Offline

Takaitaccen Bayani Kan Idin Ghadir



Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin Kai

Lamarin Ghadir yana daya daga cikin muhimman lamurra a cikin addinin muslunci, da ke bukatar dukkanin musulmi su yi karatun ta natsu a kansa, domin sanin hakikanin abin da ya faru a wannan rana ta Ghadir, tare da fadada bincike a kan lamarin, domin kuwa lamari ne da ke da alaka kai tsaye da addini da makomarsa, kamar yadda rashin sanin hakikanin abin da ya faru zai iya zama mai illa ga musulmi da kuma makomar addininsa.

Har kullum abin da mai bincike yake tambaya a kansa shi ne mene Ghadir? yaushe ne ya faru? Kuma wane sako ne yake cikin wannan lamari na ghadir? da dai sauran tambayoyi makamantan hakan. To wadannan tambayoyi dai su ne abin da za mu yi kokarin amsawa a wannan shafin, don haka sai a biyo mu.

Da farko dai malaman tafsiri, tarihi da hadisai dai duk sun bayyana cewa wannan lamari dai ya faru ne a kusan karshen rayuwar Ma'aikin Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) wato lokacin hajjin "Ban Kwana" a ranar 18 ga watan Zil Hajji shekara ta goma bayan hijira.

Malaman dai sun ce a wannan shekarar dai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) ya kuduri aniyar zuwa aikin hajji na karshe a rayuwarsa, hajjin da daga baya ake ce masa "Hajjin Ban Kwana". To koda wannan labari na tafiya hajjin Manzon (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) ya yadu sai jama'an musulmi suka dinga tuttudowa daga garuruwa daban-daban na musulmi don raka Manzo, ta yadda an ce yawan adadin wadanda suka je wannan aikin hajji sun kai mutane dubu dari da ashirin, ban da wadanda suka sami shi a can garin Makkan.

To bayan gama aikin hajjin, sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) ya kamo hanyar dawowa gida Madina tare da wadannan mabiya nasa har suka iso wani guri da ake ce ma "Ghadir Khum", wata mararraba ce da ta hada hanyoyi daban-daban, wata hanyar ta yi Madina, wata kuwa ta yi Iraki, Masar da kuma Yaman, sun iso wannan mararraba ce kuwa a ranar 18 ga watan Zilhajji.

Don haka a nan sai aka dakata dukkan al'umma wadanda za su sauran kasashe kuma suka yi ban kwana da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) suka kama hanyarsu ta zuwa gida, haka nan shi ma Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) da tawagarsa wadanda za su Madina suka fara shirin tafiya.

A daidai wannan lokaci kuwa sai ga Mala'ika Jibril (a.s) da sako daga wajen UbangijinSa Madaukakin Sarki, wato ya zo wa Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) da wahayi kenan. Abin da Jibril (a.s) din yake dauke da shi kuwa ita ce wannan aya ta "Isar Da Sako" .

Abin tambaya a nan shi ne wani sako ne Mala'ika Jibril ya zo wa Manzo (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) a daidai wannan lokaci? Kuma me ya sa Allah Ya ke yin barazana wa ManzonSa (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) cewa lalle fa ya isar da wannan sako idan har bai yi hakan ba kamar bai idar da sakon da aka aiko shi da shi ba ne wato Musulunci? Shin akwai kokwanto ne cewa Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) zai boye wani abu cikin sakon da aka aiko da shi? To me ya sa aka masa wannan barazana? Kuma shin wani muhimmanci ne wannan sako ya ke da shi da har Allah Zai yi alkawari wa Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) cewa Zai kare shi daga mutane? Shin akwai wasu mutane ne da za su so cutar da Annabin (s) idan har ya isar da wannan sako? To wadannan dai da ma wasunsu, sune tambaoyin da za mu yi kokarin amsawa nan gaba, Insha Allahu.

To bayan saukar wannan aya, sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) ya dakata, ya yi umurni da kowa da kowa ya taru, wadanda ma suka riga da suka wuce a ce musu su dawo, wadanda kuma ba su riga da sun iso ba, a jira su su iso. Don haka lokacin da kowa da kowa ya hallaro, a daidai lokacin kuwa lokacin sallar azahar ya yi ga shi kuma ana tsananin zafin rana, ta yadda wasu ma sukan sanya mayafinsu ne a kasa don su taka saboda zafin rana, wasu kuma a kansu don kare zafin rana.

