-- Ammar Muhammad Rajab
A matsayinka na dan Harka Islamiyya wanda ya dauki bangaren 'soshiyal Midiya' a matsayin gudummawar da za ka bayar wurin yada sakon fahimtarka, har kake kiran kanka da 'Dan Media', yakamata a ce ka zama 'Image maker' na Harka Islamiyya ba 'Image destroyer' ba.
Aikinka a wannan sahar shi ke nuna zurfin tunaninka da iliminka da fahimtarka, wannan yana daya daga cikin matsala/tasirin rubutu a fahimta ta. Domin ta hanyar abin da kake rubutawa, yadawa (sharing), yabawa (like), kwafa da saukewa (copy and paste), sharhinka (comment), ana iya gane wane ne kai da zurfin tunaninka da iliminka akan abin da kake magana a kai; wanda hakan ke sake 'exposing' din iliminka ko jahilcinka kan abin da kake ikirarin wakilta.
Amma ta ya ya za ka zama 'Image maker' na Harka Islamiyya a soshiyal Midiya?
A gani na abubuwa da dama na iya sanyawa ka zama 'image maker' na Harka Islamiyya; daga ciki ina ganin akwai;
(i) Sanin Harka Islamiyya da hadafinta.
(ii) Fahimtar Jagoran Harka Islamiyya.
(iii) Fahimtar yadda Harka ke samun ci gaba da kulen da take fuskanta a 6angarenka.
(iv) Nazarin jawaban jagoran Harka Islamiyya (nazari ba saurare ba), tare da fahimtar su wane ne aka yi wa jawabin (audience), a wanne muhallin ne aka yi jawabin (context), yaushe ne aka yi jawabin (date).
(v) Sanin kauli da ba'adin harshen da kake rubutu da shi; tun daga amfani da Daidaitacciyar Hausa/Ingilishi da ka'idojin rubutun Hausa/Ingilishi.
(v) Fahimtar abin da ake kira da 'public relations' wajen kyautata abin da kake wakilta.
Akwai bukatar na warware wadansu 'points' din da na kawo domin fahimtar abin da nake nufi sosai. Insha Allah zan zo da karin haske a rubutu na gaba.
Tags
Makaloli