Wata tawagar da aka hada a bayan nan mai suna 'Anonymous Sudan' ta saki tarin sunaye (Usernames) da lambobin sirri (Password) da suke mallakin mutane fiyeda 762 daga shafukan Israila.
Bayanan da suka fallasa sun hada da na manyan bankunan Isra'ila kamar su Bank Hapoalim,Bank Leumi,Bank Hadoar,Telebank da sauransu.
Daga cikin mutanen da aka kaiwa farmakin an fallasa sunaye (Username) da kalmomin sirrinsu (Passwords) a fili haka ansamosu ne daga shafukan da ake gudanarwa dasu neh a yankin da aka mamaye daga cikin muhimman shafukan da aka kwamushe sun hada da Drushim IL,shafin kula da kwararrun ma'aikata,AllJobs.co.I'll,sshafin daukar ma'aikata na kasar Israila da kuma shafin govojobs.
Farmakin ya shafi Golan Telecom,babban kanfanin layukan sadarwar kasar Israila dake samarda Network a kasar.
Farmakin 'Anonymous Sudan' din ya nuna goyon bayansu ga falasdinawa da kuma 'yan gwagwarmayar falasdinawan,wannan farmakin kuma yana mayarda martani ne kan zaluncin Israila akan falasdinawa.
Lokacin farmakin kwanan nan a Gaza, (Anonymous Sudan) sun hana jiniyar ko ta kwana da Isra'ila keh amfani dashi gurin ankarar da jama'ar kasar lokacin faruwar farmakin makamai masu linzami a kasar.
A wani sakon gargadi da 'Anonymous Sudan' suka isar ga Israila sun sanarda cewa muddin Israila ta cigaba da farmakar Falasdinawa tabbas a shirye suke don cigaba da kai farmakin yanar gizo a kasar akowaneh lokaci.