Don haka sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) ya jagoranci mabiyansa sallar azahar, bayan an idar da salla, sai al'umma suka tattara sirdodin rakumansu daya bayan daya aka yi wa Manzon Allah wani abu kamar mimbari don ya hau kowa ya ganshi da kuma jin abin da zai fada. Daga nan sai Manzon Allah (SAWW) ya hau, ya daga sautinsa iyakacin iyawansa, ya fara jawabinsa.

Inda bayan godiya ga Allah da kuma tsarkake Shi, ya gabatar da jawabi mai tsaron gaske ga musulmi, ga kadan daga cikin abin da ya ce wanda kuma shi ne ya yi daidai da wannan maudhu'i da muke magana a kai.

Ya ce: Ya ku mutane....an kusan kirana kuma zan amsa (wato rayuwarsa ta kusan karewa), kuma ni abin tambaye ne kamar yadda kuma abin tambaya ne, to me za ku ce?

Cikin murya guda sai suka ce: Lalle za mu shaida cewa ka isar (da sako) kuma ka yi nasiha kana kuma ka yi jihadi, Allah Ya saka maka da alheri.

Sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) ya ce: "Ashe ba za ku shaida cewa Babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah ba, kuma Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa, kuma Aljanna gaskiya ce haka nan wuta ma gaskiya ce, mutuwa kuwa gaskiya kuma ranar tashin kiyama mai zuwa ce babu kokwanto cikinta, kuma Allah Zai ta da wadanda suke cikin kabari?"

Sai suka ce: Lalle mun shaida hakan, Sai ya ce: "Ya Allah Ka shaida".

Sai ya sake cewa: "Ya ku mutane kuna ji". Sai suka ce: Na'am, (muna ji).

Sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) ya ce: "Lalle zan isa zuwa ga tafki...don haka ku kula da yadda za ku halifance ni a bayana a kan Thakalaini (Nauyaya Biyu)?"

Sai wani ya ce: Ya Manzon Allah mene nauyaya biyu?

Sai Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) ya ce:"Mai nauyi na farko kuma ya fi girma shi ne Littafin Allah, sashinsa na hannun Allah daya sashin kuma yana hannunku, ku yi riko da shi ba za ku taba bata ba. Dayan kuwa shi ne karami. Don kuwa Allah Madaukakin Sarki Ya sanar da ni cewa ba za su taba rabuwa da juna ba har sai sun riske ni a bakin tafki, don haka kada ku wuce gabansu sai ku halaka, haka nan kuma kada ku gaza dangane da su sai ku halaka"

Daga nan sai ya kama hannun Imam Ali (a.s) ya daga sama duk kowa ya ganshi yana mai cewa:

"Ya ku mutane! Wane ne ya fi soyuwa ga muminai a kan kansu?

Sai suka ce: Allah da Manzonsa.

Sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) ya daga sautinsa ya ce:"Hakika Allah Shi ne Majibincina ni kuma ni ne majibincin dukkan muminai, kuma ni ne na fi soyuwa a gare su a kan kawukansu. Don haka duk wanda na kasance majibincinsa to Ali ma majibincinsa ne.....Duk wanda na kasance majibincinsa, to Ali ma majibincinsa ne.....Duk wanda na kasance majibincinsa, to Ali ma majibincinsa ne....Ya maimaita hakan har sau uku.

Sai ya ci gaba da addu'a yana mai cewa: Ya Allah Ka jibinci wanda ya jibince shi Ka yi gaba da wanda ya yi gaba da shi, Ka so wanda ya so shi, Ka ki wanda ya ki shi, Ka wulakanta wanda ya wulakanta shi, ka tabbatar da gaskiya a duk inda ya ke. Wanda yake nan ya isar da wanda ba ya nan".

Haka nan dai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) ya ci gaba da jawabinsa da nuna wa mutane cewa a bayansa fa Imam Ali (a.s) ne zai kasance halifansa ba wani ba, kana kuma ya yi kira ga al'umma da su yi masa da'a da kuma biyayya matukar dai sun yi imani da Allah da kuma ManzonSa, haka nan kuma matukar dai suna son samun tsira gobe kiyama.

Gama wannan jawabi na Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) da kuma nada Amirul Muminina Aliyu bn Abi Talib (a.s) a matsayin halifa ke da wuya, kuma kafin jama'a su watse sai ga Mala'ika Jibril (a.s) ya sake dawowa da wani sakon na daban, yana mai karanta masa wannan aya mai albarka, "Ayar Cikan Addini". Ayar kuwa ita ce:

Bayan saukar wannan aya nan take sai aka ji Manzon Allah SAWW) yana cewa: "Allahu Akbar (Allah Mai Girma) Kan Cika Wannan Addini, da Kuma Cika Ni'ima, da Kuma Yardar Da Ubangijina ya yi da Wannan Sako Nawa da Kuma Wilayar Aliyu a Bayana".

