Offline

Jiragen yakin Black Hawk biyu na Amurka sunyi hatsari yayin wani atisaye a Kentucky.

 


Jiragen yakin Amurka biyu samfurin Black Hawk sunyi a hatsari a yayin wani atisayen koyon aiki a Kentucky, Ma'aikatar tsaron Amurkar ta sanar.


Adadin wadanda suka rasa rayukan nasu a yayin atisayen har yanzun ba'a tabbatar dasu ba,mai magana da yawun sojin kasar Amurkar Nondice Thurman ya fadawa gidan Jaridar Reuters, ba tareda sanarda adadin mutanen da jirgin ya dauko bah.


Gomnan Kentucky, Andy Beshear ya fada a wani posting dinsa a Twitter "mummunan abu ya faru a Kentucky ammah 'yansanda da hukumar kula da aikin gaggawa suna kokarin shawo kan lamarin da ya aukun" 


'Yan tawagar dake tukin jiragen biyu na Black Hawk sun tashineh misalin karfe goma na safiyar ranar Laraba a Trigg county kamar yanda Thurman ya fada, musabbabin faruwar lamarin yana kan bincike zuwa yanzu.


A halin yanzu mun maida hankaline don kulawa da iyalan matuka jirgin da ibtila'in ya aukawa.

Post a Comment

Previous Post Next Post