Offline

Falasdinawa 'yan gidan yari sunyi shirin fara yajin cin abinci don nuna adawa da 'yan mamaya da kuma Neman asaki abokan zamansu maras lafiya.

Dubban yan gidan yarin sun shirya yajin cin abincin neh na kwana daya a ranar litinin, don nuna adawa da tsarin yan mamayar, da kuma neman asaki 'yanuwansu 'yan fursunar da basa da lafiya.

Babban kwamitin 'yan fursunan Falasdinawa ne suka sanarda yajin cin abincin a ranar lahadi,zasuyi yajin cin abincin ne don matsa lamba ga 'yan mamayar da kuma neman asaki dadadden dan fursunar falastin Walid Daqqah.

Walid Daqqa marubucine kuma dan gwagwarmaya da aka daure tun shekarar 1986 saboda nuna adawa da mamayar kasar Palasdine.

Shekarar da ta gabatane dai aka auna lafiyar Walid inda aka sameshi da kamuwa da cututtuka da suka hada da ciwon Cancer wacce take hana jininsa gudana, kara tabarbarewar lafiyar tasa tayi silar haifar mishi da ciwon sashin jiki wanda ya kai ga dole aka kaishi asibiti.

Daqqah yana daga cikin manyan 'yan fursunar da suka dade a hannun Isra'ila.

Yajin cin abincin kuma yana alawadai da damar da aka baiwa Israila na kama falasdinawa da kuma kullesu ba tareda yin shari'a bah, wanda ya sabawa hakkin 'yan Adam.

A wani rahoto na baya bayan nan ya nuna cewa fiyeda falasdinawa 4,900 ne Israila ta daure hadi da mata da kananan yara a gidajen yarin kasar.

Rahoton yazo neh a ranar Falasdinawa 'yan fursuna, inda suka bayyana cewa palastinawa mata 31 da kananan yara 160 da basu kai shekaru 18 ba suna daga cikin yan fursunar, haka kuma sun bayyana irin cin zarafi da kuma rashin tsaftataccen muhalli, da azabtarwa da kuma nuna kiyayya da ake yimusu a gidajen yarin kasar amatsayin abun kyamah da kuma take hakkin falasdinawan.
Previous Post Next Post