- Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)
“Abin mamaki, yanzu mu abin da (wannan al’ummar) suke so shine matsiyata (kar a ce na zage su), miyagu, rubabbu suna wari, wai su ne za su gyara mu. To, bai taba faruwa ba, kar ku taba mafarkin wannan zai faru.
“In ana son a samu adalci ma’abota adalci za a nema. In ana neman addini wajen masu addini za a nema. Wadannan kuwa da suke gudanar da zalunci din nan a haka za su karata, kuma lallai sai sun ga hukumcin Allah a nan duniya kafin na Lahira. Amma ba su muke son su gyaru su gyara mu ba!
“Ka dauko tarihi ka gani. Dauko tarihin duk Annabawa ka karanta, ka ga ta ina ne ka ga wani dama can ana damawa da shi a zalunci ya zo ya gyaru? Sam! Karanta ka gani, ka fada mana in akwai.
“Kuma ka duba da kyau ka gani, shi Annabin da su wa ya yi amfani? Da wadannan lalatattun ne? Ba da su bane. Da bayin Allah na gargaru ne. Shi Manzon nan da ya yi da’awa ba wadannan azzaluman ya tattaro yace to ku gudanar da adalci ba. A’a, wadansu mutane ne raunana, wadansunsu ma Bayi wadanda ake tursasawa.
“Kamar Bilal wanda da ya yi imani da Manzon nan, mai gidansa ya rika daura masa katon dutse a ciki, Bilal na cewa Ahad! Ahad! Kamar Suhaib Barume. Kamar Habbab, wanda aka ce uwar gijiyarsa ta kan yi shimfidar garwashi ta sa shi ya kwanta, in jininsa na zubowa shi yake kashe garwashin. Don akwai wani yaki cikin yakoki da ya tube rigarsa, sai Manzon Allah (S) ya ga bayansa bakin kirin. Sai ya tambaye shi me ya faru? Sai yace ai lokacin da ya Musulunta ne.
“Sauyin da Manzon nan (S) ya kawo, ba wadanda suke barna ne suka zo suka yi gyara ba. Su sun ta gaba da shi ne har izuwa karshe. Amma ya yi amfani ne da wadansu raunana, da yawansu ma Bayi, kamar Bilal, kamar Habbab. Ina ba da labarin Habbab, Manzon Allah ya ga bayansa ya zama kamar gawayi, yace ai bayan da ya Musulunta ne uwar gijiyarsa take shimfida masa garwashi ya kwanta a kai, in jininsa ya gangaro shi ke kashe wutan.
“Haka nan wadannan bayin Allah din da ake ganinsu raunana, su ne suka tsaya kyam, su suka taimaki Annabi (S), da sune addini ya tabbata. Sune kuma wadanda za su samu manya-manyan darajoji gobe Kiyama.
- Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a jawabinsa na Mauludin Manzon Allah (S) a cikin birnin Zariya a shekarar 2014/1435.
