,Talajibin,Rediyoyi da social media mallakin Yahudawa ne,amma tabbas Isra'ila ta sha kaye ta bangaren nan.Akwai Jazira,Press TV,da wasu kakafen da ke yada Barnar da hare-haren Hamas ke wa Yahudawa.Da zaran sun bayyana karya,sai rahoton gaskiya ya bayyana kuma ma'abuta hankali da 'yancin tunani suna fahimtar gaskiyar lamarin.A bangaren yakin kwakwalwa tabbas Hamas sun yi nasara a kan jikokin makasa Annabawa da 'ya'yan Annabawa (as).
3.Jefa tsoro a zuciyar Natanyahu:Rundunar Hamas bisa tallafin Iran,Hizbullahi sun sami nasarar jefa tsoro a zuciyar Firaministan Isra'ila Natanyahu.A ranar Talata 16/10/2023 kafar Aljazira sun bayyana wani bidiyo na Natanyahu fuskarsa cikin tsoro yana zagaya Sojojinsa yana cewa da su:''Ku daure,ku ci gaba da yakin nan,tabbas yanayin da muke cikin muna tsakanin mutuwa da rayuwa ne.''
4. Jefa rudani da firgici a tsakanin Sojojin Isra'ila:A ranar 24/10/2023 kafar Aljazira sun yada karamin Bidiyo;wani Sojan Isra'ila na zagin Natanyahu yana mai cewa:''Ka rusa qasa,ba za mu je yakin ba,abokanaina da yawansu an kashe su.'' A yayin da Almizan ta ga wani babban Soja na tsawatarwa karamin Sojan yana mai cewa:''kana da 'yancin bayyana ra'ayinka,amma sigar da aka yi amfani da ita ba ta dace ba.''Wannan ma nasara ce.
5.Samun daukakar rundunar Hamas:A tsawon shekaru 70 na kafa Isra'ila,ba a taba tona musu asiri da sance musu zani-a-Kasuwa kamar guguwar Al'aksa ba.Ina kwarewar MOSSAD,ina kurin basirar iya yaki?Ina dakarun da ba a iya gaba-da-gaba da su? Sai ga Media tana bayyana tankoki da gawarwakinsu.Hakan kuma karin samun daukaka ne ga Hamas.
Ku sauke Application ɗin Fadakdata anan👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.absoft.fadakdata
6.Tsohon jami'in CIA Scott's Ritter ya bayyana cewa:''Wannan yakin ya kara dagula lissafin Amurka da kawayenta,kuma da kyar idan ba za su sha kunya ba.
7.Daya daga cikin masu aiki a hukumar samar da tsaro ta Amurka ya bayyana cewa:''Sun aika runduna ta musamman domin tallafawa Isra'ila,kawai sai suka ga mambobin rundunar a na haska hoton jikkunasu a tarwatse a mace.
8.A ranar 23/10/2023 Hukumar tsaro ta Isra'ila sun bayyana cewa:''An kashe musu mutane 1210.Mu lura fa,Idan aka kashe 10 to biyu suke cewa,wannan kuma makircin Yahudu ne na rashin bayyana rauninsu a gaban muminai.
9.A ranar 21/10/2023 fitaccen masanin tarihin Isra'ila Illan Panel a hirarsa da Dan Jarida Ali Zafariy ya tambaye shi cewa:''Shin Hamas kungiyar ta'addanci ce''?Sai yace:''Hamas ba 'yan ta'adda ba ne ba,su wata runduna ce ta samar da 'yanci da tsaro ga al'a'ummarsu.''Masu magana na cewa:''Tsagwaron gaskiya ita ce wacce makiyi ya bayyana.''
10.Lallashin Iran da Amurka take yi a kan yakin:Ministan harkokin kasashen waje na Iran a ranar 23/10/2023 ya bayyana cewa:''Tun sad da aka fara yakin nan,Amurka sau 2 tana turo mana wasikar cewa ita fa ba ta son Iran ta Shiga yakin nan.''
11.Shugaban Faransa a ranar Alhamis 26/10/2023 ya ziyarci Isra'ila ya bayyana cewa;Na zo kasar nan domin in taya mu jajen wannan bala'i,akwai 'yan Faransa 30 da Shaidanun nan Hamas ta kashe.Babban fatanmu shi ne,murkushe su ta kowacce hanya.''
Ku sauke Application ɗin Fadakdata anan 👇
12.Lalatawa Isra'ila muhimmancin wurare:Ga mai bibiyar fafatawar nan zai riski cewa,Hamas a ranar farko babbar nasarar da suka samu ita ce,lalata dukkanin kyamarorin da ke jikin katangar da ke kaiwa Shalkwatar tsaron Isra'ila bayanai.Kuma tsawon kwanakinan na yaki,Hamas na kaiwa muhimman wurare hare-hare ne ba wai ta kashe mata da yara ba.A kalla a ranar Asabar 7/10/2023 sun kama wani kundi hannun Sojojin iyaka da yake dauke da dukkanin bayanan muhimmanci wuraren tsaro na Isra'ila.Kuma hakan yaDuk da fa Isra'ila din cikin matukar firgici da tsoro.
Don haka tabbas Isra'ila sun firgice ne hakan ya sa suke kai hare-hare kan kowa a Palasdinu!kuma yadda Imam Husaini (as) ya yi nasara tabbas Isra'ila za ta gushe a yayin da Gazza za ta wanzu insha Allahu.

