__ Malam Muhammad Maina ( 9/2/2018 )
Wannan shi ne jawabin da Malam Muhammad Maina ya gabatar a gurin zikirar cika shekara daya da Shahadar Malam Kasim Umar Sakkwato, wacce aka gabatar a ranar Assabar 9/2/2018 a Sakkwato. Tun a farko ya fara ne da taya jaje ga daukacin ‘yan’uwa Musulmi musamman mahalarta wannan taron da aka gabatar, daga nan kuma ya cigaba da jawabi kamar yadda aka bukace sa, inda yake cewa;
“Kamar yadda kowa ya sani ne dai tun a matakin farko mu ‘ya’ya ne kafin ma mu zo mu zama almajirai, zan iya tunawa a wannan marhalan, nasan su Malam Kasim tun a yarinta, amma a marhala ta aiki, sai bayan fitowarsu daga Gidan yari, a lokacin da suka zo nan Zariya, a wancen lokacin nasan su Malam (H) sun musu tarba ta girmamawa, to kuma tun a wannan lokacin dai muna ta kallon su Shahid, domin ba mu san wannan bawan Allah wane irin aiki ne zai hada mu da shi ba, bayan sun kammala wannan ganawa da su Malam (H), zan iya tunawa a wancen lokaci mun je mun sami Malam Kasim da Ni da su Sayyid Mahmud, da Hamid, da Hammad, muka tafi duka bayan su Malam (H) sun shiga ciki, sai muke gaya masa cewa, “to ga mu nan dai mune ‘yan Abulfadal watakila kuna jin labarinmu, a lokacin da kuke tsare” sai Malam Kasim ya ce “eh lalle hakane muna jin labarinku” muka ce to mun kawo gaisuwa ne, wannan shi ne farkon alakar mu da su Malam Kasim na aiki a gwagwarmaya.
Abu daya da zan dan yi kokarin fitarwa dangane da su Malam Kasim duk da nasan cewa an yi maganganu dayawa kan abubuwan da suka shafi rayuwar Shahid, ibadarsa, sadaukarwarsa, dss. Mu a ta janibinmu akwai abin da ya fi burge mu da Malam Kasim, kuma shi ne abin da ya karfafa alakarmu tare da shi, saboda haka akan wannan zan yi magana. Wannan abin ba komai bane illa wilayarshi, cikakkiyar wilayarshi ga jagora (H). Nasan a mafi yawancin lokuta mutane sukan yi mana mummunar fahimta da cewa “yan Abulfadl suna fada da mutane, suna fada da manya” to kuma a lokaci daya sai aka zo aka ganmu muna shiri da Malam Kasim, wasu sun yi ta mamaki tare da tambayoyi akan cewa, ba kuna cewa Malam kawai ba ? To yaya aka yi kuma muka ganku jikin su Malam Kasim, nasan harma wadansu sukan ce masa abokinmu. Lalle hakane Malam Kasim mu a gurinmu ya ma fi karfin aboki shi Malaminmu ne, saboda mun hango kuma mun lura da cewa shi Malaminmu ne a wilaya, dama wilayar ce muke ji da ita, sallamawa ce dari bisa dari muke takama da ita, to da muka hadu da shi sai muka gano cewa ai Malaminmu ne a ta wannan bangaren, kunga ko dole mu duka ya koyar da mu yadda ake sallamawa.
Sayyid Ahmad tarbiyyar da ya yi mana ita ce, sallamawa Jagora dari bisa dari, har yake cewa idan ya kasance a sallamawarka ka kasance ka sallama kashi tasa’in da tara da digo tara sai ya kasance baka cika sauran wannan ziro foyinti wan wan dinnan ba, to al’amarin wilayarka ya zama zero, ba za a karbeta ba, yazo a ruwaya fassarar ayar “wakiffuhun innahum’mas’ulun” akwai riwayar da take cewa, bayan an gamawa mutane hisabi a ranar lahira, sai ance su tafi su shiga Aljanna sannan za’a sake kira daga baya ace “wakiffuhum” a tsayar dasu, “innahum’mas’ulun” akwai tambaya a kansu, aka ce “mece ce wannan tambayar ” aka ce “wilayatu amirul mu’uminin Ali (a.s)”, wannan ya nuna mana cewa kenan dukkan ibadarka, dukkan gwagwarmayarka, dukkan abin da mutum zai iya yi a tafarkin Allah, idan a wilayar shi, akwai nakasu na koda kwayar zarra, to ya rusa aikinsa ga baki daya, amma idan wilaya ta samu dari bisa dari to yana nufin za’a iya yiwa mutum tagoma shi a fitar masa da sauran kurakuransa da ya yi a gefe. To kuma gaskiyar al’amari wilayar nan musamman a wannan yanayi tana cikin abubuwa masu tsada, wanda ya zamanto cewa, samun muwalin da zasu sallamawa Jagora dari bisa dari sun karamta sosai, ga dai tulin mabiya nan fululu, Miliyan shabiyar, ashirin, za ka ji ana ta kirga adadi, to amma su waye muwalin na hakika ? Su waye wadanda basa gabatar da nasu son rai akan karantarwar Jagora ? Waton wadanda duk abin da ya yi umurni da shi shi za a je a yi ba tare da an shigo da son rai ba, to akan wannan ne muka yi observing da su Malam Kasim kafin ya kasance mun saki jiki dasu.
