Offline

Rasha ta Zargi Amurka da hada soji masu tsaurin ra'ayi a Siriya don ta'azzara lamurra.



Ministan harkokin wajen Rasha,Seigei Lavrov ya zargi Sojin Amurka da daukar sojoji daga masu tsatstsauran ra'ayi da suka hada da ISIS don hada wata runduna mai suna "Free Syria Army" a cikin garin Raqqa dakeh arewacin siriyar.

Lokacin zaman mitin na kwana hudu da aka gabatar tsakanin Turkiyya da Iran,Lavrov ya bayyana cewa "Amurka tana tattara da yawan kabilun larabawa da mayakan kungiyoyin 'yan ta'adda don amfani dasu gurin wargaza zaman lafiyar siriyar'', Lavrov yayi gargadin cewa akwai bukatar kin goyon bayan wannan yunkuri na Amurka na samarda wadannan sojojin, haka kuma yayi Allah wadai da katsalandan din kasashen waje na kirkirar soji a wannan yankin.

A wani rahoto da aka fitar ya nuna cewa a Disambar shekarar da ta wuce, Sojin Mamayar Amurka suna gina wani sansani a kudancin shigowa garin Raqqa dukda barin garin da sukayi shekaru uku da suka gabata.

Kremlin ya sha zargin Amurka da horarwa da kuma bayarda makamai ga 'yan ta'addan ISIS,Al-Qaeda, da kuma Kungiyar 'yan ta'addan Hayat-Tahriril-Sham don su yaki sojin Rasha run farkon fara yakin Yukren da Rasha.

A cikin watan Maris Daraktan Wajen Kula da fikira na Rasha, Sergey Naryshkin, ya bayyana cewa Amurka na yunkurin shiryar da tarzoma a siriyar ta hanyar horar da masu tsatstsauran ra'ayi a kasar don farmakar sansanonin sojoji a siriyar da kuma kasar Iran hadi da yin garkuwa da ma'aikatan Iran da Rasha.

Ana zargin cewa Amurka tana taka rawar gani gurin samarda rundunar "Free Syrian Army" dakeda alaka da 'yan tawaye da kurdawa da aka kirkira a shekarar 2011 haka kuma sunada alaka da Kungiyar Al-Qaeda da ISIS.

A wani binciken sirri da aka gudanar ya nuna yanda tattaunawa ta gudana tsakanin sansanin sojin Amurka a Al-Tanf da kuma 'yan Kungiyar ISIS inda suka basu umurnin kai farmaki a sansanin sojin larabawan Siriya hadin gwiwa da sojin Kasar Iran.

Sojin Amurka hadin gwiwa da Kungiyar hadakar sojin kasar sun kauracewa sansanonin sojin siriyar dake Hasaka,Deir Ezzor da kuma Homs wanda yake da alaka da kamfanin raba mai da iskar gas na kasar siriyar.

Bugu da kari Amurka ta shigar da sojojinta dari tara 900 bah bisa Qa'ida ba a cikin kasar,kasancewar sojin acikin kasar da kuma gina sansanonin da Amurkar tayi ya haifar da damuwa da suka daga bangarorin kasashen duniya saboda saba dokar da Amurkar tayi na yin kutse a Siriya.

Post a Comment

Previous Post Next Post