Akwai wasu surori na Alkur’ani da suka zo a ruwayoyi na hadisi cewa ana son karanta su a kowane dare da kuma ko wace rana na watan Rajab.
Wadannan surori ko sune:
An ruwaito daga Imam Ali[AS] yace,Manzon Allah[S] yace, “Duk wanda ya karanta a kowane dare da kuma kowace rana surar Fatiha,da Ayatul kursiyyu,da kulya-ayyuhal-kafirun,da kul-huwallahu,da kul'auzu birabbil falak da kuma kul'auzu birabbin nas to Allah zai gafarta masa zunubansa baki daya.Ko wace sura mutum zai biya sau ukku ne.
Haka nan ana son mutum ya karanta kul huwallahu sau dubu a watan Rajab,in kuma ba zai iya ba to akalla duk ranar Jumma’a na watan Rajab ya biya ta sau dari.
Yazo a ruwaya cewa duk wanda ya aikata haka to zai kasance yana da wani haske ranar kiyama wanda zai jashi zuwa Aljanna.Saannan baya ga haka kuma ana son mutum ya yawaita karatun Alkur’ani a wannan wata na Rajab,wato dai ya samu ya sauke Alkur’ani da yawa,misali ya samu ya yi sauka goma ko bakwai ko biyar ko ukku in zai iya,in haka bai samu ba to akalla ya samu ya sauke Alkur’ani sau daya a cikin watan.
©Copyright: Tambihi.net
*Daga Zauren: F-Fighters A'amal*
*Freedom Fighters Ng.*
www.freedomfightersng.com
Tags
A'amal