Mai karatu wannan dai ita ce "Ayar Cikon Addini" wacce ta sauka bayan tabbatar da wilayar Aliyu bn Abi Talib (a.s). Hakika akwai abubuwan da ya kamata mu kula da su a nan karkashin wannan aya. Za mu yi bayaninsu na gaba. Mai son karin bayani kan hakan sai ya bangaren fehrisan wannan bincike a bangaren hannun hagu karkashin maudhu'in "Ayar Cikan Addini".

Daga nan kuma sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) ya sauko daga kan wannan mimbari ya umurci dukkan mutanen da suke gurin da su zo su taya Ali (a.s) murnar samun wannan babban matsayi da Allah Madaukakin Sarki Ya ba shi da kuma yi masa mubaya'a a gabansa don kada wani daga baya ya zo ya ce ba haka nan ne ba.

Haka nan kuwa ya faru dukkan mutanen da suke gurin sanda suka zo suka yi wa Imam Ali (a.s) mubaya'a suna masu cewa Assalamu Alaika Ya Amirul Mumin. Daga cikin wadanda suka yi wannan bai'a kuwa hadda Abubakar da Umar, inda har ma aka ruwaito Umar yana cewa: Barka-Barka Ya Dan Abu Talib, A yau ka zama Shugabana da kuma shugaban dukkan muminai maza da mata.

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) bai bar wannan wajen na Ghadir ba har da dukkan mutanen da suke gurin (Ghadir Khum) suka yi bai'a wa Imam Ali (a.s) a matsayin muminai, wannan bai'a kuwa ta ci gaba har na tsawon kwanaki uku, don kuwa bai aiki ne na 'yan wasu sa'oi ba saboda yawan mutanen da suke wajen.

To mai karatu wannan dai ita ne waki'ar Ghadir wannan ya faru a wannan rana ta 18 ga watan Zul Hajji shekara ta goma bayan hijira. Wanda kuma ya ke tabbatar mana da wilaya da kuma halifanci Aliyu bn Abi Talib (a.s) bayan Ma'aiki (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa).

Wani abin da kuma ya dada kara wa wannan lamari da ya faru a wannan rana armashi da kuma dada tabbatar da matsayin Imam Ali (a.s) a wajen Ubangiji da kuma kare wannan sako na Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) shi ne saukar wannan aya ta Alkur'ani mai girma da take cewa:

Tun da jimawa dai kafirai sun ta bayyana cewa Manzon Allah (s) ya tsufa, don haka idan ya rasu babu wani mai gadonsa, kenan wannan addini na Musulunci zai kawo karshe kenan. To amma bayan nada Imam Ali (a.s) a matsayin halifan Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) nan take sai kafirai suka yanke kaunar cewa za su iya yin wani abu wa wannan addini, don kuwa sun riga da sun san wane ne Ali, kuma sun san irin kashin da suka sha a wajensa tun farko Musulunci ya zuwa kuma wannan lokaci.

Shi ya sa ma Allah Madaukakin Sarki ya ce a yau (wato ranar da aka nada Ali a matsayin halifa) kafirai sun yanke kauna a kan addininku, don haka abin da kawai ya hau kan muminai shi ne jin tsoron Allah ta hanyar yin da'a da kuma biyayya ga Imam Ali (a.s), matukar suka yi haka to babu wani abin da zai same su, kuma kafirai ba za su iya yi musu komai ba.

Akwai wani abin da ya faru a wannan lokaci, wanda kuma yake dada tabbatar mana da wajibcin yin biyayya ga Ali (a.s) da kuma cewa hakan daga Allah ne ba wai daga wani ba ne, kana kuma kin amincewa da haka yana a matsayin kafirci ne, kana kuma babu makawa mai hakan zai fuskanci azabar Ubangiji ko a nan duniya ko kuma a jinkirta masa sai zuwa ranar tashin kiyama, wanda babu kokwanto cikin hakan.

Da Wannan dan takaitaccen bayani za mu tsaya, amma mai bincike zai iya komawa zuwa ga littafai masu yawa da aka rubuta su bisa dogaro da sahihan bayanai kan lamarin Ghadir domin kara ilmantuwa.

Muna rokon Allah ya kara mana shiriya daga hasken shiriyar manzonsa da alayensa masu tsarki.

Post a Comment

Previous Post Next Post