Kuma mun gano cewa lalle Malam Kasim muwali ne na karshe, domin abu na farko, ya tsallake jarabawar azzalumai wanda dama mun san akan jarabe mutum da azzalumai ta inda ya zamanto sukan bi wadansu hanyoyi domin takurawa mutum, misali, za a iya kwadaitar da kai da mulki ko dukiya, za a iya tsoratar da kai da kamu ko kisa, kuma sukan shirya trap (tarko) wanda idan ka fada to sai su rika amfani da wannan suna juya kambunka ta baya, to munsan duk Malam Kasim ya tsallake wadannan, kuma shi yasa azzalumai suka rantse cewa ko ta wane hali sai sun ga bayanshi.
Na ji daga bakin su Sayyid Ahmad cewa, “a gwagwarmar Imam Khumaini (q.s) a wancen lokacin azzalumai da kafircin Duniya ba su taba hankoron suje ga Imam Khumaini ba, saboda yana da wadansu almajirai wadanda da su azzaluman suke tunanin cewa idan ma sun ga bayan Imam din to barin wadannan almajiran ma matsala ne, saboda haka kafin a kai ga shi Imam a fara gamawa da wadannan almajiran, sai Sayyid Ahmad yake cewa, “to mu abin takaici a wannan harka, sai ya zamanto Malam (H) kadai ake hankoron sai an kai gareshi” waton babu wadansu almajiran Malam (H) da suka zamowa azzalumannan ciwon kai, wadanda kuma zasu dauke musu hankali akan Jagora (H), to kuma sai gab da shahadar su Sayyid Ahmad, muka sami labarin cewa, su jahiliyan sun shirya cewa, Ahmad dole a kawar da shi, waton kafin a kai ga su Malam (H) dole a kawar da su Sayyid Ahmad, saboda suna tsoron, tasirinshi a cikin matasa, sa’annan kuma ba’asan mene ne zai iya yi ba bayan ba mahaifinsa, saboda haka sai suka ce “kafin a kawar da mahaifinsa sai an kawar da shi, kuma shi ya janyo suka yi duk haukan da suka yi suka yi, kuma sun kashe su Sayyid Ahmad.
Haka kuma tun bayan wannan lokacin ba a kara samun irin wannan yunkurin ba, sai a kan su Malam Kasim, inda suka haukace dukkan matakan da zasu iya dauka na kisa ba kunya ba tsoron Allah, koma me zai faru sai sun kashe shi, saboda a lokacin tunanin da suka fara yi, shi ne cewa, Malam (H) na hannu amma ga wani a waje wanda yake basu matsala, wanda a nasu tunanin koda sun iya gamawa da su Malam (H) to suna kallon fa Malam Kasim matsala ne, ta yadda zai iya hada kan al’umma, zai cigaba da gudanar da al’amurra da irin karantarwa ta su Malam (H) tare da ya yi compromising na komi kankantar abun da ake so ya yi compromising ba, kuma lalle wannan shi ya nuna mana cewa, indai mutum ya bi wannan sahun, to fa lalle azzalumai ba zasu barshi ba, kuma ba wai kawai zasu rika surutun cewa zasu kashe mutum bane a a da gaske zasu yi, a takaice dai wadannan abubuwan su suka kara dankon alakarmu da shi Malam Kasim ta yadda ya zamanto cewa, mun gurfana a gabanshi muna daukar darasi, musamman na wilaya.”
Tags
Munasaba