Offline

Kwamandan Sojin Islamic Jihad na Falastin yayi shahada biyo bayan kisan da Isra'ila tayi masa yayin da abubuwa suka tsananta a Gaza


Wani reshe na Kungiyar gwagwarmayar falastinawa wanda akafi sani da "Al-Quds Brigade" ta bayyana bakinciki akan kisan kwamandanta na bangaren makamai masu linzami.

Kwamandan Ali Hassan Ghali wanda akafi sani da (Abu Muhammad), ana zargin sojin Isra'ila da shahadantar dashi a Khan Yunis,wani yanki a cikin garin Gaza.

Al-Quds Brigade sun fitarda sanarwar ne don girmamawa ga Kwamandan da kuma sauran shahidan da suka rasa rayukansu a farmakin.

A cikin kwanaki uku sojin mamayar Isra'ila sun tsananta hare hare ta sama a zirin Gaza, ta dalilin hare haren falastinawa uku da kwamandan suka rasa rayukansu.

Harin dai kai tsaye an kaishi neh akan wani gini garin Hamad kusada Khan Yunis a ranar Alhamis.

Wannan farmakin na zalunci dai yana cigaba da faruwa tun ranar Talata wanda yayi sanadiyar kisan falastinawa 24 da kuma raunata da dama.

Daga cikin wadanda abin ya shafa akwai Kwamandoji uku na Islamic Jihad tareda matansu da iyalinsu,don mayarda martani 'yan gwagwarmayar falastinawa sun mayarda martani da gomman makamai masu linzami wanda sukayiwa lakabi da "Revenge Free" (Daukar fansar Kawai), inda suka farmaki Telaviv da sauran garuruwan da Isra'ilar ta mamaye.

A wata sanarwar hadin gwiwa da kungiyoyin gwagwarmayar falastinawa suka fitar sunsha Alwashin kare rayukan falastinawa da kasarsu da kuma wuraren Ibada masu tsarki.

Haka kuma sun ayyana kasancewarsu a cikin shirin ko ta kwana muddin Israilar ta cigaba da farmaka da cin zarafinsu.

Hukumomi a Telaviv sun bayyana cewa fiyeda makamai masu linzami 400 neh aka harbo cikin garin daga yankin Falastinawa.

Post a Comment

Previous Post Next Post