Da farko dai shi wannan Manzo (S), Allah Ta’ala ya aiko shi da saqo ya
zuwa mutane, ya kuma isar da saqon. To kuma ba ya zo ne ya samu mutane ya ce musu “ga saqonku da Allah Ya aiko ni in ba ku” ba.
Kamar misali ya zo da Alqur’ani ya ce “gashin ku! Da ma Allah ne Ya
aiko ni da wannan Alqur’anin.” Sai ya tafi abinsa. Domin ko da haka nan ya yi, sunansa dan saqo, kuma ya isar da saqo.
Domin fakam da yawa, wanda aka aiko shi ya zuwa gare ka da wasiqa, ba sai ya bare maka ambulan din ya karanta maka wasiqar ya koyar da kai abin da ke cikin wasiqar ba. In ya zo ya miqa maka wasiqar ya tafi abin sa, ya riga ya isar da saqo. Kai kuma ya rage gareka ka duba abin da ke ciki, ka fahimci abin da ka fahimta, ka kuma aikata.
Kamar yadda kuka sani ma a nizamin aiki sau da yawa akan ba da umurni ne a takardu, a rubuta kawai, in aka ba ka umurni a takarda shi kenan an gama. In dai ka ji an ce “I am directed to inform you that you should do such, such….” An gama. Kawai ya rage in har ba ka yi ba, sai ka ga takardar tuhuma ta zo maka, ana so ka ba da hujja cikin awa 48, da dalilin da ba zai sa a hukunta ka ba saboda gaza bin umurnin da ka yi bayan an ba ka a rubuce. Wato ina fadin wannan ne don in ce ai da dan
saqon nan ya zo ya ce ‘gashin ku’ ne ya tafi, to ai ya zama Ma’aiki.
To amma kasantuwar wannan saqo yana buqatar a dora mutane a kai, a tarbiyyantar da su a kai, to ba haka nan ya yi ba; kuma ba haka
wanda Ya aiko shin ma Ya yi nufin ya yi ba. Sai ya zamana ya dauki
shekaru ne – shi kansa saqon ma ba jumla daya a rubuce ba ne, a’a, an riqa sauqo da shi ne a hankali, a hankali, daidai gwargwadon buqatar lokaci da yanayi a yayin da yake tarbiyyantar da mutane saqon.
Saboda haka kuma har wala yau ba aikinsa ne ya ce muku ga saqonku ba, Ubangijinku Ya ce muku ku yi kaza ba, a’a. Saqon gare shi ne, shi ne na farko ma. Shi ma kansa an umurce shi kafin kowa ya yi aiki da wannan saqon. Saboda haka sai ya zama shi ya aikata saqon; sannan kuma ya tarbiyyantar da mutane a kan wannan saqon, ya kuma shimfida su a kai, a tsawon shekarun da ya dauka, wato shekaru 23 yana isar da wannan saqo kafin ya koma zuwa ga rahmar Ubangijinsa. Saboda haka ya dauki takalifai, ya sha wahala, wajen isar da saqon nan.
