Tun farko-farkon watan Bahman 1357 (1979) labarin shawarar da Imam ya yanke na dawowa gida ya yadu ko ina. Jama'a kuwa duk wanda ya ji wannan labari sai ya zubar da hawaye don murna, don kuwa abin da suke jira kenan har na tsawon shekaru 14, duk da cewa suna cikin damuwa kan tsaron lafiyarsa, don har zuwa lokacin gwamnatin jeka na yi kan Shah ita ce ke mulki, sannan ga kuma dokan ta bacin da ta kafa na ci gaba da aiki. Imam Khumaini ya riga da ya dauki matsaya ta karshe, don haka sai ya sanar da al'ummar Iran, cikin wani sako da ya aike musu, cewa yana son ya kasance tare da su a wadannan ranaku masu muhimmanci. Hakan ya sanya gwamnatin Bakhtiyar, bisa hadin gwuiwan Janar Haizer, suka rufe filin jirgin saman birnin Tehran sashin zirga-zirgan waje.
Bayan wasu 'yan kwanaki, gwamnatin Bakhtiyar ta bude filin jirgin sama saboda gagarar da ta yi wajen jure wa wannan bore na al'umma. Daga karshe, a safiyar ranar 12 ga watan Bahman 1357 (1 ga watan Fabrairun 1979) Imam Khumaini ya dawo gida bayan shekaru 14 na gudun hijira. Irin gagarumar tarbar da al'umma suka yi masa ya kai matsayin da hatta kafafen watsa labaran yammaci sun gagara inkarin hakan, inda su da kansu suka ce mutanen da suka tarbi Imam Khumaini sun kai miliyan 4 zuwa 6.
Tags
Resistance News