Offline

WAFATIN SAYYIDA KHADIJA (S•A)

 


بسم الله الرحمن الرحيم

اللهم صل على محمد وآل محمد


اسم: خديجة (رض) ام المؤمنين، الاب: خويلد بن اسد بن عبدالعزى بن قصي بن كلاب القرشية، الام: فاطمة بنت زائدة، الشهادة:١٠ من الرمضان

السيدة هي اول من آمن برسول الله (ص) من الرجال علي (ع) و من النساء جديجة (رض)

Sayyida Khadija itace farkon wacce ta fara imani da Manzom Rahma a maza Imam Aliyu ne bn Abuɗalib a mata kuma Sayyida Nana Khadija, 


Sayyida Khadija matace ga Annabi mahaifiya ga Faɗimatuzzahra'u (s.a) Sayyida tabayar da dukiyarta dukkanta gurin taimakawa Annabi (s) dan tsayuwar addini har yakai komai nata yakare gurin taimakon Annabi (s) tare da takurar da quraishawa sukai musu da kuma ta kun-kumin da suka sama Annabi da sahabbansa na tsawon shekaru (3). 

     Nana Khadija tayi wafati ranar 10 gawatan ramadan shekara 10 da aiko Annabi kafin hijira da shekara 3, bayan wafatin Amminsa Abuɗalib da kwana 3.

     Sayyida Nana Khadija Ta bada gudun mawa sosai ga Annabi Wacce baza'a iya musultawaba kuma ta bashi kariya dan cigabantar da Addini musulunci, Saboda irin gudun mawar databa Annabi (s) har Allah ya aiko da Jibril (as) gurin Annabi (s) yake cewa:-

ان جبريل (ع) اتى رسول الله (ص) فقال: يارسول الله هذه خديجة قدأتت معها إناءفيه أدام، او طعام، او شراب، فأذا هي أتتك فاقرأ عليها السلام من ربها، ومني، وبشرها ببيت في الجنة من قصب لاصخب فيه ولا نصب.

Jibril (as) yazo gun Annabi ya cemai Ya manzon Allah wannan Khadijace tana maizuwa gunka tare da kwano acikinsa akwai miya ko abinci ko abinsha idan ta karaso, ka gaya mata Allah yana gaisheta, nima ina gaisheta, Allah kuma ya gina mata gida a Al-jannah wanda aka gina da zinari wanda ba takura ba gajiya a cikinsa. 

     Lallai Nana Khadija tanada guri mai girma agun Allah madaukakin sarki, sabida ta taimaki addini da dukiyanta, saboda hakane Annabi yake cewa:-

أفضل نساء أهل الجنة خديجة بنت خويلد، وفاطمة بنت محمد، ومريم بنت عمران، وآسيا بنت مزاحم إمرأة فرعون

Mafi girman mataye a gidan al-jannah Khadija bnt Kuwail, Faɗimatu bnt Muhammad, Maryam bnt Imran, Asiyatu bnt Mazahim matar fir'auna.

     Haka kuma manzo (s) yakara cewa badan kariya ta Abuɗalib ba da dukiyan Khadijaba da takobin Aliyu ba (as) da wannan addinin bai tsayu da da kafafunsaba. 

Takasance uwa gurin ƴaƴansa kuma mai shayar da gidansa wacce ta soni a lokacin da mutane suka ƙini, Takuma kula dani lokacin da mutane ke kyamata. 

Hakika rasuwar Sayyida Khadija jarabawace babba ga Annabi (s) da ɗiyarshi Faɗimatu (s.a) dama sauran musulmai gabaki ɗaya, Hakika musulunci ya samu babban rashi acikinsa na Sayyiduna Abuɗalib da Khadija wanda tsakaninsu kwana 3 ne, Fadimatuzzahra'u (s.a) Tazo tana kuka tana cewa Mahaifinta ina mahaifiya, ta sake mai-maitawa nantake Allah ya aiko Jibril (as) yazo da sako a fadawa Fadimatu

قل لفاطمة أنّ الله تعالى بنى لأمك بيتا في الجنة من قصب، لانصب فيه ولاصخب

Kacewa Faɗimatu Allah Maɗaukakin sarki ya ginawa mahaifiyarta gida a aljannah wanda aka gina da zinari, wanda bagaji ba wahala acikinsa. 

     Irinwannan musiba data sami Annabin Rahma na rashin Amminsa Abudalib da Matarsa Nana Khadija har yakira wannan ranar (yaumul huzin) ma'ana ranar bakin ciki. 

     Sayyida tayi wafati ranar 10 gawatan ramadan banyan wafatin Abuɗalib da kwana 3.

#Release Zakzaky's Passport


©FREEDOM FIGHTERS NG


Post a Comment

Previous Post Next Post