- Shaikh Zakzaky (H)
kullum na kan tunatar da mutane cewa, ku gane cewa kafa addini daram a doron kasa wajibin kowane Annabi ne, kuma burin kowane Annabi ne.
Sai dai ya zama wasu burukan sun cika wasu basu cika ba, amma burin kowane Annabi shine addinin ya da zo da shi ya tabbata daram, ya yi iko a inda aka aiko shi. In ya yiwu ya kafu daram, Masha Allah, in bai yiwu ba, shi dai Annabin ya yi aikinsa, sai ya zama su al’ummar ne suka ki amsa, ba wai laifin Annabin bane, domin duk Annabawa sun isar da sako.”
@SZakzakyOffice
13/10/2022
